← Book details Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 197

Sashe 33

Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yayi worst har haka ita dai aydarh batace komai kanta nakasa ko dagowa batayi ba hawayen idonta take gogewa gently ganin bata ma kanshi lokaci yake ga condition din malik fita yayi yatafi pharmarcy yasiyo pain reliever injection yafara yiwa malik din kafin yasamu nutsuwa gano abunda yasami malik din sosai yake kokarin kan malik din amma abun kamar yana so yafi karfin sa duk yahada zufa,juyawa yayi yana kallon aydarh dake tsaye kamar zata shige jikin wall din parlor da ka kalli fuskanta kasan hankalinta ba a kwance yake ba yace madam ko mutafi asibiti ne naga kamar his condition is getting worst aydarh dai takasa cewa komai sai bin malik da kallo take,ahankali yake bude idonsa kafin yadaga hannunsa ya taba dr ibrahim dr yayi sauri ya matsar da kunnan sa daidai satin bakin malik din murya can kasa malik yake gayawa dr ibrahim alluran da zaya siyo yayi masa,dr ibrahim likitane yasan kalar alluran yasan amfaninta kallon malik din ya dinga yi kafin ya mike yafita pharmacy ya koma yasiyo alluran ya hadu dana bacci yayi masa,cikin good 10 minutes malik yafara sauke ajiyan zuciya numfashin sa yafara daidaituwa sweating din dayake yana bushewa kyarman dayake yana rage da alama alluran baccin na fizgar sa, dr ibrahim ya kalli aydarh yace Alhamdulilah madam he is getting better ,ina ga zan tafi yanzu tunda nayi masa alluran bacci ko zai farka sai cikin dare ko da asuba kuma in sha Allah daya farka shikenan ma,ko ki kamasa ku shiga bedroom kar ya kwana anan dan akwai sanyi sosai aydarh ta gyada sallama sukayi da dr ibrahim kafin taje tasakawa kofan key ta dawo ta kusa 5mins tana kallonsa ko dauke ido babu,yarda yake bacci a matukar wahala zaka san yayi matukan jigatuwa, mikewa tayi ahankali ta bude kofan bedroom din first kafin tadawo ta dinga binsa da kallo to ita ta ina ma zata fara kama sa ina ita ina shi ma? Kuma yace akai sa bedroom saboda sanyi yanzu yazatayi? Dr hafsa ce tafado mata a rai tayi saurin kunna wayarsa takalli time kusan pass ten yanzu girgiza kai tayi aranta tace yazaayi ta taba sa ita da ba matarsa ba ma ai haramune wata zuciya tace mata ke ce matar ke yakamata ki kamasa,da wannan tunanin yasa ta kara gyara zaman hijabin jikinta hankali tasa hannu ta bubbuga pillow dayake kwance akai,baccin nasa bawai yayi nisa ba duk wani motsin datakeyi yana ji amma bazai iya ce mata komai ba hannunta ta mika masa,kallonta yakeyi sosai ita kuma ta saukar da kanta kasa wani irin rahama ke bin duk wani parts na jikinsa har cikin soul dinsa yake jin sallama da nutsuwa sosai yarike hannun nata as if his life’s defenses on her hand kallonta yake cike da tausai da tunanin daban daban sai yanzu ta dago ido takalli kwayar idonsa tayi saurin dauke kai domin wani irin fuzgagen kyau da tagani kwance a sick face dinsa, tunda aka daura auranta dash isai yau yake kallon kaddarar da abunda aure ke nufi ba karamin tausayin kansa yaji ba da ita baki daya a yanzu fa su basu da kowa basuda komai bayan su biyun shikenan yau da ta Allah takasance akansa bai san irin halin da zata shiga ba,yasaba da wannan ciwon amma bai taba jigatuwa irin na yau,tagaji da durkusan datayi ga tafin hannunta da nashi dasuka hade waje daya very soft and clean, hankali muryanta can kasa tace yace nan da sanyi kaje bedroom bai ce mata komai bas ai bin da yake da kallo kafin ahankali ya mayarda da idonsa yarufe yafara motsa bakinsa ahankali kafin yace sai ki dauke ni ki kaina can din,sai sannan ta bude ido tana kallonsa sosai baki bude kafin tace baka da lapian ma amma sai ka dinga gaya magana “to ni ai bazan iya daukan ka ba wallahi wait did you ever look your self through the mirror?ya girgiza mata kai bakaramin relief yake samu a maganar nan dasukeyi ba tayi kasa da murya kamar mai tsoron abunda zatace tace to wallahi you are very tall and fat takarasa tana kawar da kanta gefe tareda turo baki duk da halin dayake ciki bai hanashi yin murmushi ba dan ba karamin dariya tabashi ba zatayi iya yin kwana biyu batayi magana Amma duk ranar datayi magana sai ta bashi dariya she is very sturbborn and arrogant ga mugun tsoro da raini kuma Allah yaga abunda yagani yayi miskila bai ce mata komai sai kokarin mikewa tsaye dayayi cike da karfin hali yake komai dan he is brave enough duk yarda alluran baccin ke fizgar sa haka ya daure yamike ganin ya mike yasata mikewa itama tana kallonsa hannu yasake mika mata itama ta miko nata hannu da taimakon ta duk da bawani karfin kirki gareta ba har suka isa bedroom din side din datake kwanciya anan yayi ma kansa masauki,wallahi scent din wurin ba karamin dadi yake masa ba hankalinsa nawani masifan kwanciya (ni fa no words can express waye aydarh gareku)komawa tayi can waje wardrobe