← Book details Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 123 OF 197

Sashe 123

Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ki duba lamarin nan ummi tace gaskia hakan baiyi ba ai saboda tsoron larura ake tahowa dawasu extra kayan inna tayi kasa da murya tace sam fa haka nan aka gina musu asibitin duk suka siyan manah manyan gidaje muka koma amma sam basu da wayewa idan kika fidda ni cikinsu tau abun nasu duk da duhun kai aciki ummi dai sai faman murmushi take ta dauki akwatin inna maryam ta taso dasauri tace bara na dauka ummi “inna tawashe baki tace kaji wata yar bafullatanar yarinya masha Allah wannan ai bazata wuce matar audu ba don dai kowa da jikinsa sai sannan inna ma ta tuno bata ga aydarh ba “dasauri tajuyo tana kallon malik tace bawan Allah ina mai dakin taka??malik yashafa kansa yace tana can gidansu inna ta gwala ido tace tau mi zai sa tatafi can ummi tayi murmushi tace ai bango daya muke hajiya ku huta duk sai muje ku dubata bata jin dadi “sai sannan dr hafsa da hibba da duk sun so su fara ganin aydarh sukayi magana dr hafsat ace subhanallah Allah yabata lafiya tace shine yallabai baka gaya mana ba?malik yayi dan murmushi yace aie taji sauki ma ban fada mata da zuwanku ba nabarshi as in surprise hibba tayi murmushi tace ai shknn nan dai ka kyauta “duk akayi dariya ummi da inna suka wuce dakin da ummi tafidda wa inna mai kyau wanda ke well furnitures anan kasa,shiga dakin sukayi maryam ta ajiye box din tafita inna ta dinga kallon dakin wannan yafi nata na can kyau duk da suma mansion ne aka siyan musu yanzu atare suke zaune da iya rabiah da inna da dr hafsa “sai dr ibrahim din da hibba a dayan side din gidan cikin jin dadi da kwanciyan hankali suke zaune “ ummi tace kuyi wanka da salla hajiya yanzu zaa shirya abinci inna tace tau ba laifi yar nan sannunku da kokari damu “ummi tace yauwa kafin tafita inna tabude box dinta dake da kaya kusan kala goma tafara jerasu a wardrobe kafin tagama tawuce bayi kaman yanda inna tafada hakane sam bata da duhun kai don kowa amfani da toilet din gidan idan ba wanda yasaba zama outside countries ba akwai wahala amma tsab inna tayo wankanta da alwallarta tafito “ ,dr ibrahim da hibba ummi tasa malik yakaisu karamin part din dake nan kasa wanda ke da parlor da bedroom da toilet yanda bazasu takura ba “dr hafsa ma dayan dakin dake kusa da na inna aka kaita “ .kaman sun saba da juna haka suka ci Abinci anan dining duk sun lura inna ma dai kusan kalan hajajju ce gata da shiga rai “ bayan sun gama abby yamike yace tau malik tare zamu tafi hadda dr ko?malik yace ehh abby tareda dr ibrahim suka fita zuwa campany steels din da aka siyan ma abby wanda malik yafasa niyyarsa yaba abby takardan yau dasafe har kwalla sai da abby yayi Wallahi da matsayin karamin ma’aikaci yake a campany yau sai gashi shine mamalakin campany baki daya “bayan fitarsu inna tamike tana kallon ummi tace mu shiga mu dubu yarinya can ummi tace tau inna da ummi da inna da Hibba sai dr hafsa suka fita zuwa gidansu aydarh aka bar su aysha a gidan maryam sai faman bakin rai take don ummi tace tazauna zataje zuwa gobe “,Oum da rufaidarh bakaramin murna sukayi dagani su inna ba bayan ummi tayi musu bayanin su waye sosai oum tadinga musu godiya da fatan alkhairi rufaidarh ma haka “inna tace Wallahi wannan sai ace yar budurwa ce itama bata haifi aida ba sam oum tayi murmushi tana daukar da kai “dr hafsat ace dan Allah akai mu wurin nata rufaidarh tayi murmushi tace kuyi hakuri bismillahn ku ai har sai kun gaji da juna kwara damuka tsaya aka gaisa ko bahaka ba “ummi tace kwarai kuwa “dakin aydarh duk suka wuce baki daya tana nan zaune kan gado tasaka wani plain gown yellow mai kyau sosai kanta babu hula tayi parking gashinta nacan kasa was my tayi kyau kaman ka saceta ka gudu “ tsohuwan apple system dinta take dubawa bude kofan akaiyi duk tunanin ta rufaidarh ce shiyasa bata daina aikin datake ba sallamar inna taji kaman a mafarki ai dasauri tarufe system din ganin dai sune dagasken ai Wallahi dagudu tafada jikin inna “inna ta rungume aydarh sosai tace karki sani kuka aida nayi kewarki bana wasa ba itama aydarh tace nima inna nayi kewanku sosai dr hafsa dake bayan oum tayi gyaran murya hade su tayi ita da hibba duk tayi hugging dinsu Wallahi batasan tayi missing dinsu har haka bas ai yanzu duk suna audio call dasu vedio call dasuna Washington “sai sannan aydarh ta sukunya tana gaishe da ummi “ummi tayi murmushi tace sannu baby aydarh tagyada kai inna tace bara kiga abar waennan muje can kasa muma ummi tace gaskia dai rufaidarh tace muje ahada muku abinci inna “dasauri inna tace wooo sai zuwa anjima yanzu muka gama ci a can “ fita akayi aka bar hibba da dr hafsa a dakin sai aydarh hibba tadinga bin