Sashe 112
Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da tausai maryam ke kallonta tace wai auntie faduwa ce ko miye ko ciwon kafan ne haka nan?aydarh ta saukan da kanta kasa tama kasa magana aysha tayi mata wani kallo tace bafa nason surutu kinsani kuma “maryam taja bakinta tayi shiru aysha takama aydarh da kyar suka shiga toilet din,halime da ta sallame sallarh tace muje waje nafada miki yarinya maryam tawaro manyan idonta tace dan Allah yah halime?halime tace da banyi niyya ba da har nace muje waje “fita sukayi reception Maryam tabaza kunnuwa tana sauraron halime “halime tayi kasa da murya tace ina ganin fa miscarriage tayi shine take ta wannan jinyar “maryam tace eyyerh wayyo Allah amma naji tausayinta tasha wahala Allah “da kyar fa take tafiya daman haka akeyi?halime tace nikaina ban sani ba maybe ko twins ne shiyasa tasha wahala hakan nan “maryam tace Wallahi yah halime ina sonta kaman yanda nake son yayah “halime tace nima haka maryam tace kuma har tafi yayah kyau ma fa “harta mamanta tafita kyau,halime tace ai ni ban taba ganin kyau kalan nata ba ga gayu fa “sosai yar gayu ce bana wasa ba maryam tace ina son scent dinta kiga rigan datasaka yau din nan “halime ta rage murya tace ke banza bakiga ma kaman tana fushi da yayan ba maybe fada sukayi ko yayi mata wani laifin maryam tace eh fa nagani ko ba bacci take ba daya shigo ne sai kiga ta rufe idonta “halime tace kinsa rahama kebani wani labari maybe suma hakan tafaru maryam tace namiye?halime tace maybe wajan wannan abun cikin ya zube kila da karfi yayi mata shiyasa take fushin fa “maryam tawara ido tace kai haba nidai yah halime ba ruwana Allah kedaman kin iya suchs magana “yanzu sai nafadawa addah fa halime tace tau dan ubanki bismillah idan kin fasa “maryam ta turo baki tace ita dai yar baiwar Allah sai kunya ni daman yayah yace na shirya su tafi dani can Washington din billahi halime tace you are sick gaskia maryam tayi wani kala da fuska cike da masifa tace ban gane am sick ba saboda miye?halime tace maybe ma fa zaki iya bata shekara daya Allah yarinya ce kawai saboda she is full package and well shaped shiyasa zaki ga haka kuma dai baby face gareta maryam tace nasani manah ai dai naga har addarh ma tafi hankali shiyasa nutsuwa gareta ga bata son hayaniya saidai ta dinga wannan cute smile din nata ga hakorin makka “halime tace kinsan ma yayah bazai yarda ba ummi ma haka har kwara abby ma “Maryam tace wai ma ina ruwanki sai anbarni din halime tace lallai yarinyar nan baki da saiti kin raina ni bara na saba miki jiki a asibitin nan marar kunyar yarinya halime tayi kaman zata bigeta da sauri Maryam ta juya ta bude dakin tashige da gudu malik na daidai shigowa girgiza kai yayi ganin har yanzu basu daina behaving kaman tom and jerry ba “sun manta asibiti ne nan din kuma yana nan shiyasa maryam na shiga dakin da gudu saboda tasan tsaf halime zata jibgeta tayi bayan aydarh da niyyar ta boye bayan tagama salla bata koma ta kwanta ba ta gaji da kwanciyan yasata kama karfen gadon ta rike tana gwada tsayuwar “Ko hijab dinta bata cire ba,red hijab ne yayi mata kyau sosai maryam da kawai kokarin ta wani ya cece ta bata kula da kyau ba ta taba aydarh kasancewan jikinta babu kwari ko kadan tayi bay abaya zata fadi hankalinta yatashi ta tsorata sosai malik dake bakin kofan budewar sa kenan yayi kanta dawani over speed daf ya dauketa bata fadi ba amma ta rufe idonta gam ta fama wajan ciwon sosai “kuka tafasa marar kara sai ga hawaye sharrr bakaramin fama wurin tayi ba Wallahi azaban radadin yayi mata yawa kwantar da ita yayi without wasting a second yafita zuwa office din dr raudarh equipment din dake cikin box kawai ya dauke baki daya hada stitchs box din dr raudarh bata cikin office yafito yakoma dakin “yafara bude kayan aysha da duk hankalin su yatashi ta kada su suka fita reception su dukka ukun maryam da hankalinta in yayi dubu yatashi ganin abunda taja kuka kawai tafara aysha kam fada tafara yi musu kan abunsu yayi yawa ai gashi “malik ya dage riganta yaga da gasken dai tafama “allura yayi mata na rage zugi “kafin yafara duba stichs din har cikin ransa yake feeling pains dinta sosai ahankali ya gyara mata kafin yasake mata another injection tsaban wahala bacci ya kwasheta ajiyan zuciya yayi yacire gloves din hannunsa yana share zufan goshinsa “ganin tayi bacci yasashi rufa mata duvet “kafin yamayar da kayan a box ya rufe yawuce toilet yacire kayan jikinsa ya sakarwa kansa shower yakai 20mins a kasan shower kafin ya mayar da kayansa yafito Still bacci take chair din gaban gadon yaja ya zauna ya buga tagumi yana kallonta “ko dan kiftawa babu “maryam tace nashiga yanzu na duba ta addarh?ganin duk maryam ta firgice yasa aysha gyada mata kai kaman jira take ta shige dakin