Sashe 21
Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Babban parlor ne yaji tiles sai bedroom daya da kitchen sai toilet a bedroom din dakuma wani a parlor, parlor babu komai sai karamin carpet a tsakiyar parlor “ babu kura ko kadan wajan tass yake,Tunda ta tsaya bakin kofar dakin bata motsa ba kamar wacce aka dasa,kayan dake hannunshi yasauke tareda saukar da ajiyar zuciya mai karfi ahankali yake tafiya zuwa bedroom din dashi ma kofar shi ke a rufe sake fido key yayi daga aljihun shi ya bude dakin sai dayayi sallama kafin ya shiga , bedroom din dan madaidaici da katifa akasa nan ma akwai carpet da wardrobe like a bangon dakin taga dayace da plain ash curtains a both kofan da tagan, babu bedsheet a katifa sai rigar katifar kawai da pillow kwara biyu, “kallon dakin yake ko kiftawa babu anan kuma rayuwa ta kawo su anan kuma rayuwa ta maido su anan kuma zanan kaddarar su zata cigaba da kudana Yah rabbi ya furta ahankali tare buda kofar ya dawo parlor “idan take tsaye tun shigowar su anan take ta gaji da tsayuwar domin jikinta sam babu kwari amma bata jin zata iya zama sai lumshe idonta datayi ta jinginar da keyarta a bango tana sauke ajiyar zuciya ahankali da gani kasan bata son tsayuwar da take “kallonta yayi cikin few seconds ya dauke idonshi yayi kasa da kanshi tun tahowar su this is the first time data bashi wani irin mugun tausai haka nan yaji yana tausayin ta dagani kasan deep inside she is hurt, bayan dogon nazari dayayi ya fuskance abubuwa dayawa game da ita, Ahankali yake matsawa towards her “cikin wannan muryar tashi but this time can kasa yayi maganar yace ki shigo , bata ce komai bas ai buda idonta datayi tana kallon parlor, duvet din da pillow ya dauka ya juya yasake cewa follow me “ koda suka shiga bedroom din nan ma dakin take kallo ko dauke ido babu “yana lura da duk wani motsin ta bags dinsu ya aje , ya daura duvet din kan katifar da pillow dake hannunshi “ mikewa yayi ya kalleta yace come and have a set “ shiru tayi Kamar bataji shi ba kusan 2mins bai sake magana ba sai can ahankali kamar tana taka garwashi ta zauna kan katifar ahankali tana takure kanta cikin hijabin dake jikinta “ fita yayi ya koma parlor ya jinginar da tabarmar a bango kafin yabude kitchen din yashiga dan karami ne kitchen din babu komai ciki sai camping gas karami da pot a gefe da alama dai mai gidan daya tashi tafiya duk ya barsu. Kusan 1hr tana kwance babu ko alamar bacci a idonta tun dazu take kanannun hawaye takasa jurewa takasa mantawa so take kawai ta mutu domin duniyar ta isheta,knocking yayi ahankali kafin ya tura kofar dakin yashigo kwance take ta ba kofar baya yarda take curewa waje daya yana bashi mamaki kamar bata da k’ashi da sallama yashigo dakin bata amsa ba domin Hankalinta sam baya jikinta kallon bayan nata yake kamar zai gano wani abu a bayan ‘ kusan 3mins yana ahaka ahankali kuma ya matsa kusada da katifar da take kwance ganin bata ji motsin shi ba ko alamar tasan dashigowar sa dakin hakan yasa shi yin gyaran murya “dasauri ta tashi zaune ganin mutun tsaye a kanta idonta yayi raurau alamar zatayi kuka don ta tsorata kallonta yayi ya dauke ido “ yace sannu ya jikinki? Fuskar nan kamar za shi yak’I batace mashi komai bas ai sa bayan hannunta datayi ta goge fuskarta shima bai sake magana ba yabude bag dinshi yafido kudin da abby yabasa 20k ne cif domin baa cikin su yataba kudin mota bay ana son ya fita ya siyo abubuwan amfani amma bai san inda zaije ba hakan yasashi tunani zuwa clinic wajan dr ibrahim duk yace mashi zai shigo da,daddare amma kafin daran sun bukaci wani abun kamar bockets sponge toothpaste da sauran su, har yakai kofa zai fita yajuyo ya kalleta yace stay here don’t out I will not stay long “aydarh batace masa komai ta koma ta kwanta, Dr ibrahim ya kalli malik yace amma ai akwai gas da tukunya a kitchen din ba? Malik ya gyada kai sannan yace masa eh akwai, dr ibrahim yace tau Alhamdulilah yanzu bara lokacin tashina yakarasa sai mu shiga kasuwa mu siyo dan abunda ba’a rasa ba wanda zaku nema right? Malik yace eh hakane ina jiranka tau. Keke suka hau har central market din garin babu nisa Sosai daga clinic zuwa kasuwan cikin few minutes suka karasa, zanin gado suka fara yanka aka dinka musu da four pillows kamar yarda malik din yace babu bata lokaci aka gama suka karba suka wuce, bockets suka siya na wanka kwara biyu sai plate 6 spoon 6 cups ma haka sai knife da container karama daya babba daya sai warmer masu kwara uku kanana masu saukin kudi nan yabiya suka wuce wani shago yasiya soaps detergent da kuma sponges sai toothpaste da Vaseline babba daya sai karami daya, nan malik ya mika kudi “dr ibrahim yakalle shi yaso yayi shiru amma yakasa sai yace ka manta baka