aydarh da kallo “kafin tace Wallahi duk tunani na yanzu cikinki yafito sosai “dr hafsa tayi murmushi tace nalura yarinyar nan kila dai basuyi niyyar haihuwan ba yanzu “Aydarh tayi yar dariya kafin takalli hibba tace kai auntie kinga yanda kikazama masha Allah “tace itama auntie hafsa duk kunyi jiki “dr hafsat ace ai aydarh kin kara 100 kan yarda kike aydarh tayi dan murmushi kafin tace ina su iya da rabiah?hibba tace duk suna gaishe ku aydarh tace aikam muna amsawa yah dr banda shi?hibba tace mijinki ko barinsa yahuta baiyi ba yajasa “Aydarh tawara ido tace kai haba shi wannan kafan yawone ai dr hafsa tace saukin ma ke kika fada ai aydarh tayi dan murmushi “hibba tace yace manah bakya jin dadi ma aydarh tace erh nayi fever kwanana biyu a asibiti dr hafsat ace eyyerh yajikin naki yanzu aydarh tace Alhamdulilah “hibba ta dinga kallon frames din tace masha Allah auntie aydarh kedai komai naki mai kyau ne nan dakina budurwa ne kafin kiyi aure?aydarh ta gyada kai dr hafsa tace su kansu furnitures din dakin daga ita tasaka akayi mata irin nata in whole Nigeria aydarh tayi wani smile tace kai auntie “dr hafsa tace tau shi miya hana kisaka nashi frame din a daki tun kuna saurayi da budurwa?aydarh tace ai bai yason hoto fa shi “ hibba tace kuma auntie hafsa tarasa idan zatasa hotonsa sai dakinta acan dai gidanta ita dashi akwai “ dakin ma yahade kamshinsa danata da alama baa jima dagama making love baa nan mudai kuyi hakuri kubari ku karasa daga idan kuka tsaya a gidanku nan gidan oum mu ne ahtau aydarh tajuyar da kanta tana turo baki tace ah’ah fa duk yau ban gansa ba “ dr hafsat ace wasa dai kikeyi “Aydarh tace uhm kawai “ringing wayanta yayi wanda ita har tamanta ma da wayan “tana dubawa tagashine batayi niyyar dauka ba kawai ta Chanza mind dinta ta dauka murya can kasa ta amsa masa sallaman yace kinci Abinci ?kaman yana ganinta ta girgiza masa kai “baiji ta amsa bay asa shi sake maimaita tambayan “ahankali tace no yace mi zaki ci tau?tace babu “shima murya can kasa yace what of grilled meat ko hot dog? Tace the last one “yayi karamin murmushi yace ohk kafin yayi ending call din shi fa dariya sturbborness din yarinyar ke bata he loves her Wallahi,ta janye wayan a kunnan ta dr hafsat ace tau why bazakiyi jinyar baa can gidansu aydarh tayi kasa da kai tace yau nazo nan hibba tace Auntie ai kwara ta huta gida itama tunda kaman nan da four days zaku koma ba?aydarh tace erh “dr hafsat ace Allah yakaimu lafiya duk suk ace Ameen “sosai suk asha firan yaushe gamu har isha”I kafin hibba ta mike tace mun sha wuni nan fa har nafara jin bacci ma aydarh tace to ki kwanta anan manah auntie “hibba tabude baki tace shifa mijina?aydarh tayi murmushi tace hakane fa dr hafsa tamike tace muje ki sa araka mu can kofofin naku ne sai ahankula “Aydarh tace tau auntie maids tasaka ta raka su har can gidansu malik ita kuma tadawo toilet tashiga tayi wanka kafin rufaidarh tashigo ta hada maganin dazatayi mata sit bath shafe jikinta tayi da perfume as usually bata shafa komai a fuska ba amma tayi kyau bana wasa ba Wallahi “bude box din ta tayi tajawo kayan bacci masu nauyi navy blue tasaka har tafara gyara shimfida zata kwanta “sai ga kiransa yashigo har yanzu haushin sa take kaman bazata dauka sai kuma ta zauna gefen gadon tadauka tayi shiru batace masa komai ba shima cewa ki sauko ina parlor yakashe wayan sai data harari wayan kafin ta ajiye takai kusan 15mins kafin tamike tadauki baby pink din hijab dinta har kasa tasaka ta dauki wayan kafin tasaka wani black slippers masu dan azaban taushi sunyi ma kafan kyau sosai har yanzu tafiyanta sai ahankali walking very gentle and slow takarasa cikin parlor tun tana kan staircases yake kallonta kaman zai hadeta hijab nayi mata kyau sai daya ga takusa karasowa kafin ya janye idonsa kalan kayan bacci daya ke jikinsu don dais hi yasaka rigan sanyi akai “ko zama batayi ba tace gani kallonta yake underneath his breath yace kindaina gaisheni ne cuddle bug?sai sannan tace ina wuni yana kallonta yace how your body tace fine “yamiko mata ledan hot dog din da grilled meat yace gashi hadda pizza ma hannu tasa ta karba tace thanks har zata juya yayi kasa da murya yace babu komai a kitchen dinku am hungry kallonsa tayi for few seconds tayi saurin janye ido murya can ciki tace miyasa baka debi wannan ba? Ya girgiza kai yace ai naki ne kitchen din tawuce yabita da sai daya kalli ko’ina na parlor wai yaga akwai mai ganinsa yaga babu don ginin gidan ma yana iya kwana babu wanda yasan ya kwana hanyar dayaga tabi shima yabi yana shiga babban kitchen din dake nan hadda tv kaman dai nasu “yaganta tsaye ta dauki wani hadaddan unbreakable ta bude ledan tasaka hot dog daya daman kwara biyu tadiban masa
Chapter 123 · 0% Book details