← Book details Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 113 OF 197

Sashe 113

Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

mata? Aysha tayi shiru maryam da halime duk sun tsore suna kallon aysha alaman tayi shiru ko kallonsu batayi ba tafara bawa ummi labarin tunda ga farko har zuwa dawon wansu ummi takallesu fuska babu alaman wasa tace oh naku rashin hankalin har yakai matsayin haka shi malik din yana ina?aysha tace rushing yayi yadauko equipment din sai muka fita ummi tace babu wacce ya daka cikinsu?aysha tace eh ummi tace bai birgeni ba shashashan yara mararsa hankali da kunya ku fice mun anan “maryam da halime sukayi kasa da kai duk suka mike ummi tace gida zaku wuce fa bana son ganinku a asibitin zamu hadu gidane “halime tace dan Allah ummi kiyi hakuri baza mu sake ba fa in sha Allah kuma bada gangan mukayi ba kiyi hakuri ummi ta kalli aysha tace ina key din gidan?aysha tace yana wajan abby ummi tace ku samesa a reception din ku karba ku tafi a keke aysha tace tau shknn ummi Allah yabata lapia na daura girkin dare ne?ummi tace ku sa iya naku kawai basai ankawo ba “aysha tace sai da safe ummi tace Allah yabamu alkhairi.hajajju tace tau kadai ji duk wani take takensa kenan Wallahi “malik yayi shiru yace tau hajiya shi abby mi yace hajajju tace minene wani abby wai ibrahin kake nufi? Malik yace erh shi fa hajajju tace babu abunda yafada wannan kwara ma yayah kulu zatayi magana habibun yamike yawuce fat dinshi babu ta kan wanda yabi shi dan banza “ malik yace nufin sa kenan nasaketa wai? Hajajju tace kaima kafada “haka yake nufi malik yace gaskiya nidai hajiya kwara ace zaa kaisheni da ace nasaketa bazan iya ba gaskia “hajajju tayi shiru tana kallonsa tace tau karka kuskura ko dawasa ka bi umarnin su “malik yace yanzu fita zanyi zanje cikin gari nadawo idan nadawo sai nasameki muyi magana hajajju tayi kasa da murya tace tau daman kazo manah da kaza dai “ita ma matar ai kaman jego take kyau dai da nama malik yace kedai kice ke zaki ci yarinyar da bata ma iya cin abinci balle kaza “hajajju tayi wani kala da murya tace kaji dan kwal uba abunda kayi mata wane rai ne zai sake morowa bayan ita da Allah yasa da sauran kwanta gaba malik yashafa kansa yace tau ke ina ruwanki hajajju tace ga ruwana nan ko lefe bakayi mata ba ni idan nice ita dubun ka ashirin zan mayar maka ka sakeni na huta da wannan jaraba ace ka kusance diya sai ankawo ta asibiti duk ina dalili malik dai juyawa yayi yana dan murmushi kaman ba yanzu tagama cewa kar yasake yasake ta ba amma yanzu har ta Chanza magana “hajajju bata koma dakin ba ta nufi ofis din dr raudarh “ tana shiga dr na zaune tacire labcoat din jikinta tana danna waya “tana ganin hajajju tamike tsaye tace oyoyo hajiya sannu da zuwa “hajajju tace yauwa ramda ya gidan? Dr tace lafiya lau hajiya ya jikin aseeyarh hajajju tace wane jiki yarinya dai yagama da ita dr tayi murmushi tace aaa fa hajiya kawai dai bai bi ta ahankali ba “hajajju tace yanzu dai gata can bacci kawai take tsaban wahala billahi dr tace eh ai ance faduwa tayi shiyasa tayi fami mijin ma da kansa ya gyara wurin hajajju tawara ido tac eke dan mahammada rasulilahi?dr tace eh hajiya amma yace mun bawani abu bane hajiya tace yau muna ganin jarabawa mudai billahi yarinya taga rayuwa wayyo Allahnah dr tace bbu komai Allah yabata lafiya hajajju tace Ameen kafin tace kinsan fa can kasar yake aiki dr tace wacce kasar hajajju tayi shiru tace kingani ma fa namanta Wallahi dr tace eyyerh Allah sarki hajajju tace shine babba a can asibitin kaf likitocin turawan nan kasan sa suke a asibitin dr na murmushi tace masha Allah Allah yasa albarka hajajju tace Ameen kafin tace barakallah ramda kema da kyanki kamar mu a gari dr tayi yar dariya tace nagode hajajju tace shima mai gidan naki likitane? Dr tayi kasa da kai tace aaa hajiya “hajajju tadinga kallon dr ganin kaman mood dinta ya chanza hajajju tace aikin mi yake shi?dr tace dan siyasa ne hajajju tawashe baki tace masha Allahu yaran ku har nawa? Dr tace yan biyune hassan da ussaini hajajju tace Allahu akbar tau suna ina?dr tace suna wajan mamana hajajju tace ke aiki bazai bari ki rike su ba komi? Dr ta girgiza kai tace aaaa har kwalla yakawo idonta tace mun rabu yasake ni kuma bazai rike su ba kawa isai kuka ya kwace mata ta fashe da kuka hajajju tamike da sauri tana jawo dr tace inalilahi waina illahil rajiun asha ka mamma dai daga ji bakaramin mugun abu yayi miki ba ramda kiyi hakuri ki kwantar da hankalinki in sha Allah dan banzar zai gane kinji Allah ya watse masa karama ya yaye masa albarka ai suma yan biyun tunda bada su kikaje gidansa ba dasau ki maka shege kotu ya mika masa diyansa tunda dan wiwi ne dan iska “ dr data cigaba da kukanta tana