Sashe 9
Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tace ahtau dole dai mutun ya zauna adamawa har aysha ta mike zata kwade ta ummi tace ba fa na son shirme ku tashi ku kama aikin gabanku da alamar hadari a garin nan ,yauwa ummi daman so nake mu juya tsarin dakinmu cewar halime,Maryam ta kwabe fuska tace ku kullun da aikin da za ku dinga jawo manah babu wanda ya tan ka ta cikin ,Abbyn malik ga ruwan can na kai bayi idan sanyi baiyi ba sai nasake sirka shi mikewa yayi yakamo hannunta yace Allah yayi maki albarka yabiya ki da gidan aljanna murmushi ummi tayi tace Ameen yah rabbi miji nagari . Rufaidarh tace amma dai uktiee duk da halin da ake ciki yakamata ko saloon ne kije sharp sharp ayi maki sabo fa da Allah mutunan ya saba duk tafiyan da zaiyi yadawo zai tarar dake kal kamar amarya wannan karon kuma yazaayi kibari yadawo ya tarar dake babu lalle babu gyaran kai oum batace komai sai warware salkaqiyar sumar kanta baka sosai har gadon baya tashafa tace yanzu uktiee gashin nan fa babu abunda yayi and kuma na fiso yazo ya tarar dani ahakan domin tun kafin wanzuwar komai yasan akwai matsala ,hakane fa uktiee wannan ma wani tsarin ne saboda shi kanshi zaiyi mamakin ranshi gyaran naki,can kuma tayi murmushi tace uktiee n isai naga ramar nan dakikayi kamar ba wannan damuwan bane kawai anya uktiee tafada tana sake rike dariyar zaro ido oum tayi tace anya mi? Babu komai rufaidarh tace sannan tace ko dai aydarh zaa wa kanni ko kanwa ban sani bah hararar wasa oum ta ballawa rufaidarh tace saidai ke idan kin amince da doctor Ahmad sai kiyi mata amma nikam badani ba dariya rufaidarh tayi tace uhm ni kwana biyu ma ya hakuri ko waya bama yi oum tace ai laifinki shi pa gani yake kamar takura maki yakeyi shiru rufaidarh tayi domin bata shirya kare kanta wajan oum ba kan korafin ta kan doctor Ahmad din,oum tace uktiee nagani nake lokaci bai gudu kamar komai bazai faru a ya uba gyara zama rufaidarh tayi ta kamo hannun oum tace ki kwantar da hankalinki uktiee in sha Allah Komai zai tafi daidai karar ringtone din wayanta ke tashi tana dubawa taga abba ne da number shi ta Nigeria that means sunyi landing kyarma jikinta yakama kirjinta na lukude yana dugan tara tara cikin sanyin da jikinta yayi ta amsa wayar tamkar mai jin bacci ko wace take fama da kasala kuma agajiye sallama tayi daga can ya amsa tareda sanar da ita yana airport basai tazo ba tabar driver yataho kawai ya daukeshi da tau ta amsa tare mikewa tsaye duk wani nutsuwa ta, ta tanema ta rasa sai kai kawo take har rufaidarh ta fadawa drive sakon ta dawo oum ta tsaye zaunar da ita rufaidarh tayi tace uktiee ki nutsu ki kwantar da hankalinki nasan abba aydarh bai daukar komai dasauki amma in sha Allah abunda mu ka saka ma ranmu shima shine hukuncin shi Allah yasa uktiee Allah ya amince Ameen rufaidarh tace sannan tawuce kitchen domin karasa girkin da suke ita oum da kansu domin abba bayace girkin kowa idan ba na oum ba inhar yana kasar. Zama hajajju tayi tace am audul tashi zakayi ka dauke ni da ada mu tafi can gidan naku ai Ibrahin nan koh? Kallonta malik keyi ko kiftawa babu yace wacece haka? Sake daure fuska hajajju tayi wai ita ala dole taci serious tace zaka tashi ko sai na zab zabga ma mari,aydarh sam bata fahimtar su zufa ke tsatsafu mata a goshi da hanci zuwa yanzu har tayi ja ba karamin dauriya take ba amma marar kamar zata fito tsananin azabar da take mata duk baaba kulu na lura da yanayin ta cikin sanyin murya tace Aseeyarh ta shi ki bisu ki bashi key din motar naki ku tafi can gidan su sai ki karbi sakon ki wuce gida tau kawai aydarh tace tareda mikewa tabar key din kan kujera domin bazata iya mika mashi ba da hannunta bacin bazata iya driving da kanta ba kuma rufaidarh tace mata da ta karbo maganin shikenan ba amma da babu abunda zai sa tabar su ,su shiga motan ta ba ganin key din da tabari kan kujera yasa baaba dauka tamikawa malik bai ce komai ba yakarba yayi gaba shima.Bayan fitar malik da aydarh hajajju tayi kasa da murya tace yaya muna fita kema ki rufe wannan kurkukun ki tafi can gidan habibun zuwa yanzu ya sauka ku jirani acan kar ku damu zanyi komai kan tsari in sha Allah baaba tace tareda zama tana jiran tashin motar su sannan itama ta shirya tafita, back sit ta bude ta shiga tana hade rai ganin yanda yake wani shan kamshi yana wani isa trash shine abunda tace can kasa yanda babu wanda ma zai ji ta hajajju tafito da wata katuwar jikka da uban mayafi ta bude front sit ta hakimce sai daurewa take babu wanda ta tan kamawa cikin su shidai malik bai ce mata Komai ba duk da ya lura da daurewar da hajajjun keyi cikin kwarewa nutsuwa kamala yake driving yanda motar tayi fitting dinshi kana iya rantsewa