← Book details Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 197

Sashe 8

Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

hirar abba da aydarh sunata sakawa oum albarka domin sunce oum mutunce hadda rabin mutun ma .Tagwayan numfashi oum tasauke jin yanda aydarh ta fizge motar ,tace uktiee kinji dai koh naji uktiee in sha Allah komai zai wuce da yardar Allah shirune yabiyo baya kowa da abunda yake juyawa a ranshi. A gaskiya mutane sun zama abun tsoro a wannan rayuwar tau idan ba abun tsoro bah ace tun shekaranjiya sai fama ake dakai kamar wani rubabbe kazo kazo amma kadauke ni wata abu can daban kasa tayi da murya tace ko dai baka da na napap shiyasa ahtau niba bakuwar tsanina bace sai kayi magana na ara maka dan gaskia bazan iya baka kyauta bah idan bahaka bah kai kamar wani abun arziki sai ka kadama kake zuwa waje shidai malik kallonta kawai yake sannan yace tau yanzu dana zo hala ke kika bani? Ina ce nagaya maki banda lapia gwalo tayi tace haram haramun karya haramun yaushe kace mun baka da lapia ni binta ka gayawa haka saidai koh yaya, baaba kulu da ke ta kallon ikon Allah tace hajajju wai miye haka yaron nan ko gaisuwarsa baki amsa ba amma kin hau shi da masifa kamar dai wanda yayi maki wani laifi sake kasa da murya hajajju tayi tace ma malik tashi kaga mu fita mu gaisa a waje kafin wasu su cigaba da samana baki a magana tunda mutane basu san su ja bakinsu suyi shiru ba idan bada su ake zance bah murmushi malik yayi yana kallon baaba ganin irin duban da take ma hajajju da ta mike tsaye fita sukayi ita da malik dayan dakin baaba suka zauna ta kawo masa shayi da irish tace ga naka muna iya wuni nan tsohuwar gidan bata damu da bamu abinci ba shidai bai ce komai ba yazauna yafara cin irish din can hajajju ta mike tace jirani ina zuwa,wai yaya Adar ta taho ne?gyada kai baaba tayi tace ehh uwar tace yanzu haka ma ta kusa zama hajajju tayi ta dinga dariya kamar sabon kamun hauka inda sabo baaba yasaba da halin hajajju batace mata komai ba har ta tsaya da dariyan tace yau akwai hada bamm a Nigeria wooo yau zasu ga fim ganin idonsu kowa sai ya girgiza da lamarin shekara 22 biyu ba wasa bah zumunci gaskia da tarihin gaskia zai fallaso Allah yakawo ta lapia Ameen baaba tace,har ta kai bakin kofa ta juyo tace tau shi dan karunar pah ya taho gyada kai baaba tayi da tunani kala kala aranta, wai audul kasan wasu a kano girgiza kai malik yayi yace aa gaskia ni sau daya ma nataba zuwa kuma naga shima gidanki idan baki manta bah Naga kuma gidanki ne naje ko? Ehhh hakane audul gidana ne kaje shiru tayi tana ta girgiza kafa can malik yace miyasa kika tambaya,kallonshi hajajju tayi sannan tayi kasa da murya tana kallon kofa tace aa babu komai gani nayi matar gidan na man wani gani gani kamar wata yar hau,murmushi malik yayi yace ke dai kika fadi haka kowa pah hakuri yake dake a cikinmu wani irin kallo hajajju tayi ma malik tace tau da nayi niyyar kawo ma komai cikin sauki amma saboda baka kaunar Allah filan dina kanka zaka sha mamaki!kallonta malik yake ko kiftawa babu yace plan kuma na mi?shiru tayi bata sake yi mashi magana ba shima malik din shiru yayi saboda yasan halin hajajju sometimes hakanan take magana babu kai babu kugu.Duk yanda taso ta daure ta gano direction din gidan baaba batare da magana yahada ta kowa na anguwar ba ta kasa irin gudun da take da motar tamkar zata ta shi sama yaran da manya na anguwar sai sauka suke a hanya domin ko da ganin zubin motar ko bigeka mamallakin motan yayi babu abunda zai faru,duk bayan seconds sai ta fitar da sautin tsaki cikin kwarewa da sanyi take tsakin ji take duniyar tayi mata duhu gabanta tsananta faduwa yake duk da ba komai tasani na illimin dunia bah zama a iya cewa cikin kashi dari na illimin zaman duniya tau aydarh kashi talatin tasani saura saba’in din bata sani ba kuma bata damu da tasani din bah(iyaye dan Allah duk yanda yakai da gata da son dakuke wa yaranku ai kokari ana daura su kan hanya ba kamar yaran mu mata basu san idan zasu riski kansu ba misali gidan miji d.s.s) takasa gane gidan hakan yasa ta nemi wuri tayi parking sauke glass din motar tayi tareda mai black shade dinta a ido tana kallon wani mutun dake tsaye kusa da wani gida cikin sanyi da izgili da isa tace tambaya nake waiwayo yayi yana dubanta sakin baki yayi yana kallonta mamaki yake yarda har ta iya hausa,sake motsa bakin ta tayi kamar taga abun kyama tace are you dumb?washe baki yayi yace hajia Allah yasa nasani bata ma san inda zata ce tana nema bah aka yasata yi mashi nuni da hannu batareda tayi magana ba,hajiya ai ko shaidan bai san nuni da hannu ba balle ni kallonshi tayi domin bata fahimce abunda yake fadi ba and yasan