← Book details Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 197

Sashe 82

Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tace Ameen kafin ta mike tace auntie bara nayi sallarh hibba tace tau shknn shiga nima banyi sallan ba aydarh tace ina ma da alwalla fa hibba tace tau shigo bedroom din “ Aydarh ta girgiza kai tace kibani prayer mat zanyi anan kawai hibba tace tau shknn abun salla takawo mata kafin ta wuce bedroom din ita sai datayi alwalla kafin tayi sallan “har ta fito aydarh na zaune kan prayer mat zama hibba tayi kan kujera tana kallon aydarh tace auntie aydarh ko muyi wainan flour shi nake son ci? Aydarh ta gyada kai tace tau shknn auntie hibba tace tau yallabai yana ci ne? Aydarh ta girgiza kai tace erh yana ci amma ba sosai ba gaskia ranan auntie hafsa ta yi manah amma bai ci ko biyu ba nidai kam ina so sosai, hibba tace dr kam na so Sosai ko sai ki girka masa ko jallof din macaroni? Aydarh tace ah’ah auntie kawai ayi wainan idan mukaje gida nayi masa girkin “hibba tace aaaaa aydarh kar nasake ji kar ki sake barin mijinki yawuce lokacin cin abinci bai ci ba saidai idan baya nan yanzu kinsan sai sun kwaso yunwa ga rana kafin su dawo kuma har sai kunje gida kafin kiyi masa girki?aydarh dai tayi shiru tana wasa da rings din hannunta bata ce komai ba Hibba tace muje sai kiyi greating kayan miyan akwai vegetables ma hadda kifi sai ki saka masa “Aydarh dai tace thank you auntie kitchen din suka shiga Hibba ta ba aydarh duk wani ingredients din da zata masa girkin “ kafin ta cigaba da harkan wainan flour ta “Hibba dai takasa dauke idonta daga kallon aydarh ganin yarda take girkin komai tsaf komai cikin kwanciyan hankali, sunayi suna fira aydarh dai sai kokarin rike numfashin ta take saboda kamshin wainan flour dake damun ta “can dai tafara jin numfashin ta na seizing ta dai daure tayi shiru hibba kam sam bata ma lura da abunda aydarh keyi ba labari kawai take bata cikin kwanciyan hankali duk da aydarh bata amsata tacigaba da labarin daman tasan haka aydarh keyi “ can dai tafara tari ahankali ahankali hibba tace sannu auntie aydarh mura neba?aydarh ta girgiza kai tana cigaba da tarin ta hibba tamike ganin yarda aydarh ta rike chest tana tari non stop ga zufa dayafara keto mata dasauri takashe camping gas din datake suyan wainan flour daman takusa gamawa,karasawa tayi kusa da Aydarh tana tambayar lafiya ko sarkewa tayi cike da karfin hali aydarh ta girgiza kai idonta yayi ja tana jan numfashin ta dakyar “har tama kasa breathing din da kyau hibba data gama rudewa tace aydarh ko dai kinada asthma??????da kyar aydarh ta gyada mata kai aikau dasauri hibba takama ta suka shiga parlor banda inalilahi waina illahil rajiun babu abunda hibba ke fada sai jera ma aydarh sannu take tama rasa yarda zatayi ita Wallahi ganin yarda aydarh ke fighting da numfashin ta yasa hankalin hibba karasa tashi kama aydarh tayi tana kara gudun fanka kafin ta sake ta duk ta rude tana dage curtains din parlor da wani irin speed tashiga daki tayi dialing number dr ibrahim bugu daya ya dauke “yawani langwabar da murya yace did you just started missing me roohi?a rude tace dr kuyi sauri ku dawo Wallahi banyi tunanin aydarh is asthmatic patient ba kaurin wainan flour yasa asthma tashi dan girman Allah ku dawo “kashe wayan tayi ta koma parlor tacigaba da jera ma aydarh sannu Wallahi iyakan tashin hankali Hibba ahankalin ta yatashi bata masan taya zata taimaka mata ba kafin su iso duk ta gigice “ addua tacigaba da tofa mata “ .wallahi malik gani yake mai keken baya sauri du kinda hankalinsa yayi dubu yatashi dr ibrahim ke ta basa karfin gwiwa yayi hakuri ba abunda zai faru da ita amma ina bayaji sai ruwan masifa yake zubawa mai keken “shidai bawan Allah sai iyakan bakin kokarinsa yake daga mai keken har dr ibrahim sun masa uzuri saboda ganin duk yarda ya gigice “sunata basa magana “ ai suna isa kofan gidan dr ibrahim ko jiran mai keken ya tsaya bai yi ba ya dire “cike da sarfafa yake tafiya daga kansa kaga cikaken karfafan namiji mai ji da karfi gashin kansa har kwantowa yakeyi “sallama yayi yashiga aydarh na rungumai jikin hibba duk ta gama galabaita, tana ganinsa “kwalla yasauka idonta ai hannu yasa kawai yayi sama da ita kafin hibba ta mike ta zira mata hijab dinta “kaman baby haka ya fita da ita rike hannu dr ibrahim da bai sallami mai keken ba yabasa hanya shiga da ita rike a hannunsa duk ya rude ya gigice dr ibrahim yashiga gaban keken ,mai keken ya tayar suka wuce clinic”dr ibrahim yakira hibba yace ta rufo gida tasamu keke ya kawota clinic kafin kashe wayan “ Wallahi malik kaman ma ba dr ba don yakasa yin komai ma kallonta yake kawai har suka isa clinic din yafito da ita 2k dr ibrahim yafito ya mikawa mai keken yayi masa godiya da adduan Allah yabata lafiya dr ibrahim ya amsa masa kafin ya