← Book details Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 187 OF 197

Sashe 187

Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

wani abunda zai sa ta dinga wahala shi keyi “daya shigo office din yaga ba kowa kuma shidai bai ganta waje ba “ah ko tana toilet ne aie bai ma karasa tunanin ba yaji wani kara da salati dawani kalan speed yafada toilet din yaganta kwance cikin jini rufe idonsa yayi ya hau salati yakasa yin komai ma ga jini tana fitarwa sosai ganin bai da niyyar kamata duk yarude yasa tafasa kara tace waii yah faisalllllllllll baka gani cikin masifa tayi magana taja sunan shi sai lokacin fa yadauke ta yayi labour room datayi kasa yin komai yay isai dai aka kira wata babbar nurse ita ta taimaka ta gyarata still jini yaki tsayawa sunyi iya kokarin su saidai yarage duk dr faisal yayi wani firi firi dakyar nr yasir yasamu yakai sa gida yayi wanka atare da rabiah sukaje tashiga gidan dr faisal din ta kwaso ma dr hafsa duk abunda zata bukata ga gida ga gida suke cikin doctors housings din “ sune kawai dangin juna da rabiah da dr hafsa din rabiah ce tsaye kan dr hafsa din wanda ita har yanzu amarci suke sha ba ciki da ita da aysha daman da halime da dr hafsa ne masu cikin Allah dana shi ikon kuma ga na hafsa ya zube har dare dr hafsa her condition is critical rabiah ce takira gida ta sanar dasu duk hankalin kowa yatashi inna data dinga kuka wiwi wiwi a cikin daran tad’aga ma abby hankali sai ankai ta lagos taga halin da marainiyar Allah take ciki diyar amana ce yau hajajju har tafi inna kamewa ita ta lallashi innar tadinga bata baki su iya ma dasu hibba duk rabiah ce tafada oum takalli ummi tace yanzu kodai konice naga zan iya samun flight ko zuwa asuba ne sai naje lagos din tunda babu wani babba acan ummi tayi shiru tace wannan shawara ce oum su amma ko bari zaayi muga abunda hali yabada ko zuwa gobe ne in sha Allah idan ba sauki wanda baa fata sai mu tafi baki daya Abby yagyada kai yace wannan gaskiyane oum su mubari zuwa goben in sha Allah yatashi yakoma kusa da inna yazauna yace hakuri zakuyi hajiya in sha Allah zata ji sauki manya likitoci ne acan din damuna nan damuna can duk dayane ko munje babu abunda zamu iya yi kuyi hakuri dan Allah ai ta addua kukan da ifaceifacan bashi da amfani adduar tafi bukata inna tayi shiru tasa gefen mayafinta tana goge hawayenta hajajju na taya ta hajajju takalli oum tace itama tagoge hawayenta tace ki kiramun mijin aida ki sanar dasu halin damuke ciki shima habibu ki kirasa ki fada masa da jafa’in damuka tashi yau wannan masifa dami tayi kama anata murna yarinya tasamu rabo amma matsafan legas sun cinye ciki baba tace uhm-uhm subhanallahi wai ku dan Allah miya har yanzu kaman baku da lissafi watau kenan Allahn daya basu bai karban abunsa sai tsafi kenan anya anya kam hajajju tayi mitsi mitsi da ido tace aaa yaya abunda hwa nasani na fada kaf wurin nan kaf familin nan duk wanda yayi magana baki ga bakinsa basai ni abby yadafe kai yace kunga kunga duk ayi hakuri hajiya wannan ba lokacin kace nace bane lokacin jimami ne hajajju ta tsuke baki takama bakinta tayi shiru tace tau bara muyi shiru kafin a canza manah magana ta kalli inna tayi mata alaman datayi shiru abby yakalli oum yace kinga fatima maganar ki fadawa malik abarshi kar a dagawa ita asiyar hankalin tunda ga halin datake ciki itama ummi tayi saurin gyada kai tace wannan gaskiya ne malam ubangiji Allah yabata lafiya duk suka ce Ameen “acan lagos kuma ba ita ta farka bas ai wurin 1:30am na dare rabiah ce zaune kusa da ita a dayan side din sai dr faisal din dake zaune kusa da kanta rike da hannunta wanda babu cannula yazuba mata idonsa dayayi yaushi don wallahi kuka yayi whatttt yanda yake son hafsa yanda yake valuing likitar shi inaaaa dole yashiga wani hali gashi wallahi dole kaji tausan ta taji wuya “babu yanda nurse yasir baiyi dashi ba yayi hakuri su tafi gida yana bukatar hutu idan yaso yadawo da asuba amma inaa dr faisal kiyawa yayi yace babu inda zaije babu yanda aka iya haka abarsa “fuskanta gefen dayake take kallo ahankali take bude idonta har tabude sa kansa yana ganin haka yayi maza yamike yana murmushi yace sannu hafsa sannu boo ta gyada masa kai bakin ta yayi nauyi “rabiah tace Alhamdulilah sannu auntie ya jikin dr hafsa ta gyada kai rabiah tace Allah yabaki lafiya dr hafsa ta jinjina kai awani kalan hankali da muryanta dayayi kasa da yawa tace yafita?dr faisal yakama hannunta daya yakai lips dinsa bisa yagyada mata kai gently talumshe ido tabude tasake cewa kamani naje bayi dasauri yamike yabi ahankali yazare mata cannula daman jini ne ake kara mata ya kusa karewa ma daukarta yayi bai bari tayi tafiya bai ta dai rabiah daga yar jinya yar