siyan ma madam perfume ba koh? Shaf ma ya manta a ranshi yace ka kasan kamshin datakeyi da baza kayi magana ba,baice komai ya koma ya daukar mata wani medium perfume body splash ne bai da karfi sosai yabiya kudin suka kwashe kayan suka fice fira suke ammar abin da kwatan firan dr ibrahim ke yinshi shidai malik daga um sai aa idan kuma abun dariya ne yayi wannan miskilin murmushi nasa “ malik yace please ina zamu samu abinci nasiyan mata? Dr ibrahim ya girgiza yace aaa bara mu fara biyawa gidan sai a karbar mata wajan iya kafin taji sauki tafara girki,malik yace aaa Doctor dawainiyan yayi yawa kuma “ mu dai sami inda ake siyarwa ko da restaurant ne sai muyi takeaway “Dr ibrahim yace na lura har yanzu baka daukeni yarda na dauke bah? Malik yayi kasa da murya yace aaa sam bahaka bane kawai dai naga anyi wahala damu dayawa ne “dr ibrahim yace indai ka daukeni yarda na dauke ka muje mu karbar mata abincin can wajan iyan, keke su ka hau har kofar madaidaicin gidan, sallamar shi sukayi suka kwashe kayan suka shiga gidan dasu dakun ne kwara biyu a jere sai wata rufa da nan ma daki ne sai filin tsakar gida da kitchen da toilet a dakin koi na shafe yake cement anshare gidan kwal,kamshin turaran tsinke da aka kunna a daki har tsakar gidan, da sallama dr ibrahim yasaka kai yashiga rumfar malik na biye dashi baya dauke da ledojin siyayyar dasukayi a hannun sa,daga cikin dakin aka amsar sallamar dare bada izinin shigowa “babbar mace ce zaune kallo tayi saar ummi kallo daya zakayi mata kasan mahaifiyar Doctor ibrahim ce saboda tsananin kama dasukayi dashi cikin ladabi malik ya gaishe ta cike da kamala da fara’a ta amsa bata gane shi ba hakan yasa ta cema dr ibrahim bako mukayi ne? Gyada kai yayi yace eh iya ABDOOLMALIK ne wanda nake baki labarin sa, ohh Allah sarki tasake fadada fara’arta tace Abdul sannu ina gajiya ya mai jikin takara ji? Da sauki alhamdulilah iya,iya tace tau madallah Allah yakara sauki,Ameen suka amsa atare dr ibrahim yace iya ina yaran gidan suke su hadawa ABDOOLMALIK abinci a warmer ,iya tace duk sun tafi wajan biki nan baya bara natashi na hada da kaina bata jira amsar su,ba ta mike “a kula biyu ta hada masu lafiyayan tuwo da miyar danyan kubewa dayasha naman karamin dabba da man shanu sai kamshi yake “ sallama sukayi da iya tareda yi ma malik alkawarin zasu shigo su duba jikin aydarh in sha Allah Sosai yayi mata godiya har cikin ranshi yaji iya kamar umminsa.Saidai ya shirya duk abunda suka siyo a muhallinsa tun can daman yana taya su aysha aiki shiyasa duk wani aikin gida ya iyasu babu abunda yake basa wahala, toilet din dake parlor yashiga yayi wanka” wani cotton yard yasaka black duk da ya kwana biyu amma yayi masifar karban jikinshi kamar wani baindiye,shiga yayi dakin har yanzu bata ci abincin daya zuba mata ,kallonta yayi ya dauke ido bai ce mata komai ba yawuce bathroom din sai dayasa detergent ya wanke bayin duk da babu wani dirty a ciki fitowa yayi tareda komawa kitchen yana tunanin inda zai je ayi mashi refeling gas, yasan bazata iya sakawa jikinta ruwan sanyi ba.kallonshi take ko kiftawa babu gani irin kallon dake mashi yasa bata ranshi yana jan karamin tsaki a ransa har zai gota ta yawuce cike da iyayi tace hey handsome ina zuwa haka? Bai ce mata komai ya wuceta bin shi tayi a baya har yafita kofar gida, Daga murya tayi tace bawan Allah magana fa nake. Malik dai sai wage wage yake yana neman wanda zai tambaya yayi masa kwantancan inda ake siyar da gas, budurwa dake tsaye mai suna ramlah,takasa shiru sai magana take masa wanda ya maida ta da ita da banza duk daya “gajiya yayi da maganar da take masa,ya juya yayi tafiyarsa, dasauri ta like jingin bangon dan karamin gidan nata da parker rike a hannu da alama dai shara ta zubar sai faman sababi take ganin malik yasata likewa jin bango tace “wa’inahu min sulaimanu wa’inahu bismillahil rahamanin rahim,sai gwale ido take tana kallonshi kamar taga mutuwa shi mamaki ma tabasa yatsaya yana kallon ikon Allah,ganin yarda take yasa shi ajiye gas din hannun sa ya matsa kusa da ita, kara shigewa tayi jikin bangon tana rufe idon zuwa yanzu malik yarasa abunyi hakan yasa shi cewa baba lafiya? Har sai daya maimaita sau uku sannan tsohuwar ta bude idonta,tana kallonshi murmushi yayi mata yace ina wuni? Inna dai bata amsa bas ai kankance ido datayi ,malik yace baki da lapia ne baba? Sai sannan ina ta sauke ajiyar zuciya tace ohh ashe daman mutun ne kai ka razana ni hakan nan? Yanzu fa Ko Allah ya isa na banka sai ta bika ahtau wannan abunda kayi man tunda nazo duniya ba ataba firgita ni irin haka ba,malik was confused and speechless at the same time “ ya firgita takuma ta ina?shida ko magana baiyi mata ba and tafiya yakeyi lafiya lau