← Book details Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 197

Sashe 34

Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Doctor hafsa tace zanyi sallarh,dr hafsa tace tau shknn ki shiga toilet sai kiyi alwalla akwai prayer mat a bag dina,sai datayi sallarh kafin ta mike,tace auntie zan iya duba sa?tafada tana wasa da gefen hijab dinta kamar mai jin kunyar abunda tafada din,Dr hafsa tayi murmushi ta girgiza kai tace kya ji dashi kibari sai anjima yanzu yana bacci muje gida kiyi wanka kisamu kiyi girkin dazaki kawo masa ki dauko masa kayan da zai sake, Aydarh ta girgiza kai tace ahah zan tsaya anan din babu yarda batayi ba dr hafsa tabar ta amma tace dole sai sunje tayi wanka tayi girki kafin tadawo ba dan taso ba haka tabi dr hafsa din suka wuce cikin gidan tawuce da key din a hannunta ko da tashiga tsakar gidan babu kowa part dinsu ta wuce ta bude tashiga, bedroom din ta wuce tacire hijab din ta linke,few minutes ta dauka tafito a toilet din daure da toilet sai karamin da ta daura akai, Vaseline ta shafa kafin ta dauko sabon bubu gown din dasuka siyo tasaka,plain light purple inner cap din ta tura calaban kanta dake nan ya maida ta kamar kan yaran hadaddun larabawa ba karamin kyau rigan yayi mata ta kwanta a jikinta luff color din rigan yabi skin dinta Side din wardrobe dinsa ta bude ta dinga bin kayan dake nan a wanke tass da kallo faran jallabiya ta daukar masa sai short da singlet dinsa perfumes din dasuka siyo jiya ta dauka tasaka masa a ledan ta yafa mayafin gown din ta fito hannunta rike da ledan,sai sannan gabanta yafadi tunuwa datayi dr hafsa fa tace tayi masa girki ita mi zata dafa masa? Bata taba tunanin rana irin haka zata zo a rayuwarta ba ranar dazatayi regretting duk wani actions dinta na baya bata tsaya ta koyi girki ba duk kokarin oum akan ta koya din kwalla ne a idonta ta gaji da kukan nan she just wants to face the reality now tashirya karban rayuwan da suke a yanzu wata zuciya tace hadda karban shi a matsayin miji? Noo shine ta furta a fili this is the last thing dazanyi a rayuwa na karbansa a matsayin miji bana son sa, knocking kofan da akayi yamaido ta daga dogon tunanin data tafi, ahankali ta ajiye ledan hannunta tanufi kofan ta bude dr hafsa ce tsaye rike da basket a hannu, sanye take da doguwan rigan atampha sai labcot din ta tayafa white jersey veil, murmushi tayi tabi aydarh da kallo kafin ahankali tace Allahumma bareek tabarakallah mrs ABDOOLMALIK you fine die matan malik aydarh tayi murmushi tace thanks dr hafsa tace Allah yasa dai baki daura girkin ba ina shiga gida fa na tuna akwai stew a frigide din inna white spaghetti kawai na dafa,aydarh tayi murmushi kadan tace aa yanzu ne zan daura sai naji knocking dr Hafsa tace tau Alhamdulilah tunda baki daura ba,sai ki dauko masa kayan mutafi na hada abinci dake nasa baki karya bai dan mukaje can sai ki ci ba?aydarh ta gyada mata kafin ta dauko ledan suka fito tana rufe kofan ne dr hafsa,tace yawwa aydarh har zan manta yanzu naga Ramlah a kofan gida tau kinsan inna bata nan,shine nake fada mata yallabai na asibiti idan innan tadawo sai tashiga tafada mata idan yaso sai ta iske mu can kinsan halin inna,idan baa gaya mata ba rashin mutunci sai wanda ta manta,aydarh da tagama rufe kofan ta kalli dr hafsa tace waye kuma Ramlarh?dr hafsa tace yarinya dake part din can aydarh tagane wacce take nufi tsaf amma bata nuna mata ba ta juya kawai suka wuce, a kofan gidan suka samu keke suka wuce clinic din,a keken dr hafsa takalli aydarh tace wannan perfume din naki yanada masifan dadi kuma kinsan mi yahadu da natural body scent dinki shiyasa yake fitan dawannan kamshin aydarh tayi murmushi tace “ Erh” dr hafsa tace ahakan bakiyi lacking komai shine kike nima ki jazawa kanki ko aydarh tafada da alaman tambaya aydarh dai tayi shiru batace komai ba,bakin clinic din mai keken yayi parking dr hafsa ta biyasa suka shiga ciki.Rabiah ce zaune a dakin a kujeran dake kusa da gadon da malik din yake kwance idonsa arufe yake amma ba bacci yake ba,sai wani kallonsa take kamar tasamu t.v dr Ibrahim ne yakira iya yace ta ba rabiah takawo masa ruwan zafi a flask shine tace zata shiga ta duba malik yace mata tau zata iya shiga bara yaje yayi attending wasu patients dasuka zo yanzu, kallo daya aydarh tayi mata ta dauke kai ta ajiye kayan dasuka zo dashi a gefen drawer drugs din dake dakin,dr hafsa ma ta ajiye kayan dake hannunta tace sannu rabiah sai sannan rabiah ta dago tace mata yawwa mun kwana lafiya?dr hafsa tace Alhamdulilah,aydarh ko,ko iskan daya kwaso rabiah bata kalla ba balle har tasa ran zata amsa ta,dr hafsa ta kalli rabiah fuska babu wasa tace rabiah ina ga ki tafi tunda ga mai dakinsa tazo rabiah takalli dr hafsa kafin ta maida kallonta ga aydarh,kallo daya tayi mata gabanta