← Book details Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 197

Sashe 39

Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sallama can kasan throat dinsa daidai itama ta fito daga toilet din tana gyara daurin towel dinta, bata lura dashi ba har takara so cikin dakin, sai sannan tagansa ta firgita ta juya babu abunda zatasa ko ta rufe jikinta sai kawai tashige jikin bango tana saukar da kanta kaf size din bra din dasuka siyo yayi mata kadan kusan half din boobs dinta a waje yake yarda tayi daurin towel din har kana iya hangowa,yi yayi kamar bai san abunda take nufi ba kamar bai san da shigan datake ba kallonta yayi kafin ya janye ido kuma ya lumshe su,kamar zatayi kuka kuma a tsoraci tace to ka dauke warmer ka fita manah ni banda kaya fa,yarda tayi maganar yasa shi hade fuska yadinga tahowa towards her har yakawo inda take jikin bangon, kallonsa take a rude ganin yana nufuta har yayi mata rumfa da fadaddan kirjinsa ta rufe idonta kam jikin ko’ ina rawa yake cikin wannan muryan tasa ba wasa yace bazan dauka na fita ba sai kin gaya mun wanda kika raina,kike harara kike gaya ma bakar maganar,girgiza kai tace wallahi Allah ban raina ka ba ni bana hara..ra.nka tafada tana ina ina malik yace idan kinga na fita sai kingaya mun wanda daya mike magana sai kin mayar masa da baka, gabanta faduwa kawai yake hankalinta yayi masifan tashi tace ni dai bakai bane ka yiakuri dan Allah wallahi ba da kai nake ba ka yiakuri malik yace idan kinga na hakura fa sai idan kin gaya mun dawanda kike yafada yana bin da kallo wani irin extraordinarily kyau take dashi yarda baby pink din towel din yabi fatan jikinta haka ma bra din baby pink ce ga towel din dake nan daure ba sosai ba,so yake ta kiyayyesa ta dinga jin tsoron sa ko abubuwan sun zo masa dasauki hakan yasa shi gently ya kai hannunsa kan towel din wllh jin hannunsa a towel din har wani fizga numfashin ta yayi suddenly taji kasancewar idonta a rufe yake shikansa sai dayaji wani kala amma ya daure dai har yana iya jin yarda gabanta ke wani irin faduwa bakaramin tsorata tayi ba, hannunta dake wani irin rawa kamar yarda jikinta keyi tasa tana kokarin cire hannunsa daga wajan tunda ga brain dinsa har tafin kafar sa yaji wani irin abu ya tsarga masa jin hannunsu ya hadu wuri guda wani irin ajiyar zuciya yasauke ahankali yafara ja da baya sai kuma yayi Saurin fita yabar dakin ,takai kusan 3mins bayan fitan sa bata motsa daga jikin bangon dake ba yarda kirjinta ke over racing kai kaje wasan gudu tayi ahankali ta zame nan kasa ta zauna ta fashe dawani irin kuka har shedewa take takama jikinta ta kankame waje daya kamar irin yayi mata wani abu, har sai dataji numfashin ta nafita da karfi kafin ta saurara daga kukan datake. Anan kofan gidan yazauna ,yazuba ma waje daya ido babu abunda yakeyi irin tunanin rayuwarsa yanzu haka shi mijin aure ne nauyin ci,sha surutu da kuma tarbiyyar yarinyar na hannunshi,duk ya dauke wannan kuma ai yana yi bakin karfi da ikonsa tunda duk saboda da ita yake duk wani abunda yakeyi, da kuma amanar ta da ummi tabasa ,tunani ne kala kala a ransa tau yanzu idan yasake kamar yarda zuciyar sa ke raya masa fa?idan yabari soyayyar yarinyar da tausayinta yakarasa shiga zuciyarsa da ruhinsa fa? Yasan kiyayyyar da mahaifinta ke ma abby, yasan yarda mahaifinta yake kar ya shimfida rayuwa da ita daga baya mahaifinta yazo ya raba su fa? Duk duniya bai taba jin wata a rai ba bayan ummi dasu aysha sai ita,saukar da ajiyar zuciya yayi ahankali yatashi ya shiga cikin gidan sai da yarufe kofan part din kafin yazauna parlor yana kallon kofan bedroom din ji yake kamar yashiga,amma yafasa. Kasancewan yayi daran bacci shiyasa ya makara sallan asuba ma a gida yayi ta Sai da ya gyara ko ina kafin ya dafa masu indomie sharp sharp yau ko ganinta baiyi ba ko daya shiga daukan kayansa tana toilet,bayan yafita already tayi wanka tashirya ta fito tun dazo take son tafita ta dauko tsintsiya amma bata son ta fita su hadu wani irin girma da kunyarsa take ji gani take babu wani sauran abu kuma daya rage yanzu yariga da ya gama da ita, guntun hawaye tashare kafin ta mike ahankali ta bude kofan dakin tana kallon cikin parlor ya share koi na babu kuma shimfidar shi hakan na nuni daya fita komawa tayi bedroom din ta fiddo warmer jiya takai kitchen tana shiga taga nan ma ya share tass sai warmer nan ajiye tabude taga indomie ce ciki. Ta dinga bin indomie da kallo kafin ta rufe warmer,Sai da ta gyara bedroom din tass yau hadda toilet ta wanke ,tana aiki yau duk jikinta babu dadi kaman wace batada lafiya,ahankali ta fito daga bedroom din tana tafiya kamar mai counting steps dinta kitchen din tashiga ta ajiye mopper da tsintsiyan kafin ta bude warmer ta dauki plate ta zuba kadan ta fita parlor,bata ci dayawa ba ta ajiye ,kitchen ta