girgiza ma hajajju takai tace Wallahi hajiya ina son yah Sulaiman Sosai kuma mamana bazata bari nakoma wurinsa ba ni kawai ina sonsa saboda ba laifinsa bane Wallahi hajiya “hajajju tayi shiru tana patting bayan dr tace kwantar da hankalinki kinji ramda zanyi iya kokarina naga komai yawuce in sha Allah karki damu kinjini kwantar da hankalinki ki rike yan biyun Allah yayi musu albarka kinji ni daga mayi magana kiyi hakuri dr ta goge hawayenta kafin tamike tace nagode Hajiya muje sai na raka ki hajajju tace Wallahi aaa ramda da kin barsa kiyi hakuri dai don Allah dr tace babu komai hajiya muje har dakin dr raudarh tarako hajajju kafin ta duba aydarh ta tambaya ina malik din ummi tace maybe yafita “ummi tace dr zuwa yaushe za’ayi discharging dinmu? Dr raudarh tayi shiru tace bara mugani maybe ko zuwa gobe ko jibi in sha Allah ummi tace Allah yakaimu lapia “dr tace Ameen “ tajuya tafita hajajju takalli ummi tace ai yanzu nakada audul nace yaje ko dan kazan nan yar daya ya siyo baiwar Allahn yarinyar nan ummi tace gaskia kam hajajju tabude kulan pepper chicken din ganinsa kadan badayawa ba tace wannan dai tsaban bakin hali ne billahi ace komai bazaa kawo kaca kaca sai cin mutun daya yoo du kinda dalili jama’a cikinsu wacce mai dan banzar rawan kanne ta kawo nama? Ummi tayi shiru kafin ahankali tace maryam ce hajajju tace ai wannan yarinyar dakyar idan zatayi abun arziki ko da kuwa ibrahin mai kudi yazama nidai shawara ta daman audul daukarta yayi suka koma can kasar ummi tace haba hajiya tayi mi acan din ?hajajju tace ni fa dadina dake akwai kauyanci har yanzu dan wayewan nan nakai yara turai baki santa ba “miye dan yatafi da ita kinga sai mu tafi tare gudun ma ace anbar yara daga su sai turawa acan kasar “sai lokacin ummi tayi yar dariya saboda tafahimce abunda hajajju ke nufi atafi da ita “ummi bata Sake magana ba tayi shiru.ummi tace da kin daure baby ki kara ko kadan ne kinji aydarh da kaman zatayi kuka tace nakoshi “ummi tace tau sannu aydarh ta gyada kai kawai tanayin kasa da kai saboda ko son hada ido da ummi batayi ummi duk na lura da ita sallama yayi ya turo kofan dakin ahankali yashigo idonsa kanta sai kallonta yake as if his life depends on her “ummi dai kallo daya tayi masa ta janye ido aydarh duk da taji alaman shigowansa a jikinta amma bata dago ba “yace ina wuni?ummi tace lafiya “yakarasa kan drawer ya ajiye ledan kasassan kazar sai ga hajajju tabude kofan toilet tafito malik yadan kalleta kafin yace barka dai hajiya hajajju tace dole kace manah haka saboda ka cuce mu ka hada mu da dan banzar zaman asibiti ina dalilin wannan abu ni sam hakan bai mun ba daurewa kawai nake saboda na lura iyayanta ba saiti garesu bai ta kuma asiya ayi idan akace haka za,ayi ba dan karamin cutar ta akayi ba “malik dai baice komai ba balle aydarh da kanta makasa ma ummi tace baby ko nasaka miki kazan ki daure muryanta dayayi kasa sosai na alaman rashin lafiya tace zanci anjima “ummi tace ohk”hajajju tace audul ko har ka mance da zancan kazar ma? Malik yace nasiyo hajajju ta bude baki tana kallonsa tace da ban tambaya ba babu wanda zai ce mun gashi tau daga kai har uwar taka har ita matar taka tsoron Allah yayi muku karance said ai ace ubangijin isah da musa ya shirya ku “tafada tana jawo ledan tabude kazar “ta hau ce “kusan daya taci ita kawai saiga oum da rufaidarh sai wata maid biye a bayansu rike dawani classy basket na yan gayu kana gani kasan kayan campany daban dana gida don foreign ne na kirki ta ajiye kafin tafice ta barsu gaisawa sukayi da ummi kafin ta gaishe da hajajju itama rufaidarh haka hajajju dai ta mike tace bara tayi waje Saboda malik data aika siyan fura “ ummi tace ina yallaban?oum tace yana gida jikin neb a dadi inaga stress ne ummi tace Allah sarki ina ganin hakan ma ne gaskia Allah yataimaka yabada sa’a oum tace Ameen duk datafada ne amma abban lafiyansa lau kawai dai yarufe part dinsa ne oum bata taba ganin yayi fushi irin haka ba har da ita “can tace ina yayah ibrahim din? Ummi tace sunje gaisuwa amma yanzu kingan sa nan ba jimawa “rufaidarh ta matsa kusa da aydarh dake bacci ta zauna tana kallonta kusan 10mins jefi jefi suke dan magana can sai ga aydarh tabude ido tana ganin rufaidarh tayi yunkurin tashi duk taji zafi sosai amma tadaure tana ciza lips dinta nakasa rufaidarh dai na kallonta haka oum ma na kallonta ta kasan ido ummi tayi saurin tashi tace sannu baby kin tashi ko zaki shiga toilet ne sorry aydarh ta girgiza mata kai kafin tace ah’ah ummi “ganin yanda ummi ke kula da aydarh yasa oum jin wani sanyi aranta “rufaidarh ma kallonta takeyi da dan murmushi ummi tace bara naje rufaidarh sai ku samu ku gaisa sosai “rufaidarh tace ai da kinyi zamanki babu komai
Chapter 113 · 0% Book details