yayi wani irin faduwa wani irin kyau tagani kwance a fuskan aydarh rigan jikinta kamar dan ita akayi ta,batace komai ta mike ta fita daga dakin dr hafsa tabi bayanta da harara, sai da tafita kafin tace aydarh bara naje sai ki tashi sa yayi wanka yace abinci drip din naga ancire masa saura allura daya maybe anjima,ku koma gida,Aydarh tace to, bayan fitan dr hafsa zama tayi a kujeran da tashi wanda tafi kusa da malik din cikin few seconds takare ma fuskansa kallo kafin ta dauke ido karaf yabude idonsa fess a kanta kallonta ko kiftawa babu, ta kalle sa kafin ta saukan da kanta kasa tace how are you feeling? Murya can kasa irin na wanda yayi ciwo yace “fine”batasake magana ba shima bai sake magana basai can yace zanyi wanka, bata tanka sa ba ,ta shiga toilet din dakin very tidy koi na fess kafin tadawo ta dauki flask din ruwan zafin da tagani a gidan tahada masa kamar yanda yakeyi mata,tadawo ta tsaya atsaye tayi folding hannunta a kirji yarda yake kallonta kamar irin yau dinnan yafara ganinta can ta gaji da tsayuwa tace “ko ba yanzu zakayi wankan ba? This is the first datayi masa magana with full respect mamaki yafara yi anya kau itace? Bai ce komai ba yatashi ahankali dan yanzu sosai yake jin saukin jikin nasa sai dan abunda baa rasa ba, hannu yasa ya dauki ledan dayagani nan kan drawer din komawa tayi ta zauna kan kujera ta zubawa waje daya ido ta ina zata farawa dr hafsa bayani to?mi zatace mata tana son koyo? Idonta tasauke kan basket din abincin dasuka zo dashi yunwa takeji amma bata jin cin komai haka yasata yin lamo ta rufe idonta tanaji bacci kadan kadan yana fizgan ta,sai dayayi spending kusan 20mins kafin yafito shirye cikin jallabiyan sai kamshin perfume din data kawo masa yakeyi yakara jaa sai fadawa dayayi kadan hadda suman kansa ya wanke tayi luff akansa,zaman yayi ya ajiye ledan wanda yazuba kayan da ya cire a drawer kafin yadawo ya zauna kan gadon “murya can kasa yace tau ko bazaki bani abinci ba?batace komai tabude warmer ta zuba masa abinci kafin ta dauko masa bottle water da dr hafsa tasaka a basket din ta ajiye masa a gefensa yadinga bin abincin da kallo kafin yace wannan naki ne?takalle sa ta dauke ido kafin tace ina kai kace zaka ci din”baice komai ba yajuya batare da yadauki plate din ba kallo ta dinga binsa dashi,kafin tace wai bazaka ci bane? Sai sannan malik yace hala baki san ni inada cin abinci ba dazaki saka mun wannan dan abinci kamar dai wani yaro sai sannan ta tuna da ranar data gansa ya zuba abinci a plate kamar zasu ci su hudu yana ci batace komai ta kara masa abinci ta daura masa a cinya,sai daya kusa cinye abinci sannan ya lura da ita bacci take nan kan kujera kallon rigan yayi yarda tayi mata kyau sosai duk yarda creams soap shower gels dinta suka chanza amma kalan fatan ta na nan babu abunda ya rage glowing take sosai,idonta a rufe hakan yasa ya dinga kallon fuskanta gashin gaban kanta yayi luff yadan fito har kana iya ganin calaban kanta yarda hulan yazame,dewdrop ya furta can kasan ranta sai yayi maza kuma yayi shiru saidai day agama cin abinci kafin ahankali ya mike ya ajiye plate din hannunsa yasha ruwan kadan kafin ya matsa kusa da ita yasa hannu yashafa cheeks dinta tayi sauri ta bude idonta, yawani hade fuska kafin yace wake up and eat bana son wannan rashin cin abinci, harara ta watsa masa,yayi sauri yasa yatsa ya buge mata baki wani shegen kara tasake kwalla yakawo idonta ta mike tsaye,wallahi saura kadan yafadi wannan abun datayi, kallonta yake ko dauke ido babu,ita shi take kallo kafin ta dauke ido bai ce mata komai sai juyawa dayayi walking majestically and slow har ya isa gaban basket din yabude yazuba mata abinci daidai yarda take ci ya yadaura mata kan cinya kafin ya koma kan gadon ya kwanta ya rufe idonsa yana sauraron yarda zuciyansa ke bugawa, Abinci take ci cike da aji da kuma nutsuwa bata ci dayawa ba ta ture ta bude ruwan nan ma kadan tasha tarufe yanajin duk motsin ta har time din data ajiye abinci ta rufe yaji,tashi yayi zaune yace ki kwanta bara naje wajen dr Ibrahim naga kaman bacci zakiyi right? Ahankali tace ahah ni ba bacci nakeji ba,bai sake magana ba yakoma ya kwanta itama kan kujeran ta zauna tayi shiru.Inna da tashigo yanzu ta goge hawayenta tace tau daman banda anyi niyyar audu ya tsane ni ya tsani kayana,sai a rasa matar dazata kirani nadawo daga wurin rubabban sunan nazo asibitin fisabillahi banda rashin kaunar Allah yayi yawa ace yaro tun jiya akawo sa nan ace babu wanda zai kirani ya gayamun sai tasake fashewa dakuka,malik dai yayi shiru can yace kiyi hakuri hajiya inna kinga sai fa da asuba kuma nayi tunanin ma kina gida ko hafsa ta gaya maki,inna ta mike tsaye ta aaaaa haram haramun wacece kuma haka? Matar da kowa yasan bata kaunar Allah, Aydarh dai na
Chapter 34 · 0% Book details