yarda take ji a zuciyan ta tsayawa datayi tana mashi magana ba karamin kokari tayi ba saboda yanda take jin har kanta na juyawa gani tayi idan zasu kwana anan wannan mutunan ba zai taba fahimta bay asa tace gidan baabarh shiru tayi kamar mai tunani can tace baabarh kulu sake gyara tsayuwa yayi yace Allahu akbar ai kin zo ma da baki tsaya kika bamu wahala ba daraat kinyi magana, kinga wannan gidan dake kallonki tau nan ne gidan hajiya baabarh bata tunanin zata iya masa godiya dan bata ma saba da hakan ba bata ga amfanin hakan ba domin a tunanin ta when you are rich you deserves anything in this life kudi ta kwaso wanda ita kanta bata san ko nawa bane ta wurga mashi ta window ta kwashe motar tayi gaba washe baki yayi ya tsugunna ya kwashe kudin tass aran shi yana cewa shashasha yoo ni Allah na tuba miye damuwa na idan ma a fuska kika watsa man indai kudi ne (Allah ya kyauta) daidai kofar gidan tayi parking bin gidan take da kallo kamar mai son gano maginin gidan relaxing tayi kan driver sit din da take maida numfashi take tareda laushe idonta takai 10mins ahaka kafin ta dauke hadaddan luxury mini bag dinta wacce zata kai almost 500 thousands (na ga wasu a ig suna nuna manah ita 😂🤭tau kunyi kokari dai dakuka siya)ahankali ta zira kafanta waje yah rabbi wani mad flat shoe ne a kafan sunyi matukar karban kafan sosai ahankali take tafiyan kaman mai counting steps har ta tura madaidaicin kofan wani irin yankewa gabanta yayi yafadi har sai da taji kanta na sarawa,Salati hajajju ke kwadawa ta gwalo ido tana karewa aydarh kallo kafin ta buda murya da karfi tana kiran baaba yaya yaya fito kingani dasauri baaba ta fito har tana tuntube da ghanan hajajju dake bakin kofar daki ,tana fitowa tayi ido hudu da aydarh murmushi tayi tareda karasawa gaban aydarh ta kamo hannunta tace Aseeyarh mi yahanaki karasowa ciki kallonta aydarh tayi tace babu komai ji take kamar zata fasa kara ji take kamar ta kwasa da gudu .hajajju dai na tsaye ta makale jikin bango tana kallon ikon Allah can taga baaba zata shiga tareda aydarh cikin daki dasauri tace yaaya mike damunki daga gani mata zaki shiga daki da ita minene haka baki tsayawa ma a tambaye a ji daga wace kasar aka aiko ta zata ki kama hannunta ku shiga ciki kallonta baaba tayi tace bana son shirme Aseeyarh ce fa,kankance ido tayi tace wacece kuma Asiya?ko dai itace adar? Baaba ta gyada mata kai tace ehh itace baki gane ta ba washe baki hajajju tayi tace billahi ban gane ta ba kiji yarinya kamar ana kara zana ta Allah mai halitta sai kuma ta fashe da kuka tace tau abunda zanyi saidai Allah ya yafe man amma dole tasani da kuma matan dasuka sak ani gaba sai kuma tayi shiru tace tau bismillah ada mu shiga daga ciki ita dai aydarh kallonta kawai take ,karasa shiga dakin su kai malik na zaune yana kallon t.v dasauri hajajju tarika su shigowa kamar an jifo ta ,ta zauna kusa da malik ta daure fuska kamar bai ta ba daidai sanda ta shigo daidai lokacin gabanshi yawani irin fadi har saida yadan dafa kirji yana mai karanto addua zaunar da ita baaba tayi a kujera kallo daya malik yayi mata ya dauke ido karamin tsaki yayi a ranshi domin tacika parlor da kamshi a tsarin shi baya son macen da take ado da kamshi da fizgar hankalin namiji yasan yanada kyau sisters dinshi na dakyau amma wannan nata yayi yawa tsaki yakara saki yana mai kwabar kanshi da gulmanta dayayi azuciyan shi,ko kallon inda yake batayi ba domin bata masan da wanzuwar shi a dakin ba,duk a takure take she is eager su bata abunda ta zo karba ta wuce bata gaishe da kowa cikin su ba domin gaisuwa ba halinta bane still bata cire shade dinta da yakasance black kanta na kasa tana juya black stone English gold din hannunta baaba tace Aseeyarh bara a kawo abinci ko?girgiza kai tayi alamar aa batareda tayi magana ba hajajju da ta hade rai ta mike tsaye tace yaya bismillah inada magana tayi hanyar fita baaba ta mara mata baya suka shiga dayan dakin hajajju tace yaya baa bori da sanyin jiki kwara ayi komai kafin yamma koh? Ummi shine yah malik yatafi bai jirani bah?auta ce mai maganar tana wani bata fuska cikin shagwaba tana turo baki halime tace tau hala mu ba mutane bane da bamuyu complain ba da yatafi yabarmu? Aysha tace rabo da ita maybe she is only human being here autarh dai batace masu komai ba tayi shiru taji haushi da yatafi wajan hajajjun yabarta,mikewa ummi tayi tace sai kuyi hakuri ai kwa je gobe idan Allah yakaimu kafin ta koma kusan dai hajajju ba ta ban kwana,dariya aysha tayi tace hajajju ikon Allah ni da abby zai yarda da wallahi bin ta zanyi ina son zuwa kano da sauri halime tace idan abby ya yarda yah malik fa? Kuma fa dariya autarh tayi
Chapter 8 · 0% Book details