Sashe 157
Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
goshi babu wani wuri daya ji ciwo shiyasa har yanzu suna cikin dubasa x ray akaje ayi masa saboda kaman yaji ciwo a hannu dakuma baya sai numfashin sa dake tafiya yana fizga shiyasa aka masa fixing oxygen har yanzu bai san abunda akeyi akansa ba mutumin nan mai trailer tunda su abba suka karaso Wallahi gani yake kaman yagama yawo yabanke yaron masu kudi har haka shikam bai san iyakar hukuncin dazaa masa ba kila ma suce daga nan ayi prison dashi ganin babu sark isai Allah yadinga istigifari yasamu yafice daga asibitin dasauri car key din malik ya ajiye motar yayi damage buh yana tashi dashi ma suka zo asibitin “ can sai ga wata nurse tafito rasa ma wanda yafara tashi cikinsu za kayi wani irin zabura suka kaman zasu cinye ta ganin hakan yasa tayi dan murmushi tana girgiza kaii abby yayi karfin halin cewa lafiya take ita da abunda ke cikinta ba? Wallahi ummi ji tayi har zuciyarta zata fito saboda rashin sanin abunda zaa ce yafaru da cikin nurse din tace where is her husband dr usama yamike yadaka mata wani tsawa yace what the hell are you doing “what’s your business with her husband? Can’t you talk ma’am ganin yanda yake magana with so much anger idonsa kaman zaiyi aman wuta yazare medicated glasses dinshi ahankali rufaidarh tasa hannu tarike hannunsa tana girgiza mashi kai shiru yayi kawai dazzy shima da nurse din tabashi haushi yayi magana sounding so pissed up yace kinga malama kimana magana ki fada manah ya jikinta wani mijin bayan waccan dake kwance yayi hadari duk waenda ke nan bazaki fada ma halin da take ciki bas ai mijinta kinsan abunda kike kam do you know your job anya “dr hafsa tace kiji malama idan baza ki fadamana ba zan shiga what nonsense is this familyn patient nason sanin halin datake ciki kina mana zancan miji bayan gashi a kwance ba lafiya “Wallahi duk maganar nan babu abun fada amma dayake kowa ranshi babu dadi shine zaa sauke kan nurse din ta fahimce su tayi musu uzuri hajajju tayi mitsi mitsi da ido tace ko dai bata da isasassar lahiya ne wannan kiyi manah kin kama baki kin rufe daman su nas din nan babu abunda suka sani ran oum yasake bace kasa magana kawai tayi don bakin haushi ya isheta ma billahi “ nurse din tagyara tsayuwanta tace kuyi hakuri dan Allah ku kwantar da hankalinku in sha Allah he will fine and itama Alhamdulilah cikin bai fita ba yananan kawai ta tsorata ne and mahaifanta bashi da kwari so bed rest muka bata saboda ko yaushe wani abu zai iya faru marar dadi wanda baa fata yanzu mu maida ta postnatal ward anjima kadan zata koma amenity jikinta Alhamdulilah kaman a tare oum da ummi suka sauke wani irin ajiyan zuciya har kana iya ji rufaidarh ma Zama tayi tana fadin Alhamdulilah abby ya jinjina kai yayi ma nurse din godiya kafin shima yazauna din har yanzu tsugunne bata kare musu ba har sai sunji halin da malik din yake kasa hakuri dr usama yayi yajuya yana nufar hanyar x ray room din dasuka nufa da malik abba yaga yanayin sa kawai yasa shi jawo hannunsa yace am sorry Doctor ka kwantar da hankali idan ma abun yafi karfin su zasu fada kuma nan there’re good in sha Allah zasuyi komai abby yace in sha Allah ummi tace tau ni yanzu dan Allah arakani wajan babyn baba tace kiyi hakuri ta huta din kaman yanda nurse din tafada ummi ta girgiza kai tace dan Allah baba kuyi hakuri ba wai gardama zanyi daku ba amma dan Allah ataimaka abarni naje na dubata “ baba ta gyada kai dr hafsa takama hannu ummi suka tafi bakin kofan wajan ga cleaner dake tsaye wajan tana hana shiga wai ba time din shiga bane ana medication ga wasu bayin Allah tsaye anyi ma yar uwarsu cs tahana su shiga su ganta kuma ta farka sai wulakanci take musu “daga dr hafsa har ummi babu wanda ya bi takanta ba dr hafsa tawani hade rai tabude kofan gently suka shige itama cleaner ko yunkurin hana su batayi ba domin taga bama wurin da zata attitude din nasu na cleaners bane “ domin wata fuskar tafi gaban mari (Allah kayi manah arziki 🙏🏼) suna shiga tana can building din karshe dassuri ummi takarasa wajan da aydarh take an yafa mata zanin asibiti ga karin ruwa ana mata ta dan yamutse fuska bacci kawai take ummi ta zauna gefen gadon ahankali takama hannu aydarh wanda babu cannula kallonta take ko kiftawa babu cike da tausai a cikin malik ma ta taba haka bakaramin wahala tasha ba ahankali ummi tarufe ido tace ubangiji Allah yaba mijinki lafiya yabaki lafiya yarabaki da abunda kika dauka lafiya Allah yayi muku albarka tasa hannu tashare hawayenta dr hafsa tace Ameen kafin itama kwalla cike a idonta tace dan Allah ummi kukan ya isa haka kuyi hakuri in sha Allah duk zasuji