Sashe 10
Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ita lokaci daya yarinya ta kwanta mata rai,gyada kai aydarh tayi batareda ta amsa ummi ba still kanta na kasa bata dago ba abby da hankalinshi sam bai jikinshi sam bai ga abunda yafaru ba kuma bai ma kalli aydarh ba balle yasan wacece tunda bama sanin nata yayi ba. Welcome sir tafada cikin sanyi da kuma raunin murya hugging dinta yayi sosai dukkansu ajiyar zuciya suka dinga saukewa zuciyoyinsu na musayyar bugawa kamshin jikinsu dana fatarsu na aikawa kowa sako cikin su ahankali ya zare ta daga cikin jikinshi yazaunar da ita kan sofa dake bedroom din nashi wanda yanayi bedroom din kamar show room shima kan sofa ya zauna tareda jawo ta ya kwantar da kanta akan shoulder dinsa yana shafa sumar kanta ta cikin Jersey veil din da tayane kanta dashi ,Zarahhhhhh yanda yaja sunanta sai da gabanta yafadi bata amsa ba sai ma kara riqe hannunshi datayi sake maimaita sunanta yayi yace zuciyata na bani akwai abunda ke faruwa wanda kike boye mun cikin sauri ta dago kanta ta zuba mashi ido kallonta yayi yace yes zarah akwai abunda ke faruwa kuma kin barni a cikin duhu girgiza kai tayi cikin sauri tana kokarin tsayar da hawayanta tace babu komai abban baby idan ma akwai ni kaina bansan ta yarda zan fara ma bayani ba kallonta yake ko kiftawa babu yace zarahhhhhhhh da dan karfi saukar da kanta kasa tayi batareda tayi magana ba zuciyarta bugawa take da sauri numfashin ta tsananta fita yake yah rabbi kaine mai kowa yah rabbi kaine mai komai yah rahaman ka gyara al’amarin nan shidai abba kallonta kawai yake ba haka yasaba ganinta ba duk sanda yayi tafiya yadawo ba yasaba riskar ta cikin walwala da annushuwar ganin shi wannan karon kuma tamkar ma bata da lapia tamkar wacce ke cikin matsananciyar damuwa da takura duk ta rame tayi haske asalin kyauwun fuskarta yasake fito tarr kamar lokacin da take shekarun kuruciyarta to mike faruwa? Mike shirin faruwa?shi kanshi yanajin wani yanayi na daban inalilahi waina illahil rajiun shine kalmar dayake maimaitawa a zuciyarshi yarasa gane kan oum sam duk yanda yaso ya lallashi ta amma abun yace tura kuka kawai take mai tsananin ban tausai zuwa yanzu hankalin shi yagama tashi yarasa ta idan zai fara mikewa yayi tsaye tareda kwantar da ita flat kan sofa yayi hanyar kofa da sallama yashiga parlor part din oum wanda yasan anan ne zai tarar da rufaidarh ko daya shigo bai ganta ba ya tambaye oum tana ina bata bashi amsa ba as well ya tambayeta ina aydarh nan ma tayi shiru sai aikin kuka take mashi duk da tasan duk dunia babu abunda ke daga masa hankali irin ganin hawayanta shi kanshi bai san iya adadin son dakewa zarah ba amma he knows that words will never enough to express his feelings on her,Mikewa tsaye rufaidarh tayi tare da fadadda fara ‘ar fuskarta tace ah masha Allah yallabai sannu dazuwa ya hanya anzo lapia? Duk tambayar da take mashi bai amsa kallon baabah dake sallarh kawai yakeyi zuwa yanzu kuma bai masan yanayin da zai kamanta abunda ke faruwa ba zama yayi cikin daya daga cikin cushion din parlor yana amsawa rufaidarh gaisuwar da tayi mashi yana tambayar su yasuke lapia lau alhamdulilah daga nan babu wanda sake magana cikin,zama yayi har baaba ta karasa sallarh murmushi tayi domin rabon data ganshi kila anyi 15yrs sam habib wani kalar mutun ne wanda shine tushe kuma shine silar faruwar komai a ahalin baki daya babu yabo babu fallasa suka gaisa duk da ba karamin nauyi da kunyar baabar ya keji ba shi kanshi yasan duk abunda ke faruwa amma sam bai damu ba shirune yabiyo bayan gaisawar dasukayi da abban kowa da yake sakawa a ranshi.Nikam adda aysha wai wacece wannan wadda suke tareda hajajju da yah malik? Naga duk a tare mu ka gansu koh tau amma adda mike faruwa ne hajajju na ta kuka kuma naga ummi da abby sun bisu tareda yah malik , ajiyar zuciya aysha tasauke tace dan Allah ku rabo dani kawai kuyi adduar Allah yasa komai lafiya Ameen suka amsa can maryam tace nikam daman na kara ganin ta ta burgeni Sosai ta iya gayu wallahi kallonta halime tayi tace nima haka wallahi aysha dai murmushi kawai take so take ta tuna idan tasan fuskar amma takasa. Wata irin zabura hajajju tayi gani gidan dasuka kazo da sauri ta kalli malik sannan ta juya ta kalli aydarh tace inalilahi waina illahil rajiun yau naga abunda ya isheni bai ishe Allahnah nan kuma ina ne jama’a ? Babu wanda ya tanka mata cikin su aydarh har wani ajiyar zuciya ta sauke ganin sun dawo gida kamar kan kaya take a cikinsu duk da babu wani datti ko alamar wahala a tattare dasu amma sam ta kasa nutsuwa cikin su cilla motar yayi cikin gidan yana mai tambayar kanshi tau miya faru miyasa zasu zo gidansu? Babu mai bashi amsar tambayar shi har ya paka motar cikin jerin motocin