← Book details Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 197

Sashe 42

Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

takeyi,12:00pm daidai ake tashin su tun 11:40 yazo ya zauna cikin office din headmaster suna fira sama sama kamar irin sun san junan duk kusan headmaster ke yinta,shidai malik na sauraron sa,yana jin an tashe su yayi ma headmaster sallama yafito bakin kofa duk kansu da nikkab wani ya sauke nashi wani kuma ya dage sa sai fitowa sukeyi wasu da goyo wasu ciki wasu kuma da yara rike a hannun sai baza ido yake yaga ta inda zata fito,Gently take tafiya kamar wacce bata son taka kasan har tafito bakin kofan school din duk inda ta bi sai maman baffa da maman noor sun sa kafar su suma,so suke suyi mata magana;tana dago kai suka daga ido har yanzu fuskanta da nikkab murmushi yayi kadan kafin yayi mata waving hannu hango sa tayi hakan yasa ta tafiya ahankali ta iske shi kafin tadaga nikkab din tace “ka cire mun “ya girgiza kai yace mutafi gida sai nacire maki din tayi kaman zata fashe dakuka tace noo zafi fa “ahankali ya sa hannu ya kwance nikkab din ya rike a hannu, maman noor da maman baffa da tun dazu suke kallonsu, ganin abunda yafaru yasa su hada ido, kafin maman baffa tace yah rabbil alameen maman noor ashe larabawa ne?maman noor tace maman baffa ko dai yayanta neb a mijinta ba kiji kama fa suke dan dau kawai kalar skin dinsu ya bambanta, maman baffa tace aaa gaskia kila dai auran zumunci ne gaskia saboda ai kinga class dinmu ba akawo yan mata,maman noor tace ai gaskia naga kyau yau wai Allah.Malik yace mutafi daga wurin aiki nake ,keke suka samu har gida tare suka shiga kasancewan rana ce babu kowa tsakan gida, suna shiga tawuce bedroom sai datayi wanka tashirya kafin tadawo ta linke uniform dinta ta ajiye,tayi tunani yafita shiyasa ta fito ta shiga kitchen din,tsaye tagansa yana zuba pasta cikin ruwan daya tafasa yanzu, kallonta yayi yace aiki ke akwai Sosai yau zaki iya yin stew da kanki ne?gyada masa kai tayi, yafita yace sai na dawo. Tsaf tagama girkin kafin ta zuba a warmer already tayi sallan azahar, kitchen din tasake gyarawa kafin ta dawo parlor ta zuba abinci kadan tacit asha ruwa,kafin takoma bedroom ta dauko jikkanta ta bude littafin daaka koya musu yau tadinga bi da kallo tana maimaita karatun daki-daki du kinda ke bata gane bas ai tasaka pen tayi underlining ta niyyar idan yadawo sai ya ta nuna masa ya gyara mata,knocking taji ana yi ta warware veil din ta yafa kafin ta tafi wajan kofan tace waye? Dr hafsa tace nice,aydarh ta bude kofan tayi murmushi tace welcome auntie,dr hafsa ta mayar mata da murmushi tace thanks dear kafin aydarh tabata hanya tashigo anan parlor suka zauna,aydarh tace ina wuni?ya jikin inna?dr hafsa tace lafiya lau aydarh inna taji sauki ta fita ma,aydarh tayi murmushi tace masha Allah kafin tashiga ta zuba mata abinci data dafa sai ruwa kan plate ta kawo mata,dr hafsa ta girgiza kai tace aydarh kullun nazo ko gajiya bakiyi abinci dai abinci dai dana shigo amma ke idan kika zo nabaki kice kin koshe “aydarh tayi murmushi kafin tace “Allah auntie nakoshin ne “dr hafsa ta girgiza kai tace ai dayake ina lura dake baki son cin abinci sam aydarh tayi shiru tana murmushi bata ce komai ba,dr hafsa ta kalli aydarh bayan tagama kallon books din dake nan ajiye kan carpet kafin tace islamiya kika shiga ne aydarh ta gyada kafin tace erh,dr hafsa tace masha Allah Allah yataimaka,yau kika fara zuwa ne?aydarh tace erh yaune first day dina,dr hafsa tace Allah yabada sa’a aydarh tace “Ameen “babu wanda yasake magana cikin su, dr hafsa ta cigaba cin abinci ta kafin can tace yauwa aydarh so nake ki tambayi yallabai gobe zamuje wajan suna na lura babu inda kike fita sai tare da shi kawai aydarh tayi kafin tace “gobe akwai islamiya kuma “dr hafsa eyyerh karfe nawa kuke tashi ne?aydarh tace twelve ne closing time dinmu,dr hafsat ace ahh Alhamdulilah kinga ai sai wajan four zamu tafi kinga time din ai kun taso har ma kingama girki time din kin huta aydarh tace Allah yakaimu dr hafsat ace Ameen kafin su cigaba da fira sama sama duk labarin friends dinta take bata wani abun dariya wani kuma abun tausayi can dr hafsa tace kinga har naso na manta yau dasafe nafita clinic aka kawo wata zata haihu ,inalilahi waina illahil rajiun aydarh mata na wahala wajan haihu yaron kansa fa yakoma a chest din matar nan gashi yanzu doka ne an hana juyawa saboda ana samun matsala gashi jini ya balle wa matar nan sai bleeding take wallahi abun tausai abun yafi karfin clinic saidai nahada su dawani Doctor a genral da taimakon sa fa muka shiga aiki da ita emergency munyi aiki successfully am the saddest part of the event yaron komawa yayi daga karshe abun ba dadi,aydarh datayi shiru tana sauraron dr hafsa har tayi shiru duk da