malik yadago suka hada ido maryam tayi kneeling kasa muryanta very slow ga alaman zatayi kuka tace am sorry yayah Wallahi malik ya daga mata hannu kawai yace it’s okay prettiest girl ki kula next time kinji a daina rawan kai “maryam tazo dasauri tabashi side hug kafin tayi kissing cheeks dinsa both tace tau yayah ita auntie bazata ji haushi ba? Malik yace yes “maryam tace tau yayah na zauna beside her please?’malik ya gyada mata kai ahankali tace thank you yayah “ .Abby yayi musu narrating kaf labarin da malik yabasa wanda babu bambamci dana baba abba was confused and shock at the same time yama rasa mi zaice yaron yayah ibrahim ke aiki a Washington kuma as MD na wannan babban asibitin ohh Allah this is unavailable tau yaushe ma har yaron yasamu scholarship yayi schooling a wannan babban uni din?baba ce ta katsewa abba tunaninsa dafadin Habib kaine mai mace kuma yara dai suna son junan su ina ganin ayafewa juna zumunci bawasa ba komai yawuce abba bai yama kasa magana mikewa kawai yayi yawuce hanyar part dinsa duk suka bisa da kallo hajajju tace yau dai muna ganin ikon Allah wannan fa daya tashi yanajin ana fadin yaro hutun kwana bakwai kawai yasamu kafin jirgin su yakuma can kasar nifa bana kaunar rashin kan gado tau ina duk da dalilin hakan fisabillahi ibrahin kai ma ka gode Allah baiyi maka arziki ba yayi ma danka yanzu don audul yahade anguwan nan ya siye bawani abu bane ahtau kuma daya mike yawuce ai bashi kawai bane mutun a famelin nan naga uban ya isa ya datse auran cikinku tafada tana mikewa ta dauka jakkarta tana yafa mayafinta ta kalli abby tace kunga tafiyata can asibitin yarinya na can daga ita sai waennan yaran masu dan banza rawan kai ita kuma babbar girman kai bazai taba iya barinta yi musu magana ba ummi tamike ahankali tana kallon abby tace ka mayar damu yallabai “abby yamike baba tace mu ma muna bayanku in sha Allah zamu gana da fatiman ne da yar uwarta hajajju ta tabe baki tayi gaba tace yaro dai yafi karfin raini illimi garesa ga kudi kaca kaca a akawun dinsa ahtau mutunan dake aiki cikin turawa gashi babba a asibitin “ummi da abby dai sunyi shiru suna binta a baya har suka karasa asibitin batayi shiru ba abby n eke dan bata amsa shima dayaga lamarin yafi karfinsa yayi shiru kawai “anan reception suka ga halime da aysha gaishe su sukayi hajajju tanemi wuri kusa da aysha ta zauna abby ma haka ummi tawuce knocking tayi kafin tashiga Still aydarh na bacci “maryam kusa da ita sai malik da ya jinginar da kansa a karfan kujera da alama tunanine yake “maryam naganin ummi taji gabanta yafadi kar ace halime tafadi abunda yafaru tasan aysha bazata fadi ba ta dai daure tace sannu da zuwa ummi “ummi tace yauwa ya jikinta? Maryam tace alhamdulilah bacci take “ malik yadago kai yakalli ummi yace ina wuni mamana?ummi tace lafiya ya jikinta malik yace Alhamdulilah babu laifi yau ta dan amsa sa dasakin fuska har sanyi sai dayaji a ransa yau dinnan kujera taja itama ta zauna tana kara jinjina ikon Allah malik dinta dai ke da wannan matsayin da aka fada Allahu akbar “ can sai ga hajajju da abby sai halime da aysha suma duk sun shigo malik yamike yana kaiwa abby kujera kafin ya dan rissina suka gaisa ‘yamaida dubansa kan hajajju yace barka da zuwa hajiya hajajju tawashe baki tace yauwa dafta ya jikin ma dakin taka?malik yace dasauki ganin kaman babu wanda ke cikin damuwa sai ya danji yafara nutsuwa duk babu wanda yace masa gashi shi kuma bazai iya tambaya ba yaso ace hadda baba kulu da sun dan fita ta masa bayani ko hankalinsa zai dan kwanta. Hajajju tace yoo wai maryam nan dakika zuba ma yarinyar nan ido fa fisabillahi? Maryam dai tayi shiru batace komai hajajju tace sai ki dinga cutar da kallo ita dai ahaka kaddararta yazo kuda dan uwanku ku dinga cutar yarinya don kunga batada hayaniya bata da magana sabo hwa da Allah ummi dai na zaune batace komai ba hajajju ma taja bakinta tayi shiru kafin tamike tana sabar jakkarta tace dafta bismillah zo mu fita muyi magana malik da kaman jira yake ya mike yabi bayan hajajju “ummi tabi su da kallo kafin ta dauke ido tana maida dubanta ga aydarh da still bacci take maryam kuma na latsar wayan aydarh sai ga halime da aysha sun shigo suma atare “halime ta kalli maryam taware ido tace addarh dubi yarinyar nan fa da 16pro a hannunta “aysha tace kun min shiru halime ta kama bakinta kafin ta zauna kusa da aysha tayi joining dinta a kallon wayan kaman basu suk agama fada last last ba “aysha tazauna kusa da ummi tace sannu ummi,ummi tace yauwa aysha ya mai jikin taci abinci kam?aysha tace taci pieces uku karami na pepper chicken din nan har yayah yafita yasiyan mata grilled meat ko zataci yaran can ma sukayi hauka bata samu taci ba ummi dake kallon aysha da mamaki tace hauka fa kikace mi sukayi