← Book details Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 197

Sashe 23

Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

nan perfumes dinta irin masu kama fatar jiki ne saboda ko da bata shafa ba kamshin na nan makalle da ita Amma sai take jin kanta wani irin tunuwa datayi bata dashi yanzu, kallon kwalban take ko dauke ido babu body splash aka rubuta jiki tasan perfume ne ,kamshin sa kadan hakan yasa tafesa kadan komawa tayi can karshan katifar ta koma ta cure kanta waje daya ta rufe da duvet, tunani kala kala a ranta, Sai da yagama sallar la’asar kafin ya tashi ya koma dakin, ledan maganin ta yabude yafido su hankali yace “tashi ki sha magani,shiru tayi kamar bata ji shi ba, bai sake maimaitawa ba sai ruwa daya fito ya dauko mata a kitchen, yace take “sai sannan ta tashi ahankali tana rike duvet din ala dole kar ya ganta da towel da hijab yarda take shan magani kadai zai nuna maka irin rashin kaunar dake tsakaninta da magani, saida tasha kowane kafin ya kwashe ya mayar a leda, kallonta yake can yace wear up your cloth akwai sanyin, kamar zatayi kuka ta saukar da kanta kasa tace babu “sai kuma tayi shiru shi fa har mamaki take basa komai na kuka ne wai “bai fahimce abunda take fada ba hakan yasa shi cewa babu mi? Tace kayan, bai sake ce mata komai ba itama bata sake magana ba, sai bude bag dinta dayayi ya fiddo dayan rigan atamphar da ummi ta bata da kallabi , abayar da take nan wajan katifar da veil din daukar abayar yayi dawani irin speed ta sa hannu ta dauke brassiere dake nan kasan rigan ,ta boye yaga abunda tayi tsaf Ko kallonta baiyi ba yashiga bathroom din dakin sai da yabi manyan pants din ta da kallo yayi saurin dauke kai pampo yabude ya tari ruwa a bucket ya yazuba detergent kadan yasaka sabulu yafara wanke mata kayan, saidai ya wanke su tass ko kadan babu dirty a kayan sai kamshinta daya adabe masa rayuwa kamar time din tafesa perfume din .fitowa yayi rike da bucket din daya dauraye kayan a hannu, Ko kallonshi batayi ba ta dauke kai shima bai ce mata komai ba yayi ficewar sa. Ramlah na tsaye a ventilation dinsu wanda yake opposite da part din su malik din wayarta a saman building din daya zagaye part din normal android ce ta yayi,wanda cikin samarinta irinta ya siya mata,tiktok take tana wani karya jiki kamar wata macijiya, ganin yafito tayi maza ta bi bayansa “cikin kissa tace barka da yammaci yallabai ina wuni “iya saman lips ya amsata yayi gaba idan Doctor ibrahim ya nuna masa ta bayan parts dinsu dake zagaye anan ke da igiya daure ya shanya mata kayan ko wane part haka yake da igiyarsu. Warming miyar yayi ya rufe, wayarsa tayi ringing yana dubawa yaga dr ibrahim ne ,gaisawa sukayi yace hala madam dince tahana ka fitowa dariya malik yayi yace karka jawa yarinya sharri babu ruwanta gajiya ne kawai ke damuna dr ibrahim yayi kasa da yace kaidai kasa hakuri zakayi ta warke shiyasa kake ta dakon ta, murmushi malik yayi yace idan ma hakan ne ai ba laifi bane, dr ibrahim yace kwarai dagaske amma dai a dinga jin tsoron Allah ana tausayi, malik bai ce Komai ba sai cewa yayi kaji dashi dai, dr ibrahim yace tau na biyo maka zakaje kallon ball din ko kuwa? Malik yayi shiru sai can kuma yace aaa gaskia sai mai jikin ta karasa warwarewa zuwa next week sai na dinga bin gwaraye yawon dare, dr ibrahim daga can ya rike baki yace naji magana saukin ma dai nima bai fi two months ba,dariya malik yayi sukayi sallama.ko daya dawo daga salar isha backyard din ya zagaya domin kwaso shanyar yasan zuwa yanzu sun bushe ga kuma alamar tasowar hadari domin har walkiya akeyi tun dasuka zo gidan akwai nepa ko sau daya bata kifta ba daman dr ibrahim yagaya masa anguwar bakasa fai ake dauke nepa ba, Ahankali ta sake curtain din window this Time bai dauke idonshi ba akanta maganar dr ibrahim yadawo masa a rai dayace masa wai suna kama da ita kallonta yakeyi sosai shidai baiga kaman ba maybe ko dan itama tana da manyan ido ne oho ganin kallon dayake mata duk sai taji bata sake ba towel din daure yake a kirjinta sai hijabin da ta dauko waccan doguwar har kasa gani take kamar yasan babu bra a jikinta, kayan hannunsa yabuda wardrobe din yasaka mata tareda jikkar ta baki daya , har yakai kofa ya juyo yace mata ki saka rigan bara na kawo maki abinci, harara taraka bayansa dashi ahankali taja karamin tsaki tace who’s he? Sai wani jin kansa yake. Sharp sharp tabude wardrobe din ta dauko abayar daya wanke mata tass tasaka ta maida hijab din, saida ya dan bata lokaci kafin yadawo dakin saboda yabata daman shiryawa “ko daya shigo zaune ya iske ta saman katifa ta jinginar da Bayanta a pillow bai ce mata komai ba ya aje abinci ya juya ya fita “ bin plate din ta dinga