kallo tazama shi mata komai yasake shirya ta pad ma tayi kadan sai da aka hadda hada pampers tass ya wanke kayan data bata yadauko ta yadawo yazaunar da itakan gadon ruwan Lipton rabiah tahada mata dakyar take sha kafin aka zuba Pepper meat a bowl mai zafi shima dakyar yasamu tasha yabata magani ta kwanta “kwanan su biyu asibiti oum da ummi suka zo hadda inna ummi tace kwara ta taho da ita idan ta warware sai yazo su taho tare don wallahi tasha wahala “har fadawa tayi bana wasa ba amma da bayan biki first ziyaran dasuka kawo dr hafsa duk tafi su cikan daki tayi wani irin masifan kyau daman abu ga mai kyau “ kwana su daya suka taho da ita ummi c eke kula da ita a kwana biyun nan har taji sauki amma ummi tace sai tayi sati arana kam dr faisal sai yakira sau goma vedio call kam ba magana abun nashi ba sauki ahhh wani lokaci ma bata dauka saboda kunyar ummi “ummi duk nasane dasu haka su baba “inna kasa hakuri tay isai datayi magana da aysha da halime hadda mariam yan makaranta shiryowa sukayi suka zo dubata dasu hibba da junior dinta sai iya hadda dr ibrahim suka dubata duk kwanan su daya suka koma wani irin kula dr hafsa ke samu wajan ummi har tamayarda jikinta ita kanta ji tayi takara wani son ummi din yanda take kula da ita wallahi kaman ita ta haifeta “Halime tayi sa’a babu laulayi babu komai Allah ne yataimake ta ga aure ga ciki ga hidiman school shiyasa ma cikin bai bata wahala “ranar da aka san anada cikin waiiiii aie cikin daran wanda can Washington safiya ce sai data kira aydarh tafada mata wallahi ita aydarh kunya mataji malik na zaune sai data kashe wayar ya kalleta yace kingani bas ai ke sarkin kunya ki dinga wasu boye boye ta tura masa baki cike da tsiwa tace erh din anyi din “ina har dadi ma kake ji kana cemun shy bea malik yace kee wa din ni a ina da dai sturbborn bea ne wannan nasan nafada aikam kaman tana jira tafashe masa da kuka ba hawaye tace ohh nine ma sturbborn bea bayan this sturbborn bead aka hadani dasu har ni kake kira sturbborn bea? Yayi murmushi yace aie rama mun suke tayi masa banza tacigaba da cin fries din gabanta “.Wani kalan ciwo da bayanta yakeyi tun tana daurewa har tafasa kuka bai nan yafita yasiyo mata hot chocolate datace tana so a cafe din kusa dasu “ wani kalan sharp pain wanda bata taba experiencing ba taji for the second time in her life daga ranar daya karbi virgin dinta sai yau take jin wani azaba kuma a bayanta da kuma maranta kan sofa take zaune amma inaa sai da ta lallaba tasamu tasauko kasa kan carpet tahade kanta da sofa ta fashe dawani irin kuka “ciwon karuwa yake ga tana jin cikin kaman yana sauka ma wayyo Allah wani kalan zufa take duk uban sanyi dake akwai a kasar zufa take kaman ana zuba mata ruwan azaba haka take ji yanda tarike rigan dake jikinta kaman zata yaga shi ruwa taji mai gumi yana bi mata kafa tana dubawa taga jini ne zuwa yanzu azaban datake ji yafi gaban tayi kuka ashe kuka ma rahama ne ashe kuka ma sauki ne tagama ba ranta ko ya dawo a yanzu said ai dead body dinta yanda dai take ji a yanzu sake tahowa jinin yayi kaiiiii bata iyawa wani kalan dogon suma tayi aie masifan yayi yawa Allah “ Yasan tashi namata wahala shiyasa ko doorbell din ma bai danna ba yayi using unlocks card yabude yashigo wani hadaddan jacket ne a jikinsa brown malik yasake zama wani kato yasake kyau kana kallonsa kasan akwai kudi da hutu a wurin kyau idan yahadu da naira maza sake hadewa suke bakaman masu kyau da kirar kyau kaman malik shigowa yayi yamaida kofan yarufe ga ledan café a hannunsa yace Assalam alaikum “shiru bata amsa ba yakarasa yaganta kwance kan carpet ga uban jini gata kaman ba rai sakin ledan hannunsa yayi da zuciyarsa tawani buga da uban karfi sai jiri yayi kokarin kwasar shi yaye hulan jacket din yayi daga kansa yayo kanta yazube kan kafarsa the forget who’s he a situation dinnan he is lose and even traumatized daga kansa yayi sama wasu kalan hawaye suka zubo yace yah Allah karka daura mun jarabawar da tafi karfina yah Allah karka daura mun kaddara dakasan ba zan iya dauka ba yah Allah kaji tausayina yah Allah kasani kasan zuciyata kasan wacece ita a wajena yah Allah karka dauki nata ran kabar nawa yah Allah ka datse numfashinmu a lokaci daya kusan this is really sad 🥺kukan namiji babba babu kyau this touch my heart!duk tunaninsa fa mutuwa tayi saboda babu wurin dake motsi a jikinta wani irin dauriya da juriya yaji Allah yadaura masa hannunsa na masifan rawa da jikinsa baki daya yakai daidai hancinta wallahi baya hayacinsa bai masan abunda yake ba shiyasa yakasa fahimta dube dube yafara yi ga hijab dinta nan kan prayer mat din datayi sallarh daga zaune a parlor hijab din yasaka
Chapter 187 · 0% Book details