Sashe 20
Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
mugun karfi har sai da aydarh ta mike tana kallon kofar wani irin harara tabi kofar dashi kamar idonta zai fado taja siririn tsaki, duk wani kala take ji amfani da riga daya dakuma brassiere daya datakeyi “she wish all this was dream ba reality bane, duk wani kala take jinta kamar wata daban ba ita ba she is totally lose take ji, ita salmarh da Doctor ashraff sukayi wa sharri irin haka “and without any investigation kuma suka saka aka koreta ba koran kawai ba hadda daura mata aure da waccan mutumin da bata ma sani ba, she didn’t have anyway to go “bata dakowa a duniyar batasan yanzu idan ta gudu daga wurin shi ina zata kuma ba she promise herself bazata sake komawa gida ba , she has no other option but to stay!” Zuciyar ta,tasake maimaita kalamanta na karshe, hawaye sharr suka zubo daga idonta.Tare suka shigo da Doctor ibrahim bayan sun dawo daga ganin gidan, ahankali ya turo dakin da sallama Doctor ibrahim na mara masa baya “ kuka take fuskar ta tayi jawur eyelashes dinta sun jiqe sun tattare waje daya hakan yaba idon damar fito da asalin kyawu da girman da Allah yabasa “ Doctor ibrahim yakalleta cikin few seconds ya dauke idonshi sannan ya juya ya kalli malik dake jingine a kofar dakin shima kallonta yakeyi ko dauke ido babu cikin wannan yanayin fuskan nashi ba yabo ba fallasa, duk da suna shigowa ta saukar da kanta kasa hakan bai hanata jin kamar ana kallonta ba, bayan hannu tasa tashare hawayenta tass sai sauke ajiyar zuciya take, Doctor ibrahim bai ce komai bah aka shima malik din duk shiru sukayi Doctor ibrahim a zuciyarsa yake tambaya tau mi yaakayi mata na kuka?baya son zagewa a lamarin su shiyasa yaja bakinsa yayi shiru, sake dubu bugun zuciyarta yayi yaga komai daidai, file dinta ya bude tare da dubawa ya rubuta masu takarda sallama. Malik ya sai ke kallon Doctor ibrahim yace taya Doctor zaka ce basai nayi biya ba naga nan din private clinic ne, kuma kace mun bana ka bane “dr ibrahim yayi murmushi yace babu komai wllh nasan da haka idan wata yayi sai a fidda a salary na, Malik dai hakan sam bai mashi dadi ba domin ya lura shima dr ibrahim kamar bawani hali garesu ba “idan kau suna da hali bazai yiyuwa ba ace da kwallin shi na degree kuma ma medicine ya karanta ace yatsaya yana aiki anan din dake kamar chemist,” Malik yace nagode Allah yasaka maka da alkhairi “ dr ibrahim yace babu komai yanzu kaje ku shirya sai na tare mai keke ya kaiku can gidan, in sha Allah da magrib sai nashigo akwai sakon da zan kawo maku,malik yace sako kuma dr sako nami?dr ibrahim ya girgiza kai yace kawai dai sai nashigo, fita malik yayi yashiga dakin “zaune take tacire veil din kanta fever dake jikinta ta sauka sai ciwon kai kadan kadan zafi takeji hakan yasata cire veil din, kanta datayi parking a keya daga gaba an rabashi biyu yayi wani musulmin kyau sai shining yake kamar wace tafito daga shagon saloon yanzu , jin alamar shigowar shi yasata saurin mayarda veil din a kanta tana cusa kanta tsakanin kafafunta ita ala dole bata son ko ganinsa, toilet ya wuce direct dan bai manta maganar Doctor hafsa ba to miye abun da tace tajika a bayi, taba kofar toilet din dayayi yasa aydarh saurin dago kanta domin ta san pant dinta na ciki,wani irin yankewa gabanta yayi yafadi to ya idan yaga pant din ta fa kuma jikinshi hadda stain,ko a gida rufaidarh ce kawai ke wanke mata pant shima sai idan ciwon nata yaci karfin ta duk ranar da oum ta taba mata pant kau dasunan wankewa kunya take wuni ji domin bata son kowa yaga private abunta abunda tsani wani gaya jikinta ko daoum ce kau har ta da rufaidarh ko bata da lapia saidai a taimaka mata akama ta taje toilet din ko ta shirya shi ma saidai adinga mika mata abubuwa, har yasa kai zai shiga,yace wannan soft muryan nata na baby’s ahankali kamar bata so na waje yajita tace “stop” tsayawa yayi bakin kofar bai juyu ba kuma bai ce komai ba almost 1min suna haka ganin baza tayi magana bayasa juyuwa cikin husky voice