kace tasa ce har suka isa anguwarsu babu wanda yayi magana cikin su ukun bin anguwar da kallo aydarh tayi kusan iri day ace da anguwarsu baabarh sai dai wannan gidan yafi gidan baabarh girma da kadan ko Parking bai gama ba hajajju tasako ta bude baya tace ma aydarh tasako ahankali aydarh tasako yau kam angama da rayuwarta zuciyarta har dace take ganin irin anguyoyin da oum tasaka ta zuwa a yau din gani take tamkar rashin aldalci ne mahaifiyarta tayi mata,hajajju ta katse mata tunani lokacin dake cewa malik tau dan cifil sifense kazama ba’a sani ba komai kawani tokare jikin kofa kamar wani rubabbe ba zaka kwankwasa a abude manah ba shidai kallonta yake he was speechless ganin lokaci daya hajajju ta juye tana ta masifa kamar ba ita tagama wasa da dariya ba dazo,knocking yayi halime ta bude. Halime ta bude ganin hajajju tsaye kamar wata yar wrestling sai faman hura hanci take yasa ta washe baki tace yau tsofaffin kano ne a yola kenan?wata muguwar harara hajajju ta watsawa halime tace yau dai anbani muna ganin jafa’I kala kala bacin maganar da dan uwanki ya kwaso sai kin tsaya a kaina kina kallona kamar wata rubabba, shidai malik kallon hajajju yake sam ya gaza fahimtar abunda hajajju ke nufi to waye dan uwan nasu shi ko wa?to mi yayi? Kama hannun aydarh hajajju tayi suka shiga gidan aydarh sai bin ta take da kallo suna shiga hajajju tasaki aydarh,Ta fadi kasa kamar mai aljannu ta dinga kwarara ihu kamar wata tababba da sauri ummi da abby suka fito daga cikin daki suna kallon sarautar Allah ummi dai takasa cewa hajajju komai sai kallon aydarh take da mamaki domin har abada bazata taba mance fuskar da kamanin oum ba ko tayi rantsuwa babu batun kaffara wannan jinin habib da zarah ce to amma miya kawo ta gidan wannan wacce kala sabuwar kaddarar ce takasa ba kanta amsar ko wace tambaya a ciki yasa ta mara wa abby baya suka doshi inda hajajju ke ta zabga ihu tana kuka, mun shiga uku mun lalace wannan wace kalar rayuwa ce ibrahin kana zaman zamanka an yayo ma jafa’I an yayo ma bala’I ,abby was shock har kusan 5 mins abby da ummi na kallonta babu wanda yayi kokarin hanata domin sun kasa fahimtar komai sun shiga matukar rudani ganin aydarh da hajajju a gidan ga kuma malik tsaye ya zuba hannu a aljihu yana kallon ikon Allah,halime maryam da aysha suma duk sun tsore babu wanda yasan abunda ke faruwa sai kallon aydarh suke lokaci daya suka ji tayi mugun shiga ransu.shiru hajajju tayi ta goge idonta tass ta kalli abby tace ai batsaye za kuyi kamar matattu ba shiryawa zakuyi mu tafi aje asan yarda za muji da wannan bala’in ummi tayi karfin halin cewa hajajju mike faru ne? Shiru hajajju tayi sannan tayi mitsi mitsi da ido tace idan mukaje can kwa ji komai ,abby yayi ma ummi alamar datayi shiru sannan ya juya ya shiga daki binshi ummi tayi domin kaf ji take hankalinta da tunaninta baza su iya daukar duk abunda ke faruwa ba ,ajiyar zuciya abby yayi cikin sanyi murya yace Aseiyarh kisaka hijab dinki mu bi hajajju domin ni kaina a cikin rudani nake.Tafiya suke cikin mota babu wanda ke magana cikin su biyar din sai hajajju dake ta rusa kuka babu sararawa wallahi daza’a bude zuciya aydarh ji take kamar zata mutu wannan wasan kwaikwayon yayi mata yawa a kai daga karban magani sai wahalan da rayuwarta ake what’s all this? Hajajju tayi shiru tace tau ada yazaki barmu munata walagigi kan hanya bazaki gaya manah anguwar ba ?aydarh da bata fahimce tambayar da hajajju tayi mata ba tunda suka shigo motar da abby da ummi ta saukar da kanta kasa takasa hada ido dasu gabanta cigaba da faduwa yake sosai batasan dalili ba ga ciwon maran nata kamar kara karuwa yake tunda tafarawa malik kwatancan gidansu gaban abby ya yanke yafadi gidan habib? Shine tambayar dayayi wa hajajju shiru hajajju tayi kamar bata ji shi ba ummi dai kamar bata cikin motar tsabar yanda hankalinta yakasa kwanciya da tafiyar tarasa yanayi da zata saka Lamarin jujuya maganar hajajju take , tsaki malik yayi cikin ranshi yace wai wannan wace kalar yarinya ce komai nata kamar ba mutun ba who is she yasake jan dogon tsaki kasa da murya hajajju tayi tace Allah na tuba wannan abu dami yayi kama ibrahin ni bakina ma yayi nauyi wajan fadin wannan masifar sai kuma tasake fashewa da kuka,duk yanda aydarh ke faman riqe ciki tana zufa duk da sanyin a.c na kadawa ummi na lura da yanayinta kallo daya tayi mata tagane tabbas itace to amma mike faruwa ?mike shirin faruwa ? Wannan wane irin rikitaccan al’amari ne mai wuyar fassarawa yah rabbi kasa duk abunda zai faru yazama alkhairi tafada tana lumshe ido , sannu shine kalmar da ummi tacewa aydarh duk da bata gaishe su bata ko daga ido takalle su ba amma wani irin yanayi ummi taji game da