← Book details Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 197

Sashe 29

Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ai,aydarh tayi murmushi kadan tace ina wuni?sannu,dr hafsa ta amsa mata,anan parlor suka zauna babu wanda yakara magana cikin su,so take ta tuno abunda malik keyi idan anyi guest,kitchen tashiga ta dinga bin koi na da kallo pure water tagani asaka biyu ta dauka ta daura a plate takawo wa dr hafsa din kafin ta koma ta bude warmer da ta gani a kitchen din abinci daya dafa ne da rana white din ta zuba a plate tasaka mata stew kadan sai salad takawo wa dr hafsa,dr hafsa na murmushi tace lah ai da baki kawo abinci ba yanzu naci abinci kafin na fito kuma ma sauri nake,aydarh tace aa fa sai kici ko kadan ne “kanta akasa tana wasa da zuben hannunta kadan kadan dr hafsa ke mata fira murmushi kawai ne nata dan bata cewa komai itama dr hafsa din bawai tafiye surutu ba, ba laifi taci abincin tasha ruwa,ta kalli aydarh tace mai gidan baya nan ne?tsaf aydarh tagane wanda take nufi hakan yasata cewa erh”dr hafsa tace kinga sauri nake jiya ne yakai wa inna wannan atamphar yace tabani na kai maki dinki, so bansan measuring din ba,aydarh tayi shiru kafin can tace kawai ayi tunda ban san style din ba,dr hafsa tace aaa ga styles nan kala kala sai wanda kika zaba, murmushi tayi tace aa ayi kawai,dr hafsa tace no kafin tayi unlocking wayanta tashiga photos screenshots din styles din dinki ta nuna mata wanda tayi a ig, ita dai aydarh sai bin dinkuna da kallo take, bata wanda zata ce yayi mata ba amma hakan nan ta zabi wani free straight yayi kyau sosai, dr hafsa tace kuma zai maki kyau sosai masha Allah, miye measuring din nan aydarh tagaya mata domin komai nata tasani kuma bata mantawa,har kofar part din ta rako dr hafsa din tayi mata godiya ta wuce, tana dawowa ta kwashe plates din ta kai kitchen ta jawo takalman sa slippers dake nan bakin kofar toilet din ta bi da kallo ta dauke ido tana tsakin siririn tsaki iya lips dinta, hakanan taji tana son zama parlor sosai taji dadin zuwan dr hafsa ashe mutun rahama ne,duk sai taji bata ji wani damuwa Sosai, yau din nan, nan kan carpet ta zauna ta kura wa wuri daya ido,kara knocking kofar akai tanaji har sai da akayi sau uku kafin ta mike taje ta bude, Ramlah ce tsaye sai wani taunar chewing gum take kamshin karamin perfume dinta kalar na yan bori duk ya cika ma aydarh hanci babu alamar wasa ko wani murmushi a fuskanta ta koma real aydarh ta na can baya take kallon Ramlah da kusa shidewa wajan kallonta batayi tunani takai haka ba domin bata taba yi mata kallon gab da gab ba, maganar da aydarh tayi yasata dawowa cikin hayacinta,tace lapia? Ramlah ta aro jarumta domin kwarjinin aydarh yasata firgita daidai nutsuwan ta tayi kafin tace lafiyan kenan yayah malik nake nema idan yana kije ki ce masa gani nan nazo,kallonta tayi sama da kasa kamar taga wani abun kyama. Ganin irin kallon datake binta shi yasa Ramlah gyara tsayuwar ta, Aydarh bata ce komai ba tajuya ta koma ciki tayi banging door din a fuskar Ramlah,wani irin mugun ashar Ramlah tayi “ kamar zatayi hauka a inda take tsaye ita tayi ma wannan rashin mutuncin tau wallahi