yi da kallo same abincin daya kawo mata da rana ne ya sake kawo mata yanzu, ahankali ta dauki plate din tafara cin abincin kaman tana taunar magani bata ci wani dayawa ba ta ture ta sha ruwa, bacci ne sosai a idonta baccin da ta mance when last tayi sa “ Ahankali ta zame ta kwanta tana rufe idonta. Har sai da gari yayi haske kafin yashigo daga sallar asuba, babu motsin kowa a gidan” bude kofar yayi ya shiga, har yanzu akwai wuta tun jiyan basu dauke ba “har yakai hannu zai bude kofar bedroom din ta sai kuma yafasa ya koma nan parlor inda yasa bargo ya kwanta sai da gari yayi haske sosai kafin ya tashi “toilet din nan parlor ya shiga duk irin sanyi dake akwai na damuna bai dame sa ba ahaka yayi wanka da ruwan sanyi yafito kayan jikinsa ya maida kafin ya bude kofar bedroom din without making any sound har ya bude wardrobe inda yasa jikkar shi ya fido black jeans ne da T shirt itama black yafido Vaseline da perfume din sa ya dauko sai comb fita yayi ya koma parlor tsaf ya shirya yayi matukar kyau, “ kitchen ya shiga ya kunna gas ya daura mata ruwan zafi, tunanin abunda zasuyi break dashi yake hakan yasa shi yanke shawaran fita shagon daya gani ya siyo musu indomie.indomie yasiyo manya kwara uku da yellow label sai sugar,masu cefanan daya gani ya tsaya wajan su yasiyo vegetables da pepper sai kifi wanda aka gasa, zuwa yanzu mutane duk sun fito masu hadahadar tafiya office,nayi masu tafiya kasuwa da masana’antu nayi tun zuwan shi garin ya fahimce kowa anan din ta kansa yakeyi,daidai kofar shiga gidan ya hadu da daya daga cikin yan gidan namiji tun zuwansa gidan bai ga namiji ko daya ba sai yanzu “mutunmin ya washe baki ya tsaya yana kallon malik,hannu malik ya basa suka gaisa “mutunmin yace Allah sarki malan ashe kai ne wanda kuka tare inda dakta ya tashi,malik yace eh nine,mutunmin yace tau ni sunana malan sabo nima anan nake zaune da iyalina mata ta daya sai yaranmu biyu duk kananane,Kamar yarda kagani gidaje hudu ne anan din kowa da matarsa yake zaune dayan ba mazauni bane matar shi daya da yarinyarsu daya Ramlah mutunmin kirki ne kwarai dagaske saidai kash “wllh bai yi saar mata ba da diya abar dai kaza cikin gashinta, dayan kuma sabon aure ne Auwalu ko wata ba a cika ba shagon siyar da kayan shafe shafe garesa na mata a kwari, malik dai surutun malan sabo ya ishe sa,murmushi yayi yace Allah sarki daga haka malik yayi masa sallama ya wuce ciki.karshe ya kai wutan gas din hakan yasa akayi daidai toni sanda yashigo ruwan na tafasa yau ma kamar jiya a bucket ya juye mata ya kai mata bathroom din already towel din daya fiddo mata yana nan rataye a kofar toilet din Sai da yasa detergents ya wanke toilet din kal duk da babu dirty ko kadan a toilet din “duk motsin da yake tana jinsa amma ko da wasa bata motsa ba har yagama yafita, kusan 5 minutes kafin ta tashi ta sawa kofar dakin key ta cire kayanta ta daura towel din tashiga bayin kusan 20mins ta bata kafin ta fito toilet din ba karamin kyau raman datayi yayi mata ba, Zama tayi gefen katifar sanyi take ji kadan kadan stain kadan tagani jikin pad dinta a pant din ma babu” shiryawa tayi tasaka rigan atamphar daura kallabin tayi simple style tayi wani irin kyau,bata saka brassiere ba amma zaka iya rantsewa da Allah akwai bra a jikinta saboda yarda breastcuff din ya zauna mata dass a jikinta, toilet din ta koma ta wanke bra din ta data shanya tass tayi hanging dinta a inda tayi hanging pants dinta, sun bushe hakan yasa ta kwaso su ta bude wardrobe din ta saka a ciki kallon bag dinsa dayasa a dayan gidan wardrobe din tayi ta dauke kai tana sakin karamin tsaki, Alhamdulilah yau tanajin saukin jikinta sosai babu abunda ke mata ciwo kawai dai har yanzu abun na mata yawo a kai yana kuma yi mata ciwo a zuciya, komawa tayi ta zauna kan katifar ta zubawa waje daya ido, duk wani abu nata mai muhimmanci shikenan fa yanzu?tambayar data samu kanta dayi ma kanta kenan sai ga kwala ya cika mata ido tayi maza ta goge kamar mai tsoron wani ya ganta tana kuka. Yarda yayi shaping vegetables din kamar wata mace ba karamin mamaki zai baka ba cikin nutsuwa yake girkin Kamar yadda wata hadadiyar chef din zatayi saidai indomie ta kusa yi kafin ya zare kayar kifin tass ya zuba, kamshin ne ya cika gidan ko ina 15 minutes ya dauke sa dafa indomie da ruwan Lipton a plate ya zuba mata daidai daidai ba dayawa ba,saboda yasan ko yazuba da yawa din asaran shi zaayi ba ci zatayi ba shima ruwan Lipton din half cup yazuba mata ya saka sugar kadan kafin ya dauka yashiga dakin da sallama,baiji ta amsa masa ba,kuma bazai iya cewa bata amsa din ba shidai yashiga kawai ajiye kayan hannunsa yayi bai ce mata komai ba itama
Chapter 23 · 0% Book details