din sa yace didn’t you need anything? Bata dago kanta ba ta girgiza kai, shima mamaki ma take bashi fa hakan yasa shi folding hannunshi a kirji this time around kaf waennan idon nashi na kanta yakafe ta dasu ko janyewa babu,ahankali ta sauko daga kan gado ta saka flat shoe din ta tun wanda ta fito dashi daga gida, shidai kallonta yake ko kiftawa babu ta gyara zaman veil dinta, tana tafiya kamar bata son taka tiles din dakin jikinta sam babu kware ga duk yau bata sa ma cikin ta komai ba, har tazo inda yake tsaye ba dauke idonshi kanta ba, kanta na kasa kamar mai tsoron taba handle din kofar toilet dinta tasa ahannu ta murda ahankali ta shiga, sannan ta mayarda kofar ta rufe,ajiyar zuciya ya sauke sannan ya koma kan kujera ya zauna babu abunda suka bata Ko abunda zai shirya bags din su ne kwara biyu kacal kuma hade suke waje daya, pillow da bargo da tabarma da warmer din duk na dr ibrahim ne yasan zai sa a kwasa a mayar gida, kwata kwata jikinta is weak ahaka ta daure ta wanke pant din tass da detergent ta dauraye shi ta shanya saman wani karfe na toilet din, Ahankali take takowa cikin dakin tafiya take kamar da gaya tafiya take without making any sound, kafafunta yake kallo so yake ko sau daya ne yaga ta hanyar da zai shaida cewa bataji ko zata iya aikata abunda akace tayi kuma shine uban dan “kafin su sauka kano ya yarda ya amince amma zaman da sukayi na kwana daya ya karance halinta tsaf bata da sakin jiki Ko fuskar dazata bada damar faruwar hakan, kawai dai yasake tabattar dacewa kaddara ce kawai ta rayuwar su ahaka. Miyasa baki ci abinci ba yafada yana tsare ta da idonshi da babu alamar wasa fuskar nan tasa a daure, hannu tasa ta goge hawayen fuskar ta ahankali tace na koshi,bai sake kallonta ba yabude “warmer din yazuba mata white rice da stew ya mika mata” bata karba ba ya dire abinci kan gado sannan yace eat! Ahankali tasa hannu ta dauki abinci tafara ci kamar tana shan magani tanayi tana goge kananun kwallar dake sauka a idon,yana kallonta bai ce mata komai shima abinci yasa yafara ci domin yayi alkawarin mance duk wani damuwa a ransa sosai yaci abincin , har yanzu bata ci ko rabi ba, shidai Malik ya cigaba da ninke ma dr ibrahim bargon sa, can ya kalleta yace kisaka hijab dinki idan baza k ici abinci ba mu wuce, ture plate din abincin tayi kamar tana jira, dr ibrahim yayi ma dan sahun kwatancan idan zai kaisu yazaro 1k a pocket dinsa yabashi malik zuwa yanzu har bai iya irga a dadin alkhairin da dr ibrahim yayi masu har yagaji dayi masa godiya, yace Doctor ga bargon can da pillow da tabarma sai acewa iya mungode Allah yasaka da alkhairi, dr ibrahim yace aaa fa malik ai na kune nason kuna bukatar su,malik yace aaaa Doctor iyakar abunda kayi manah mungode dan Allah ka barshi, dr ibrahim yace ma mai dan sahun tada babur din ku wuce, madam nasan tana da bukatar hutu anjima zan shigo Allah yakara sauki, daga haka mai keke ya ja suka tafi.Anguwar sam babu hayaniya duk dacewa anguwar masu karamin karfi ce sosai kasancewar gini anguwar kusan duk unfinished buildings new asu sa plasta babu shafe balle paint wasu kuma ko kofar kirki babu “kofar wani gida ya tsaya duk layin shine babba duk dacewa gidan kofa ce amma kallo daya zakayi mashi kasan cewa cikin gidan compound ne, sauke kayan malik yayi yana kallon aydarh da yanzu fuskarta babu hawaye amma kallon daya zakayi mata kasan she is sick domin babu walwalla sam a fuskarta duk tazama kamar wata marainiya, ahankali yace mata sauko. Da sallama suka shiga cikin gidan apartments biyar ne a gidan ko wane akwai dan space tsakanin shi da dayan, da kallo waenda ke zaune tsakar gidan suka bisu suna kafe su da ido Kamar mayu,gaishe su malik yayi dasauri suka amsa ita dai aydarh kanta nakasa ko iskan da ya kwaso su bata kalla bad uk kanta nakasa hakan bai hana matan dake tsakar gidan kare ma hallita kallo ba tunda malik yashigo wata budurwa take tsaye kallon shi take kamar tsohuwar mayya, har kofar dakin yayi dropping kayan dake hannun shi yafido ke.