sauki ummi ta gyada kai shiru sukayi daga ita har dr hafsa din fuskan su cike da jimami ga sauran patients duk a kwance wasu ga babies nan a gefensu waenda suka haihu akayi ma cs kenan .sai da suka hada result din duk wasu tests da aka ma malik din kafin sukayi ma su abby bayani “Wallahi tunda abun yafaru basu dan samu peace of mind basai yanzu da aka fada musu halin dayake ciki dr usama ya gyara tsayuwar sa kafin yace bayan frakcer da injury daya samu a kai babu wani abu bayan nan?dr din yace yes sir sai kuma chest hit daya samu wanda Alhamdulilah shi babu wani matsala right now ma he is breathing normal “ dr usama ya gyada kai kafin yakalli dr faisal da dr ibrahim yace well done sons “abby yace tau Alhamdulilah duk sai kowa hankalinsa ya nutsu tunda ba wani babban abu bane yafaru dashi din abba yace aaaa yayah ciwo dai ciwo ne saidai fatan Allah yabashi lafiya oum ta jinjina kai sai yanzu ta dawo hayacinta dr usama yamaida glasses dinsa yana kallon dr ibrahim yace can we cheaks on him Doctor?dr ibrahim ya jinjina kai yace sure sir dr usama yakalli abby yace muje amma dan Allah ku hakura da kukan nan haka nan zamu shiga wurinsa baya son hayaniya kuyi hakuri dan Allah baki daya suka shiga amenity room ne sun cika sa faa su dr umar dasu nurse yasir ma a waje suka tsaya saboda babu wurin daza su tsaya a dakin addua sukayi masa abby yace duk su fita fita sukayi banda abba dakuma dr usama su suna nan aka barsu tare dashi abby yaduba agogon hannunsa ganin karfe 12 saura yace yakamata suje gida sai abar wanda zai kwana wurinshi da kuma wurin aydarh “dr faisal da dr ibrahim aka bari babu yanda rufaidarh batayi ba ummi ta tafi gida zasu zauna ita da dr hafsa wurin aydarh cewa tayi aaaa bazaayi rashin hankalin nan ba amarya ce ita abby yace kwarai dagaske da ummi da dr hafsa aka bari sauran suka tafi maryam har yanzu taki daina hawaye “ dazzy ne da dr umar suka dawo suka kawo yan asibitin duk wani abunda zaa bukata kafin su koma “su ummi na zaune sun kasa sun tsare ita da dr hafsa tsakanin dakin da malik yake kwance da inda aydarh take ummi tayi zarya yakai sau goma bayan tafiyar su abba takasa zama duk yanda dr ibrahim yace ta hakura ta zauna amma inaaaaa bata jiba kuma daga aydarh har malik din babu wanda ya farka “wajan karfe daya da rabi nadare aydarh tafara bude idonta ahankali ahankali kanta ciwo yake ga idon sun mata nauyi celling din dakin tabi dakallo kafin ahankali tarufe idonta tana recalling yanayin dataga malik kafin tayi fainting wani kalan zabura tayi oh my goodness ‘ta tashi zaune dasauri ummi tarungume ta aydarh tafashe dawani irin kuka wanda dole kabata tausayi kira take ummi where is he?ina sir yake you should answer me please miyafaru dashi miya samesa inalilahi waina illahil rajiun nabani nashiga uku ku taimaka kuce masa kar yayi ciwo he should pity me Wallahi ba wasa nake masa ba I love him dagaske am done nabani kwalla suka cika ma ummi ido tasa aydarh sosai a jikinta aydarh kam sai kuka take kaman ranta zaya fita gashi bata da karfi gawani irin zafi datake ji a maranta “ummi tafara patting bayanta tace ya isa haka baby ya isa kiyi hakuri baki da lafiya fa kidaina wannan kukan stop shaking yourself har haka baby baki da lafiya kina bukatar hutu aydarh tasake fashewa da kuka tace a fadamun miyasamesa dan Allah auntie dasauri dr hafsa takama hannun aydarh tace ki nutsu first idan baki nutsu ba babu wanda zai fada miki dasauri tabar jikin ummi tafizge cannula hannunta ummi tarufe ido ganin abunda aydarh tayi Wallahi ji tayi har cikin ranta ita kawai tasan halin datake ciki gawannan ciwon ga tashin hankali dasauri tasa hannu tana share hawayenta tace to na nutsu Wallahi nayi shiru nadai ki fadamun dr hafsat ace he has an accident but not that much serious yadan samu injury a kansa kawai yanzu haka ma bai jima da fita daga dakin nan ba yazo kina bacci tau shima yagaji hidiman nan gashi anyi masa allurar bacci ya kwanta “kema ki kwantar da hankalinki ki huta idan Allah yakaimu gobe sai kiduba sa nama san shi zai fara zuwa duba ki in sha Allah aydarh tasake fashewa da kuka tace why not now auntie dan Allah nidai a kaini na duba shi he is all what I have shima nasan he wanted to see me Ina so nafada masa kar yasake ciwo bana so ‘ dr hafsa tace yanzu fa nafada miki yace ki huta shima zaiyi bacci dasafe kwa hadu sai yafi ma tunda yanzu anyi masa allura idan kuma bakya son yayi baccin ya warke shknn aie ki tashi muje ta girgiza kai tana goge hawayenta tace no nahakura auntie kar yace banji maganar sa ba ai dasafen zai shigo koh?dr hafsa ta gyada kai tace yes in sha Allah baki daya aydarh tamanta da ummi dake