ta zauna bata jin bacci sam sai ta tura kanta tsakanin laps tun yana kallonta har wani baccin ciwo yayi gaba dashi.Anan inda take tazame ta kwanta bacci barawo yayi gaba da ita,kiran sallan asuban da akayi yayi daidai dawani irin azababan ciwo daya Sake saukar masa wani irin nishi yafara yi wanda yasa ta farkawa daman bata da nauyin bacci sam,jin nishi dayakeyi yasa ta saurin kunna globe din dakin haske tarr tasauke idonta a fuskar sa idonshi yayi wani kala kamar rushin wuta gabanta yawani fadi tama kasa matsawa kusa dashi domin batasan abunda zatayi ba yanzu ma kamar jiya kiran wayan dr ibrahim ne ya shigowa wayan shi daman yabari sai asuban saboda ya daidaici lokacin da zai farka din dasauri tayi accepting call din bata jira jin abunda dr ibrahim ke fadi ba muryanta cike da rauni tace bai fa da lapia har yanzu he is breathing hardly inalilahi waina illahil rajiun shine kawai abunda da dr ibrahim ke fada yace wait kwantan da hankalinki ki bara nakira dr hafsa yanzu tazo ku same ni a clinic kafin yakashe wayan,cikin few minutes taji ana buga kofan part din tajin haka tasan dr hafsa din ce dasauri ta fita ta bude mata hankalinta a tashe kwalla cike a idonta dr hafsa ta kama hannunta tace kiyi hakuri aydarh in sha Allah babu abunda zai same sa kinsan yanzu asuba ne babu masu keke shiyasa na kira yaron neighbor mu shima keke garesa ki shiga sai ku fito mu wuce, komawa dakin kawai aydarh tayi wardrobe ta bude ta fito kudin nan dake cikin bag din ta rike a hannu bazata iya kamasa ba kuma ai bazata ce ma dr hafsa ta kama mata shi ba ahaka tasamu da yarda yake daurewa ta kamo shi dr hafsa ta rufe part din ta cire key din,titi babu kowa hakan yasa basu hadu dawani traffic ba sosai suka isa clinic din dr ibrahim yanajin tsayawar keke yasan su ne yayi saurin fita zuwa yanzu bakaramin galabaita malik din yayi ba da taimakon mai gadi da dr ibrahim suka shigo da malik din cikin clinic dr ibrahim da dr hafsa ke tsaye akanshi dayawa basu da manya alluran da zai bukata tunda zuwa yanzu su biyu duk sun san abunda ke damun shi,fita dr hafsa tayi tabar dr ibrahim a dakin aydarh ta ganinta ta taso daga inda take zaune kafin dr hafsa tayi magana aydarh tasa bayan hannunta ta goge kwallan idonta kafin ta mika mata kaf kudin dake hannunta 20k babu yanda dr hafsa ta iya haka ta karbi kudin domin suna bukatansu wajan siyo sauran alluran, fita tayi tafido wayanta daga aljihun wando baccin tayi dialing wata number ana daga tace gatanan zuwa mai keken daya kawo su shi yakaita babban pharmarcy din duk wani medications daza su bukata tasiya ta koma dr ibrahim ya dinga binta da kallo ganin data da alluran da maganin basu da lokacin tsayawa tambayoyi kawai ya amsa yacigaba dayi wa malik din duk abunda yadace . Dr ibrahim dai baice komai ba har sai datayi shiru ,ajiye abunda ke hannunsa yace ni kaina abun yabani mamaki kuma naga miye zai kawo masa wannan ciwon bayan yanada aure?dr hafsa taware hannu tana tabe baki tace ni kaina shi nake tunani dr,dr ibrahim yasauke ajiyan zuciya yace anyway inaga personal life dinsu ne saboda haka there’s no any need muyi involving kanmu a ciki dr hafsa ta sauke ajiyar zuciya tace “gaskia” ta mike tsaye tace bara naje office dina aydarh na can nasan nagaji nima I need to rest dr ibrahim yace tau ba damuwa zuwa anjima idan yafarka sai kice tashiga ta duba sa bacci yake yanzu tace tau.dr hafsa dake kallon aydarh ko kiftawa babu with seriousness a fuskanta tace aydarh am older than you nayi mamakin dakika bari har mijikin na shiga irin wannan condition din, kinsan mi yafi bata mun rai?yarda. Dr hafsa tace aydarh baki san fushin da mala’ikun rahama zasuyi dake ba kan kusamu sabani da mijinki kin kaurace masa,aydarh are you normal?am highly disappointed on you! wallahi aydarh kina aikinmi zaki bar mijinki kinsan halinsa kinsan yanayin rashin lapian sa amma fushin zuciya yasaki barin sa cikin wannan halin,aydarh dai kanta nakasa sam tarasa abunda dr hafsa ke nufi can ta dago kanta ta goge hawayen dake zuba a kuncinta ta dinga kallon dr hafsa din ta dai yi shiru batace komai ba ahankali dr hafsa tamike ta zagayo inda aydarh ke zaune taja kujera kusa da ita ta zauna,murya can kasa takama hannun aydarh tace nabaki shawara?still aydarh na kallon dr hafsa,dr hafsa tace don’t be silly aydarh you are wise enough take me as your biological sister your eldest sister just feel free let’s talk mike damunki kika bari har kika aikata abunda yafaru? Aydarh ta sauke kanta kasa kafin tasa bayan hannu ta goge hawayen ta tass” tace Allah babu nidai babu abunda nayi masa wallahi, dr hafsa ta saukar da ajiyan zuciya ta mike tsaye tace anyway aydarh zan jiraki duk lokacin dakika ga yadace you are always welcome ,I will be waiting, Aydarh dai tayi shiru batace komai ba,can ta mike takalli
Chapter 33 · 0% Book details