← Book details Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 197

Sashe 30

Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tana so batasan gidan ba kuma batasan yarda zata ce mata bata sani din ba ,sai gashi malik yace tashirya yarakata gidan inna,har yanzu magana bata shiga tsakanin su duk da a yanzu suna zama parlor tare amma babu wanda ke ma wani Magana. Sa kai kawai yayi,yafita ganin hakan yasa ta bi bayansa da harara tana tura masa baki “ shi yasa key ya rufe kofan part din nasu yana gaba tana biye dashi ba,maman Ramlah dake wanki a can ventilation dinta har ta hango su ,dasauri tanuna ma,fadila dake nan tsaye tana sanaar surutu kamar mai cutan dimi, itama kallon tabi su dashi kamar zata hadiye su, cikinsu babu wanda ya juyu balle ya kalli iskan daya kwaso su,tafiya yake kamar wani boss sai sauri yakeyi fita sukayi kofan gida,ya tarar musu keke kallonshi take ko kiftawa babu bata shiga napep din ba, bai lura da bata shiga dan shi har yashiga ya zauna ,can ya lura da ita da kallon datake masa, ahankali yayi kasa da murya yawani kafe da ido yace ko komawa zaki ni natafi? Tawani juyan da kai ta balla masa harara kafin tace ina fa inna tacemun anan anguwan suke?bai ce komai sai yayi shiru ya saako daga napep din side din datake tsaye yaje yakama hannunta tawani zaro ido tana kallonsa bai ko kalleta ba ya turata napep din shima ya zagayo yashiga yace wa mai keke sutafi har suka isa kasuwan babu wanda yayi ma wani magana cikin su suna sauka yafido kudi yabiya mai keken ganin yasauka yasa itama ta sauka tanata kallon inda suke ko kiftawa babu kamar tana tsoron wani abu haka tayi raurau da ido tace masa ina ne nan? Gaba yayi batare da ya kalle ta bayace siyar dake zanyi,duk da abun datake ji bai hanata hararar shi ba yana juyuwa karaf suka hada ido yaganta tsaf bai ce mata komai ba dan wannan bashi bane first time daya taba kamata tana hararan shi ba,duk inda yasa kafanshi sai tasa nata kamar wani zai dauke ta indan ta daina binsa,kanta ta saukar kasa ganin irin kallon da mutane ke binsu dashi, wani babban shago suka shiga babu abunda ake siyarwa sai inner wears Abayas da kuma bubu gown pure cotton, gaisawa sukayi da mai shagon mace ce wata hadadadiyar Hajiya tasha atampha vilisco taci uban gayu,sannu da zuwa tayi masu hadda wurin zama shagon sai kamshin turaran wuta yake da khumra kasancewar duk tana siyarwa, tambayar su abunda suke bukata tayi ya kalli aydarh sannan ya mayar da kallonsa kan matar yace inner wears zata zaba daga nan bai sake magana ba ya saukan da kanshi kasa yana latsa wayanshi, mata tace Hajiya mi da mi zan dauko maki?sai da ta dago kai taga bai kallonta kafin ta yi ma matar nuni da hannu wasu classic brassiere ta nuna mata masu tsada saboda hakan ma yasa ta fidda su gefe guda foreign ne matar tayi murmushi tace tau size nawa aydarh tafada mata cikin wannan voice din nata, matar ta bi aydarh da kallo a ranta tana mamakin size din da ta gaya mata anya bai mata yawa ba,batace komai ba ta dauko mata wani hadaddan black lace form bra sai baby pink dark green da kuma red aydarh tabi su da kallo imagination din nata ne na gida, tasan price dinsu bai kai natan ba,amma duk da haka sunada kyau pants tasa aka dauko mata this time matar kasa shiru tayi sai datace diyata anya size din daidai kika fade sa?aydarh tayi kasa da kai sannan ta gyada mata kai malik najin duk abunda ke faruwa amma ya ki dago kansa balle ya kalle su ita dai aydarh takagara agama su tafi bata son ya dago kansa yagani,shima pants din kwara hudu ta dauko mata kowani irin bra din, matar ta tambaye ta hadda undies aydarh ta girgiza kai kafin tace aa sai sannan malik ya dago kai yace shima a saka kwara hudun,bai jira amsar matar ba dan yasan ma aydarh bazata ce komai ba ya fita kofar shagon, wani bubu gown ya dauko light purple mai haske Sosai duk jikinshi sai flowers din jiki black har zip din gaban gown din purple ne da black mai shining ba karamin kyau tayi irin ta yan gayu na sosai da sosai yashigo dashi rike ahannu babu wanda ya kalla cikin su ya ajiye ya koma inda yake zaune ya zauna matar tayi packaging rigan da mayafinta babba ne ba laifi tana yabon zaben dayayi kafin tace tau ranka ya dade an mance da inner caps suma muna siyarwa na lura matar taka bata son kana wahalar kashe kudi, malik yayi murmushi kadan yace tau ba damuwa hajiya a dauko guda hudu shima aydarh najin su dai batace komai ba matar ta dauko wani karamin basket cike da plain inner caps yards din masu kyau masu tsada, ta ajiye gaban malik tace zabi”sai daya kalli aydarh kafin ya maida duban shi a basket din light purple yafara daukan mata sai ya dauki black da pink sai wata