bazata yarda ba.fadila tayi shiru tace umm ni wallahi baki birgeni ba da baki tatakata a wajan ba tau wacece ita haka?maman Ramlah datayi shiru tace nidai ku bi komai ahankali kar fa ace mutanan batar da sahu sukayi ,kuyi masu rashin mutunci ayaye ku a daure wallahi,fadila tayi kasa da murya tace wallahi fa maman Ramlah ni har tsoro suke bani daka gansu fa kaga kudi da mulki kar fa dai yaran sarkin makka ne?ramlah tayi wani uban tsaki tana hararar fadila da maman tasu baki daya tace ku fa matsalana da ku har yanzu kanku a duhu yake kauyawa ne ku wallahi bacin haka miye wani abu danganta su da wani sarkin makka miye ma tau zai kawo su nan in har hakane?kawai da wallahi abunda tayi mun sai narama shine kawai,duk shiru sukayi babu wanda ya tanka ta cikin su. Ko data koma daki tunanin ramlah ta yakasa barin ranta,tau wacece wannan kazamiyar da zata zo neman sa kuma,sai kuma taja dogon tsaki tace miye ruwanki dashi, nan take abunda yafaru da inna tazo yadawo mata a rai tayi tsaki yafi a irga,kwanciya tayi tana ta juye juye idonta ya sauka kan wani karamin littafi na azkar na shi ya manta shi a carpet din dakin jiya,ahankali ta mike ta dauka budawa tayi tana dubawa sosai ta maida hankalinta wajan duba littafin bai fi addua biyar tasani a ciki ba tunuwa tayi da yarda yake raira karatun al quraani dazu ,wannan ne karon farko a rayuwanta dataji tana so sanin wani abu game da addini bayan wanda tasani wannan ne first time datayi hawayen kin tsayawa tasan abubuwa game da addini babu yarda oum batayi ba rufaidarh ma haka amma tasamu daurin kugu wajan abba nakin tsayawa ta koya din,abubuwa dayawa gasu rubuce a littafin amma bata iya karantawa da hausa sai kuma larabci akayi rubutun,ta iya ranta hausa tsaf amma batasan ma’anan adduo’in ba.Ba karamin gajiya yayi ba a yau din nan aiki ne wanda bai saba dashi ba duk da yanda ya taso amma kwata kwata jikinsa ba mai son wahala bane,aiki ne wanda bai taba yin irinsa ba shiyasa ya sha wahala duk da matsayin shi na babba a wurin yanada hutawa amma dai yayi wahala sosai,jikinshi duk yabaci da cement haka kayanshi duk sunyi kura kadan bayan sun tashi aikin kowa ake basa 2500 cash a hannu,duk da kudin babu yawa he appreciate tunda dole ya bukaci kudi ko dan saboda aydarh ko dan saboda yanayin rashin lafiyan ta,yana shiga kitchen kawai yawuce ya daura ruwa a gas yasan batayi wanka rana ba tunda bai nan balle ya dafa mata ruwan wanka,sai da ya daura kafin yashiga toilet dinshi nan parlor yayi wanka tass kayan jikin shi ya mayar yashiga dakin da sallama kallonta yake ko kiftawa babu har yanzu littafin ke hannunta tana karantawa duk da ba fahimta take ba,abunda yakawo shi dakin yayi ya fita, sai dayashirya ya jika kayan da ya cire a bucket kafin ya duba ruwan,bucket din toilet din ta ya dauko yajuye mata yafita,Sosai ya ci abinci kafin ya koma toilet ya wanke kayan shi tass ya fita ya shanya dan kwanciya yayi kadan kafin a kira sallarh magrib.Awara yasiya masu yashiga gida domin ba karamin gajiya yayi yau din nan ba kuma kwana biyu ma sai ahankali yake jin shi kamar zaiyi fever, AFTER A WEEK Alhamdulilah malik yanzu har ma yasaba da aikin ginin dasuke