← Book details Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 197

Sashe 6

Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yayi man yau a kano zan kwana ah ni binta ina zan iya zama cikin masu zuciyar kafurai da mugun abu ina zaman zamana wannan tsohuwar ta taso ni wai nazo batada lapia bancin kaddara da mi zai ma kawoni wannan gida nata kamar zuciyar talaka gida ko farin glop babu sai ja kamar dai bamm,Har hajajju tagama hada kayanta su oum na zaune suna cigaba da tautaunawa da baaba kulu fitowa hajajju tayi da katon ghanan ta tashare hawaye ta nemi kujera ta zauna ta mike kafa tayi kasa da murya kamar ba ita tagama kuka yanzu ba tace a gaskia rufida’u ban taba sanin kunada hankali ba irin yau idan bahaka har miya hadaki dasu dazakiyi musu irin wannan halaccin tau ko ni nadake ciki guda da kakarsu habibun bazan iya wannan abunda kikayi bah gaskia kinyi kokari Allah yayi muku albarka ahankali kuma tace amma shi mai zubin yan fim din indiyan ya amince itakuma diyar wurin naki hwa?murmushi oum tayi daman tasan daga karshe hajajju zata sako tace in sha Allah hajajju komai zai zo manah cikin sauki tunda gaki murmushi hajajju tayi tace aikam nasan ta kan tsiya daman tun sauka ta jiya na kira shi audul din nace mashi gani a yola yace zai zo tau nasan wannan bahillatanar uwar tashi zata hana shi zuwa shikuma rubabben ibrahim din daman bana san ran zaizo idan nake saura yaran dama ba fita suke amma ki bari ya shigo sai nasa kulu ta kiraki kituro man ita adar shima habibun ki tada mashi hankali ki nuna wani jafa’i ke shirin faruwa a najeriyar yayi gaggawar dawowa yauwa tunda tafara magana baaba kulu yake murmushi domin tasan halin yar uwarta tsaf saidai ta shirya yarda komai zai tafi daidai daman tasan sai ta amince da zancan daman kowa yasan halinta shiyasa tayi mata wannan gorin. Karar kiran wayar yasake shigowa a wayar tashi a karo na ba adadi yasan mai kiran kuma ko daya daga bai san abunda zai fada ba bai shirya daukar darun mai kiran ba shiyasa bai daga ba so yake kawai ya cika alkawari yaje dasafe Idan Allah ya kaimu ummi na lura dashi saboda tasan da maganar sai tayi murmushi tace miyasa ba zaka daga ba? Shafa sumar kanshi yace so nake kawai naje zuwa dasafe in sha Allah,Allah yakaimu tace babu wanda yasake magana acikinsu har kowa yagama cin nasa abinci bayan sun kammala halime ta kwashe plates din tayi kitchen dasu shirin tafiya makarantar dare sukayi amma sai malik din yace su bari saboda har yanzu garin akwai alamun hadari ya yayi musu kari a gida godia sukayi mashi aysha har cikin ranta taji dadi saboda sam bata cika son zuwa makarantar bah saboda malamin su dayafiye takura mata da sunan soyayya har ummi takawo ma zancan tashare ta tareda fadin Allah yakyauta kawai babu abunda tace wajan takwas daidai abby yashigo gidan hannunshi dauke da bakar leda wanda fura ce a ciki da fresh nono mai kyau irin na fulanin adamawa gaishe sa sukayi tareda masa sannun da dawowa tambayar su yayi abunda yahana su zuwa karatun dare maryam tagaya masa bace komai sai shiga daki dayayi gidan a tsabtace yake sai tashin kamshin tsintsiyar tsinke yake abinci shi ummi tashigo mashi dashi tareda wajan dazata dama mashi furar Zarah bansan abunda yasa kika takurani cewa gobe sai nadawo Nigeria ba ajiyar zuciya oum tasauke tace amma kasan abbyn baby ba karamin abu bane zai sa nace kadawo nigeria zuwa gobe wani tarihi ne na kaddara wani salo ne da tashin zaune tsaye gaskia ce dakuma asalin rayuwar farko zai maimaita kanshi duk bai fahimce kalaman ta ba saidai gaban shi yayi mumunar bugawa har sai da glass cup din dake hannunshi yayi mumunar fashewa kokarin daidai ta kanshi yayi sannan yace zan biyo private jet around 10:00am in sha Allah munyi landing katse wayar yayi batare da ya jira amsawar oum ba sauke wayar tayi daga kunnata ta zubawa wayar ido tamkar mai son gano karafan daakayi amfani dasu wajan kera wayar wasu irin hawaye suka sauko mata bazata iya fasallata yanayin datake ciki ba farin ciki ko bakin ciki sam ta kasa fahimta bad room tanufa tasakar ma kanta shower ko zata samu saukin abunda take ji a ranta shirya tayi cikin v gown tayafa mayafin gown dinta inner cap ta rufe gashin kanta daya sha gyara da ita tayi matukar kyau duk da yanayin da take ciki yasa ta dan fada sai tayi matukar kyau yarintarta tafito kamar bata haifi aydarh bah dakin aydarh tawuce da sallama tashiga tasame ta tsaye jikin window wannan karon ta Chanza kaya tasaka soft gown baby pink tayi matukar karbar jikinta kanta babu dan kwalli amma ta daure shi tsaf da ribbon kasan kai kallonta oum keyi ko kiftawa babu ganin irin kallon da oum keyi mata yasa tayi rau rau da ido ahankali cikin sanyin muryar nan nata tace oum ina wuni ashe fita kukayi oum banda lapia pah takarasa cikin dan karyar da wuya duk tunanin laifi tayiwa