kamar ash kamar grey, duk kayan ta hada masu cikin ledan shagon ta lissafa masa kudin ya fido 35k daidai yace ta bata turaran na 5k matar ta washe baki tace tau shknn turaran kaya dana jiki ta dauko ma aydarh masu dadin kamshi Sosai tayi packaging din a tasu leda kafin ta hada su waje daya cikin ledan kayan godiya matar tayi masu sukayi bankwana har zasu fita kafin tace yawa ranka ya dade dan Allah zan iya samun number madam ko naka idan kuna son gyaran jiki ko lalle duk ina yi har kayan sawa na maza ina siyarwa, kafin ta rufe baki aydarh tace “no”shidai malik baki bude yake bin aydarh da ta tsare shi da ido da kallo tawani hada fuska kamar irin yaji tsoron ta kar yayi din nan, sai ya juya ya kalli matar yace sorry Hajiya zamu dawo wata rana ai in sha Allah ,matar tayi murmushi tace babu komai Allah yatsare,suna fita tace wai bansan mi ma yahanani tambayar su daga wani kasar suke ba wallahi sai kuma tace umm ina fuskar hakan cikinsu kowa kamar sarki duk sun tsare gida babu sakin fuska amma akwai dan banzan kyau wai Allah, ji yarinya karama amma ji body structure shiyasa aka ce natural daban yake da artificial mu dake bankar supplement ina zamu hadda kanmu da jikin yarinyar nan. Cikin 50k din da Allh musa yabashi jiya kyautan Allah saura 15k flask yasiya karami mai madaidaicin kudi wanda zai dinga ajiye mata ruwan zafi saboda yanayin aikin shi yanzu kusan sai yamma take wanka idan tayi dasafe mamadin tayi da rana sai yamma ga garin damuna gudun shi kuma sanyi ya kamata, man kitso yasiyan mata da pink oil sai comb da tsinke tunuwa daga nan gidan inna zasu wuce dr hafsa din tayi mata calaba kamar yarda inna ke gaya masa dan shi bai sani ba tunda ba wani shiga harkan juna suke ba,plate shoe yasiyan mata masu kyau sai yasiyan ma inna daya itama da sabulu da klin leda daban ya fidda kayan inna ita kuma yabar mata nata wuri daya babu abunda ya siyar ma kanshi,napep ya tarar masu suka isa har kofar gidan inna yabiya mai keken kudi kafin ya mika mata ledar kayan da yasiyawa inna da man kitso comb da tsinke din kallon shi tana turo baki tace ina kaima shiga zakayi ? Hannushi daya yasa cikin Aljihu yawani daure fuska yace eh shiga zanyi amma ke zaki rike wannan din,bata sake cewa komai ba tayi gaba ta bar masa kayansa a nan tashige gidan inna dasauri,bin ta ya dinga yi da kallo bata magana batada hayaniya amma akwai taurin kai da rashin kunya bakar magana kam sai wacce ta manta kawai ke bata gaya mashi girgiza kai yayi ya dauki kayan yabita baya inna nagani shigowar su ta mike tsaye tace kai kai kai kune tafe oyoyo asiya sannu da zuwa aydarh tayi murmushi ta dukar da kai kafin ta russuna tace ina wuni? Inna ta washe baki tace lahiya lau asiya ya gidan da audu baki daya?aydarh tace Alhamdulilah,malik ya bata fuska yace ni sai na koma ai,inna tayi kasa da murya tace ash eke dashi kuka zo aydarh dai kanta nakasa batace ma inna komai ba,inna ta kalli malik tace indai ba aikin sintiri kasamu ba yaci ace kashigo tunda kuka zo,inna takama hannun aydarh suka shiga cikin daki aka bar malik nan tsaye,inna ta kalli aydarh tace wallahi nake gaya maki tau bayan ma ba kaunar Allah yake ba tun farko basai ya gayaman sunanki haka ba fisabillahi,aydarh dake murmushi ta gyada wa inna kai,inna tacigaba dacewa “tau bai fada bas ai dai naji ya kira wani suna da larabci nidai ba fahimtan sunan nake bas ai fa ranar matar dake zaune nan gidan,wa take da suna ma hafsa ita ke fada mun sunan naki nidai ba ma yarda nake da maganar ta ba,sai dana tambayi shi audun da kanshi yake ce man ai sunanki haka aydarh dai sai murmushi take,malik yace ma dr hafsa suna ciki ni tafiya zanyi yau inna bata ni take ba daman kuma ba zama zanyi ba dr hafsa tayi murmushi tace tau kashiga sai kuyi bankwana da innar “da sallama yashiga dakin inna ta amsa masa kafin yace ga wannan babu yawa inna,inna tabi ledar da kallo kafin tace Allahu akbar audu nagode sosai Allah yasaka maka da alkhairi Allah yakawo zuri’a ya dayaba Amin dan nabiyyu rahamati malik yashafa kai yace Ameen inna ni bara na wuce idan anjima sai nadawo in sha Allah,inna tace tau Allahu yasha, ledar man kitso da pink oil din ya bar mata sai comb da tsinke tunda yasan dasu zaayi amfani babba leda kayan nata da turare ya dauka yafita dash isai dayayi enough cefane wanda zai ishe su “kafin yatsaya shago yasiya macaroni da pasta rabin cartons sai shinkafa tiya biyu da kanannun indomie carton daya sai maggi leda leda da spices sauran 15k din tass ya kashe . Sai da ya gyara koi na tsaf yashirya duk abunda yasiyo a muhallinsu inner wears din ma cikin wardrobe yasaka mata perfumes din ma bai fida su a ledan
Chapter 30 · 0% Book details