ga ta gefe guda wani irin kirki Allh musa yake masa kamar irin ya jima da sanin shin nan yana matukar jin dadin aiki dashi Sosai.kallon shi yake ko kiftawa babu har yayi shiru kafin malik yace har fa kwana biyu kace dr ibrahim ya gyara zaman sa a kujeran clinic yace eh kwana biyu zamuyi can nasarawan tunda kai ne babban aboki kaga dole mutafi tare,malik yayi shiru can yace tau Allah yakaimu “dr ibrahim yace Ameen kafin yace ya aikin?malik yace aiki Alhamdulilah,dr Ibrahim ya saukan da ajiyar zuciya yace take heart malik in sha Allah zamu samu wanda yafi wannan nasan baka saba ba nasan daurewa kawai ka ke kayi hakuri in sha Allah zaa samu wanda yafi wannan ,malik yayi murmushi yashafa kanshi yace kaga tashi muje gidan inna zan karbawa ASSEIYARH dinki gun dr hafsa dr Ibrahim yace tau badamuwa muje nima kwana biyun bamu gaisa da innan ba.inna ta kalli dr Ibrahim tace daga ina kai kuma? Lahiya dai ko?ko rashin tsoron Allah yasa wata katuwa taje tace maka banda lahiya aaa wallahi lahiya ta lau tambaye audu gashi nan shi ai yasan gaskia,dr Ibrahim dayake kallonta yasaba da halin ta basa shiri sam kullun idan yazo sai sunyi fada “yace tau ke dakika ga nashigo daga gaisuwa kinga nace maki wani abu ne?inna dai tayi banza ta kyale shi ta tashi ta shiga cikin daki , hadaddan kwadon zogale day asha kuli da kayan hade ta fido cikin kula, tace tun dazu nayi maka audu tau da nayi tunanin baza ka zo ba ,har ina cewa yamma tayi na kai ma matar ta aje maka, malik ya karbi kular yace tau shknn inna nagode shidai dr Ibrahim bai ce komai bas ai danna wayarsa yake, dr hafsa ta fito hannunta rike da dinki aydarh gaisawa sukayi cikin mutunci “ tana tsokanar shi ango ango dr Ibrahim yayi murmushi yace fadi ki kara,inna tawani tsuke fuska ta kalli malik kafin tayi kasa da murya tace kaji wani jafa’I bikin da saura kusan kwana sha biyu miye abun wani fara kiran mutun da ango banda neman magana,Allah dai ya kyauta shi dai malik bai ce komai ba yanata kallon inna, dr Ibrahim ya mike tsaye yace ma malik ka tashi mu tafi ni akwai inda zani,inna tasaki baki tayi shiru tana kallon dr Ibrahim tace aaa kai kau ibrahin kazama abun tsoro yanzu kai ina ruwanka da shi wuri daya kuke kwana ko kuma wani neman maganar ne,dr Ibrahim tace ni fa bana son kina yawan saman baki idan ina magana kema ina ruwanki fisabillahi? Malik yayi murmushi yace yanzu duk hakura inna na bara nakai ma jikarki sakon zan dawo in sha Allah,dr hafsa dai tayi shiru batace komai ba. Tsaf ya gyara gidan koi na fess babu abunda ke bukatan gyara, ranar tafara sa dinki Sosai take kallon kanta a mirror din window bedroom din tayi wani irin kyau mai fuzga bakaramin tuno mata da ummi atamphar take ba murmushi tayi ahankali kafin ta dauke body splash din ta fesa kanta tasamu tayi parking sumar can kasan kan babu saloon amma yayi matukar masifan kyau kallabin ta daura all back kafin ta dauki well iron hijab din sabowan wanda bata cika sawa ba tasaka malik ne ya goge hijab din da iron din da ya siyan masu,a parlor ta iske sa yashirya yana jiranta babu wanda yayi ma wani magana dr hafsa ce tace mata tazo tayi mata calaba daman
Chapter 29 · 0% Book details