oum dayasa ta tsayawa tana kallonta haka itama oum babu yabo babu fallasa tace Mafarin faruwar komai kaddara zane ne shikuma tarihi ajiya ne babu gaskiar dake boyuwa duk yanda aka so rufeta shin DA SO KAMANE ba iyakar soyayya zata bayanu a labarin bah faruwa da taushan komai zai fara gudana Allah shine masanin daidai hikima da dabara na iya aiki ne kawai akan abunda Allah yasa zai dawo daidai zai dawo hanya yah rabbi kasa mu ci dukkan kaddarorin dake shimfida a littafin kaddarar mu Tace mike damunki ?kasa tayi da murya tace cramps ne ta fada tana rau rau da ido kallonta oum keyi ko kiftawa babu tace tun yaushe da yamma nafara ji kuma drugs din duk sun kare sannu oum tayi fita har cikin ranta taji wannan ma wata dama ce duba da yarda cramps din ke wujujuga aydarh numfashi ta fesar tayi hanyar dakin rufaidarh domin sanar da ita halin da aydarh ke cike kasancewar daman duk sanda aydarh ke cramps rufaidarh ce ke dawainiya da ita duk sanda take cramps saboda acewar oum bazata iya da rakin aydarh bah tsaye tasamu rufaidarh tana jera kaya cikin wardrobe dinta kamar ko ina na gidan shima dakin rufaidarh hakan ya kasancewar mai matukar kyau komai a tsare yake daidai da daidai murmushi tayi tace nikam uktiee ko dan gobe abban aydarh zai dawo ne naga kin wani chanza kamar wata yar shekara sha takwas miye sirrin takarasa cikin sigar tsokana tayi sosai oum tayi tace kinga ki koh uktiee miye wani sirri bayan kinsan komai nikam babu wani sirri kuma ma ai wannan ba irin normal zuwa bane zuwa ne mai dalili hakane rufaidarh tafada agajarce sannan tace akwai abunda kike da bukata ne uktiee no babu yarinyar ki ce ba laifi nazo nagaya maki subhanallah mike damunta cramps?gyada kai oum tayi batareda tayi magana murmushi rufaidarh tayi tace Allah maji rokon bawa Allah mai yarda yaso a duk sannda yaga dama kinga hanyoyin nasara na ta zuwa ta ko ina ta hanyar da bamu zato bah koh zama oum tayi kan Italian bed din dakin tace uktiee nadai zullumi ko fargabar wayewar gobe zuciyata ta dake da duk abunda zai faru goben nayi i’mani kuma nayarda da ubangiji in sha Allah komai zai zo yanda muka tsara komai zai zo cikin sauki da yarda Allah ya maganar doctor ashraff salman tayi magana dashi ne eh uktiee salma tace ta tsara duk yarda abun zai kasance kuma bata samo matsala dashi ba wajan fahimtar yanayi domin shi kanshi shaida ne Alhamdulilah oum tace tareda kwanciya sosai kan gadon tana rufe idonta wani irin sanyi ke ratsa dukkan sassan jikinta dukkan wata kafa ta veins dinta sanyi ke ratsawa jini take jikin na kara yawan gudu a cikin veins din so take ta samu bacci sosai kallonta rufaidarh tacigaba dayi tana tsananin tausan yar uwarta ta hakika ba kowane dan adam bane zai iya aikata abunda oum ba kowane mai rai bane zai iya wannan sadaukarwar ba uktiee bara naje wajan baby kiyi kokari ki samu bacci sosai anan din daidaita gudun Ac tayi tareda sakin duk curtains din dakin kofa taja mata ta fita ko da ta shiga dakin aydarh kwance tasame ta idonta rufe amma tasan ba bacci take ba domin a wannan halin allura kawai ke saka aydarh bacci ahakan ma yanzu da sauki sosai domin kaf Europe countries babu wanda abba bai zagaye ba da aydarh ba saboda case din nan duk da idan asthma ta taso ba karamin wahala take sha ba amma ciwon marar yafi dagawa kowa hankali domin duk rashin tausan ka dole ka ji tausayin aydarh tunda rufaidarh ta zuba mata ido bata dauke ba ji tayi kamar ana kallonta ahankali ta bude ido,idonta dayayi laushi Sosai ba karamin kyau tayi ba duk da tadan fada a wunin hakan sai ya taimaka Sosai wajan fito da asalin zatin fuskar tata kokarin tashi tayi rufaidarh tace no dear kuma ki kwanta no need kamar jira take tafashe da wani shagwababan kuka tamkar wacce aka do’ka ahankali rufaidarh ta taka gaban gadon zaune ta mikar da ita cikin sigar lallashi tace sorry cutie pie maran ne gyada kai tayi ta rike hannun rufaidarh tace second ma gabana faduwa ban san miyasa ba ina jin tsoro I didn’t to be alone please stay Sosai rufaidarh ke jin tausan rungume tayi a jikinta ta cigaba da sauke ajiyar zuciya samun kanta tayi da tambayar zuciya shin ko dai aydarh taji a jikinta akwai alamarin dake shirin faruwa da ita?bata da amsar tambayar tata hakan yasa ta cigaba da tofawa aydarh addua tana shafa bayanta kusan 10mins suna haka sannan rufaidarh tasauka tahadu mata abinci a tray da bottle water marar sanyin ta shigo dakin dashi dakyar tasamu aydarh taci kadan ta turo ganin zatayi amai yasa rufaidarh barinta hakanan magani ta bada tareda gyara mata kwanciya ta rufe da duvet kallonta tacigaba dayi cike da tausayi da kuma kauna kusan 5mins ta bata tana kallon aydarh sannan ta fita tayi bangaran masu maids din gidan saboda akwai abunda take bukata. Sosai suka ji dadin karin da malik din yayi musu kowa yagane
Chapter 6 · 0% Book details