dake jere a parking space din aydarh da kamar jira take dasauri ta fita daga cikin motar kamar jira take tafita marar ta tawani irin murda har sai da ta saki siririyar kara dasauri ummi tace subhanallah tare da rike ta,wani irin murmushi hajajju tayi tace tau riketa mu karasa still malik bai fito daga motar ba yana ta kallon ikon Allah shi kam yau mamaki kala kala yake Sha, tsawa hajajju ta daka masa tace kai da baza ka fito ba hala wani abu yasami kafar ta ka ? Shidai bai ce mata komai ba yasa kafa yafito daga motar ya mara masu baya yana bin tsarin gidan da kallo tsaki yaja ganin yar ummi ke ta lallaba yarinyar kamar kwai itakuma sai wani narkewa take kamar wacce ke ciwon mutuwa. Wani irin harbawa zuciya abba tayi iya gigita ya gigita cikin wani irin yanayi yake binsu da kallo musamman malik dayake iya ganin zallar tsananin kamarsu dashi Abby yakasa saka kafarshi ma cikin parlor wani irin iska ke kada duk illahirin jikin shi wani sanyi ke ratsa zuciyarshi da ruhin shi,hajajju takaraso tane mi kujera ta zauna kusa da baaba da oum rufaidarh ma karasawa tayi ta taho da ummi dake rike da aydarh ganin yarda ta tsaya tsaye kamar babu numfashi a jikinta tsabar yanayin da ta shiga still bata saki aydarh ba ahaka suka zauna itama aydarh bata nemi hakan ba domin wata nutsuwa ke bin jikinta har cikin veins dinta wani sanyi ke ratsawa duk abunan abba bai lura da aydarh dake jikin ummi ba oum kau tun shigowar su tazuba masu ido tana jin wani rahama ta ko ‘ina to mi hajajju tayi haka dayasa komai ya cika tamkar gaske? Hannu abba ya daga yana nuna abby cikin rawar murya da tsoro yake furta ya..y…yarh ya…y..yarh kaine ko idona ne daman yayah kana adamawa har yanzu? Malik dake kallon su tamkar idonshi zasu fado yarasa gane kan komai hankalinshi da tunaninshi baki daya sun gaza fahimtar komai anan tsaye yake ko zama yakasa haka shima abby a tsaye yake yana jinjina girman da kuma ikon Allah wacce kaddara ke son tadawo baya wacce gaskia ke son bayanna kanta ashe suna da rabon sake ganin juna a duniyar nan Duk da yasha mafarkin hakan kuma kullun cikin ba ummi kwarin gwiwar faruwar hakan yake amma sam baiyi tunani yanzu ba baiyi tunanin kwana ku saba,Mikewa tsaye hajajju tayi tare da gyaran murya tace duk ku tsaya kowa sai wani gwale gwalan ido yakeyi ku da ko abunda yakawo mu nan din baayi ba har kun fara wani yan sane sane ku zauna kuji abunda yatara mu nan kafin ku cigaba da wannan ya tunane tunane ahtau ku tsaya kuji jafa’in da yaran ku suka kwaso zama sukayi kowa na mamakin maganganunta cikin abby da abba da ummi baki dayansu ta daure masu kai wasu yaran nasu?oum dai kanta na kasa itama rufaidarh haka while baaba hajajju take kallo tareda yi mata alamar datayi shiru ita zatayi magana dasauri hajajju tafashe da kuka tace aaa yayah wllh aaa dole nayi magana ki daina hanani dole nayi magana kowa ita yake kallo cikin su,kafin takira sunan abba tace habibu kaga wannan sai sannan abba yakalli direction din ummi da aydarh da hajajju ke nuna mashi, nagani hajajju kiyi magana manah kin sani a duhu mitsi mitsi da ido hajajju tayi tareda gyara zama tace tau tunda ga farko har karshe zan zayyana duk abunda yafaru domin niba’a munafurci dani ba oum kadai ba hatta rufaidarh da baaba saidai da hankalinsu ya tashi sun san halin hajajju tsaf zata iya watsa duk wani shiri nasu ta fadi gaskia amma kau da sunyi dana sanin involving dinta a case din sake fashewa da kuka tayi cikin muryar dattako abby dasai yanzu yayi magana tunda suka shiga yace hajiya kamata yayi kuyi magana ba ku dinga kuka ba duk kun bar mu a cikin duhu wani abu ya farune mutuwa akayi ko mai? Yoo Allah na tuba ibrahin ba kwara mutuwa ba da zagin da yaran nan suke shirin jawo manah. Jawo manah ba still dakin babu wanda yayi magana kowa kallon hajajju yake banda rufaidarh oum da baaba da gaban su ke ta lugude hantar cikinsu na kadawa jiran jin abunda hajajju za tace, suke. tana matsar kwalla Takai 5mins ahaka sai tayi kasa da murya tace tau Alhamdulilah haka naso kuma haka na bukata mu hadu baki daya pameli domin mu yanke hukunci tare na’am shine abunda abby yace tare da gyara zama yana kallon hajajju gyaran murya tayi “tace tau saidai fa kuyi hakuri ita zuciya bata da kashi yara ne ka haife su baka haifi halinsu zamani ne yazo da haka habibu mai mace kuma kullun mai mace shi ake cuta kai zaka lallaba ka rufawa kanka da rayuwar ka asiri ka zubda makaman yakinka ka bada hadin kai abba dai bace komai duk a birkice yake sauraran bayanan hajajju, “sai kuma ta kalli abby tayi kasa da murya tace kai kuma sai ka goye bayan gaskia kayi adalci “zuwa yanzu jikin abby yagama yin sanyi yace in sha Allah hajajju zan zamo mai adalci a duk hukunci da zaa yanke,wayar ta fiddo daga