rufawa malik baya ,emergency room din malik yashiga ya kwantar da aydarh kan gado hawayen dake fita a idonta da yanda take fighting da breath dinta yasa jin wani irin rauni kawa isai hawaye sharrr Wallahi dr ibrahim kasa boye mamakinsa yayi malik kuma kuka?ganin malik bai ma da niyyar yin komai don dr ibrahim ya fahimce malik yamance waye shi yasa kiran nr saratu dake nan reception dr hafsa bata kai da zuwa ba,bai ce wa malik Komai yabarsa nan rike da hannuta yayi kasa da kansa itama ta rike hannunsa sosai kaman zaa kwace mata shi, dasauri dr ibrahim da taimakon nr saratu sukayi kokarin daidaita numfashin aydarh cikin few minutes sukayi mata allura cikin abunda bai fi ten minutes bacci ya dauketa ahankali tafara ajiyan zuciya a wahale kadan kadan sai lokacin malik da idonsa yayi jawur ya dago kai,yana kallonta ko dauke ido babu hannunsa yasa yagoge mata hawayen dake nan a fuskan ta kafin shima yadago hannunta yarike yadinga goge hawayen fuskan sa da hannunta “ sai kallonta yake wani irin kyau tayi masa mai daukan hankali lashes dinta sun tattare wuri daya wanda ruwan hawaye ya jikasu, dr ibrahim daya shigo dakin ya kalli malik yace katashi muje masallaci in sha Allah she will be alright yallabai ai kasani dai malik kaman bazai tashi ba dan kona second daya baiyi missing kallon fuskanta ba ahankali yasaki hannunta kafin yasaka Hijab dinta ya rufe mata jikinta dr ibrahim dai sai kallonsa yake, ahankali yake bin bayan dr ibrahim duk yayi wani kala a bakin kofan clinic suka hadu da hibba dauke da basket din Abinci gaishe su tayi kafin fuskanta cike da damuwa ta tambaye su ya jikinta dr ibrahim ne ya amsa mata da sauki kafin ya nuna mata dakin yace tana ciki ta samu bacci hibba tace musu tau kafin da sauri ta nufi hanyar dakin dr ibrahim yabi ta baya yana karban basket din hannunta shidai malik yayi shiru ya lumshe ido,sai da yakai mata basket din kafin yadawo ya tarar da malik nan inda yabar sa suka wuce masallacin magrib,hibba na shiga ta zauna kan plastic chair din dake dakin tayi shiru Wallahi duk tadamu sai taga kaman ita tasaka ta cikin wannan halin gani take kaman ita taja mata duk wahalan,basu suka dawo bas ai da aka gama Isha’I ,hibba nayi musu sannu da zuwa dr ibrahim kawai ya amsata yana tambayar ta ya mai jikin ta farka?hibba ta girgiza kai tace aaaaa bata farka ba fa bacci kawai take dr ibrahim yace tau masha Allah Allah yakara lafiya Hibba tace Ameen kafin tace bara nasaka muku abincin dr ibrahim yace bara muje office nan kar motsin mu ya tayar da ita, yakalli malik yace yallabai muje office “sai sannan malik yadago ya girgiza kai yace kuje ibrahim zan zauna da ita zanci abincin anjima in sha Allah dr ibrahim yayi shiru yace tau shknn yallabai Allah yabata lafiya, malik yace Ameen hibba ma addua tayi masa kafin ta dauki warmer wainan flour da plate sai rubber yaji tabar dayan warmer shape pasta dasauran plates din tabi bayan dr ibrahim bayan fitarsu malik ya kwantar da kansa bisa gadon ya lumshe ido ,har wajan ten bata farka ba lokacin har dr hafsa ta iso “dr ibrahim yayi masa sallama yace zasu tafi in sha Allah gobe daga masallacin asuba zai shigo ya sallamesu ya mikawa malik sauran drip da alluran ta na daran tunda in sha Allah da angama dosage din suke nan hibba ta kalli malik kafin tace am sorry yallabai bada gangan nayi ba,malik yayi murmushi yace ba komai amarya mungode sosai Allah yasaka da alkhairi hibba tace babu komai yallabai Wallahi duk anzama daya. Sai wajan karfe sha biyun dare aydarh tafara bude ido ahankali kanta yayi mata masifan nauyi “ahankali tasauke idonta kansa hannunsa rike da hannunta dake da karin ruwa,ya kifar da kansa kan gadon hannunta ta dago wanda babu karin ruwa ta taba fuskan sa da sauri ya dago kansa “kana ganinsa kasan bai da kwanciyan hankali dasauri yakara rike hannunta yana jera mata sannu ita dai ganin duk ya gigice yasa ta dinga kallonsa da idonta dasukayi laushi kallo daya zakayi mata kasan ta wahala a yau din nan “ahankali tabude baki tace zanyi fitsari tafada tana kallon drip din dake sa mata mikewa yayi dasauri yakama hannunta “kaman mai tsoro ji mata ciwo ahankali ya cire mata drip din kafin yasa hannu ya dakata jikinta babu karfi ko guda, ya dinga jera mata sannu kafin yasa hannu ya dauke ta daf yayi hanyar toilet da ita toilet din dake wanke very neat “ya daura ta kan sit kafin ya dage mata riga zai taimaka mata “dasauri ta rike masa hannu tana girgiza kai kafin ahankali tace zanyi ka fita, malik bai ce komai ba ya juya yafita yana jiranta bakin toilet din bayan tagama tace naga ahankali dasauri yashiga toilet din ya daukota kaman yarda yashiga da ita ya kwantar da ita kan gado kaman wanda zai ajiye kwai “ita dai takasa daina kallonshi “drip din ya mayar mata tadan runtse ido kadan alaman taji
Chapter 82 · 0% Book details