mayar da plate din tayi zaune nan parlor, knocking kofan akayi kamar bazata bude ba sai kuma ta tashi,tace waye? Shiru taji ba a amsa ba kuma ba’a sake knocking din ba hannu tasa tabude kofan ahankali, kallonta yake ko kiftawa babu ita dai kanta na kasa kafin kuma ta juya tashige bedroom,bedroom din yashiga zaune take kan katifa ta zuba ma waje daya ido yayi kasa da murya yace hala baki iya gaisuwa ba? Kaman bazata amsa ba sai kuma ta tuno da abunda yafaru jiya,ahankali bata kallonsa ta juyan da kai gefe kafin tace “ina kwana” bai amsa ba sai bin dakin da kallo da yakama yi,itadai kanta na kasa bata dago ta kallesa ba, can yamike tsaye yace yau bazaki yi sharan ba?ta ware ido ta kallesa tace nan din fa dana gyara ,duk dayaga yarda dakin yayi kyau amma kawai so yake ya tsokaneta, yace nan din ne kika gyara? Ta bata fuska tace nafa gyaraaaaaaaa yanda taja kalaman kamar yar baby yasa shi kallonta, yace tau said ai ki sake gyarawa nan dai babu alaman anyi shara gaskia dai,batace masa komai ba tayi shiru ta kawar da kanta “can ya mike har yakai kofa ya juyu yace,dakin yayi kyau “sai kuma yafita ta dinga bin kofan da kallo kafin tayi murmushi can kasa tace sai kace shima iyawan yayi, yana fito ya wuce wajan dayake yin cefane vegetables yasiyo masu sai nama, dr hafsa ya hango yakarasa in datake,sai sannan ta gansa tayi murmushi tace “ina kwana “yallabai? Malik yace Alhamdulilah ya aiki? Tace Alhamdulilah,kafin yace inna fa? Dr hafsa tayi kasa da murya tace bata da lafiya fa,malik yace subhanallah dr hafsa ta gyara tsayuwanta tace fever take nayi magana k ozan mata allura ta rufe ni da masifa yanzu haka tana can kwance malik yace dasauki ba? Tace ehhh gaskia dasauki kasan dai halin ciwon inna malik yayi murmushi yashafa kansa yace in sha Allah zamu zo shigo idan anjima ki gaishe ta dr hafsa tace in sha Allah. Tana parlor zaune yafito da knife sai karamin rubber da cabbage sai carrot a ciki gawani plate rike a hannunsa,kallon shi tayi sai kuma ta dauke ido bai kalle ta ba ya zauna yafara yanka vegetables din kamar wani hadaddan chef,tunda yafara yanka vegetables din take kallon yarda yake duk abunda takeyi yana lura da ita sai daya kankare carrot din tass kafin yace, “yanka “kamar daga sama taji maganar sa batace komai ba ta sa hannu ta karba yarda yakeyi haka ta dinga bi tana yankawa ahankali, kallonta yake har ya shagala bakaramin kyau tayi masa ba,yarda take hade gira tana yanka carrot din murmushi yayi kadan kafin yayi kasa da murya yace “kin gaji ne? Ta girgiza kai tace ah’ah zanyi, malik yace tau muje kitchen sai mu karasa girkin?ta gyada masa kai kafin tayi wani cute smile tace erh nima zaka koyamun? Malik daya sakankace yana kallonta kamar wani yaro ya gyada kai yace mu tafi ,kitchen suka shiga ya mika mata cubes yace bare wannan kin iya? Tayi kasa da murya kafin tace to ka bude daya sai nagani,kallonta yayi bai ce komai ba ya matso kusa da ita ta matsa kadan tadan bada space a tsakaninsu cube din star daya ya dauka yace look up,ta dago kanta yafara bare maggin kwara daya ya bari kafin yace karbi ki bare sai nagani, fine fingers dinta tasa ta dauki cube daya tafara barewa, yarda take juya hannunta tana barewan yake bi da kallo sosai kananun diamond rings dinta sunyi ma hannun kyau sosai, tana bare daya ta dago tayi wani hadaddan smile tace,”nayi” malik ma yayi murmushi yace Good job mamana jin sunan daya kirata yasata bin shi da kallo dauke idonsa yayi kafin yacigaba da frying kayan miyan tacigaba da bare maggin har tagama kafin murya can ciki tace “nagama”kallon maggin yayi ya kalleta kafin yayi saluting dinta tayi murmushi kadan har cikin ranta take jin dadin yarda taga tabare maggin sosai take son ta iya girki kusan duk abunda ya dauko zai zuba sai yafada mata ko ya nuna mata duk babu wani dogowan magana amma ahaka take koyon duk abunda ya nuna mata din cikin few minutes suk agama girkin dake ta faman kamshi kallonta yayi itama shi ta kalla sai kuma ta saukar da kanta kasa hannunsa ya zuba a aljihu kafin murya can kasa yace zamuje mu duba inna ,batace komai ba shima bai sake magana cikin warmer da dr hafsa ta ba ta wainan flour jiya yazuba abincin kafin ya juye sauran cikin warmer su jin ana kiran sallarh yasa shi cewa idan nadawo masallaci sai mu tafi,fita yayi a kitchen sharp sharp kasancewan Friday ce yayi wanka wani white shadda yasaka duk da ta kwana biyu amma bakaramin kyau tayi masa ba agogon daya siya black yasaka sai azurfan shi black itama wani ubansu black shade ya kafa a ido yah arrahamar rahimin ya rabbil alameen Malik yafi kyawu kyau yayi wani irin kwantacan musulmin kyau, sai lokacin tafito bayan tagama wanke abunda suka bata wajan girkin bata ko kalli inda yake tsaye ba a parlor yana linke prayer mat zai yafa
Chapter 39 · 0% Book details