bawani Sosai ta fahimce abunda labarin ya kunsa ba amma sai data nuna jimamin ta sosai bakaramin tausayi matar taba ta ba da babyn dayarasu,tace babyn ya rasu auntie?dr hafsa ta gyada kai tace ya rasu aydarh ya rasu gyada ta sauke ajiyan zuciya tace Allah yayi masa rahama yaba maman lapia,dr hafsa tace Amin,kafin ta mike tace bara kiga na wuce gida daga general din nake ruwa kawai na watsa na fito so nake nadan samu hutu clinic zan kwana,aydarh tace sorry “dr hafsa tace tau sai anjima ki gaishe da yallaban idan yadawo,aydarh ta gyada kafin ta raka dr hafsa din har kofan part din,ta dawo ta kwashe plates din ta wanke ta ajiye kafin tadawo ta dauki books dinta ta wuce daki.Wanka yayi kafin ya zuba abinci yaci yana ci yana murmushi bakaramin mamaki take basa ba how sharp her brain is yana sa shi jin tana sake shiga ransa, yarda tayi abinci da yarda ta gyara kitchen din sai ya dinga tuna masa dream din wani abu mai kyau daya tabayi a baya yasha yin mafarkin wanda wani lokacin har murmushi yakeyi shi kadai idan yana tunanin mafarkin har yanzu kuma bawai yadaina ba time to time yana yi girgiza kai yayi kafin ya cigaba da cin abinci har yakarasa kafin ya mayar kitchen, parlor yafito kafin yahada iron ya goge sabon dinki dayayi kala biyu wanda daya kala daya ne shi da ango dr ibrahim wanda zasu saka a ranan daurin aure wani hadaddan ash gezner ne mai azaban kyau da tsada wanda Allh musa ne yasiya musu shida dr ibrahim din dayan kuma plain yard ne yasiya white aka masa dinkin kafta duk na bikin ne wanda ranan Tuesday zasu tafi su dawo sat bayan angama daurin aure, Sai da ya gama gogan kafin ya dauki kayan yashiga bedroom din ya ajiye kayan a wardrobe ta na nan zaune kan katifa Still hannunta rike da littafin ta tana sake dubawa malik bai ce mata komai ba kamar yarda ita batace masa ba ya ajiye kayan yafita yawuce masallaci bai dawo gidan ba har sai da akayi isha’I ,yana shigo parlor wayarsa tayi ringing yana dubawa yaga dr ibrahim daga wa yayi kafin yayi kasa da murya yace “bad ai basu gama din ba?dr ibrahim ya fizgan da iska yace ina fa basu gama ba waye daman haka hidiman aure yake malik?malik yayi murmushi yace sai kayi hakuri ai ance idan aski yazo gaban goshi yafi zafi,just keep patience remaining just few days komai yawuce in sha Allah yeah,dr ibrahim yace in sha Allah amma wai daman haka kaji kaima?malik yashafa kai kafin yasa key din hannunsa ya dan sosa girar sa yace haka ma kowa yaji ibrahim amma kasan ko da hidiman sa, dr ibrahim yace hakane amma gaskia yau bazan iya fita kallon wasa ba,malik yace likewise ni gaji yau mun sha aiki oga ma yace idan muka dawo nasarawa Akwai maganan dazamuyi dashi dr ibrahim yace tau Allah yasa muji alkhairi abokina malik yace Ameen, ahankali ta bude kofan bedroom din tafito hannunta rike da books din islamiyanta ,yadinga binta da kallo kafin ya zauna itama ta nemi wuri ta zauna can nesa dashi babu wanda yace komai batayi magana ba shima baice komai ba can tayi kasa da murya kafin tace “ga shi nan din inda bangane bane “malik ya karbi book din yakalli inda bata gane ba, yace tau karanta naji book din takarba tana karantawa ya dinga binta da kallo yayi mamakin jin lokaci daya har ta iya rike karatun, inda bata gane din bane yasake maimaita mata lokaci kadan ta rike ta karanta masa tsab,har sai datagama kafin yace masha Allah, tashi tayi har takai wurin kofan bedroom din kafin ta juyu kuma ahankali ta koma ta zauna ta saukan da kanta kasa tace “ dazu ne auntie tazo tace mun wai nashirya zamu je wurin suna gobe kuma wai na tambayi ka “malik yayi shiru yana ta kallonta kafin can yace wacece kuma auntie? Aydarh tayi shiru kafin ahankali tace dr hafsa,malik yace itace tace ki tambayi ni cike da yarinta aydarh ta gyada masa kai yace su idan zaku sunan kin san sune ko miye?ta girgiza kai kafin yace idan ta zo kice nace aaa bazaki je ba,aydarh tayi shiru kafin ta daga kai tana kallonsa tace itace fa tace zamuje “malik yace nikuma nace bazaki je am I cleared? Aydarh batace masa komai ta koma bedroom dinta ta zauna tacigaba da juya maganan kamar hadda miyasa ma ta tambaye shi ai da bata tambaye shi ba amma ai ita auntie tace na tambaye sa to yanzu idan tazo yazata ce mata,wata zuciya tace ki gaya masa yarda yace din. Kamar yarda sukayi jiya yau din ma haka har sukaje islamiyan kafin yace a maida hankali, tana shiga aka fara karatu kaman jiya yarda lokacin break ajin kamar kasuwa yau dai su maman baffa sun samu dama aydarh na zaune tana duba littafinta maman noor tayi mata sallama ahankali ta amsa masu sai da suka hada ido jin yarda aydarh ke magana hausan ma kaman foreign take mai mugun dadi Maman baffa ta washe baki tace ina kwana ya gida ya yara,aydarh tace Alhamdulilah maman noor tace anya dai yara
Chapter 42 · 0% Book details