← Book details Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 197

Sashe 57

Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ai ban sani ba, taware ido tace hala baka duba mirror ne ma? Yace aaa bana dubawa amma indai na kaiki na yarda ni kato ne, tace Wallahi ni am not fat kowa ma yasani aie, malik yace kema bakya kallon mirror, aydarh na kallonsa tace ina kallo manah, yace dubi nan king ani gashi babba yafada yana nuna direction din boobs din ganin inda yake nunawa tayi maza tayi kasa da kanta kafin ta dauki plate din abincin ta mike kaman zata tashi sama ta wuce bedroom har tafara hawaye, malik yabita da kallo har tashige kafin ya girgiza kai yacigaba da cin abincin sa. Yace tau shi malamin ne yace ba daidai bane tace ah’ah shi fa bahaka yace ba cewa yayi nakara daga yarda yabani din waye ya koyamun malik yace sai kika ce waye tau?tayi shiru tana wasa da nails dinta tace cewa nayi kaine yace so nake ki maimaita mun yarda kikace masa tace cewa nayi yayarh na ya koyamun shine yace bani da aure ne?nace ah’ah,malik yace kinyi shiru ki cigaba, tace ce masa fa nayi kaine yace nine wa? Tayi kasa da murya tace mijina malik yayi wani cute smile yana shafa sajansa yace tau ai kinyi kokari Sosai tace Dan Allah fa ?ya girgiza kai yace sure tace nagode kaga gobe Sunday akwai kuma wani littafin zamu bayar goben yace tau bara nadawo masallaci sai muyi tayi shiru kafin tace yau baza kaje wajan kallon kwallon ba? Yace aaaaa shima dr ibrahim din mura yakeyi bazai je ba aydarh tace eyyerh har ya kusa fita kafin tace sir yajuyo yace ma ta rage murya tace yaushe zamuje wajan auntie hibban?malik yace can din mi akeyi? Ta girgiza kai tace babu kawai I wanted to see her,malik yace barana is there turn now ai mune mu kaje last kibari idan sun zo kinganta,batace komai ba ta juya tafita shima yawuce masallaci jin har an tayarda da sallarh, itama daki ta wuce tayi sallarh anan saman prayer mat take bata tashi ba har yadawo,littafin ta dauko suka fara karatun, basu jima suna yi ba, ta haddace ya zauna akanta har mamaki yakeyi idan yana koya mata abun sharp sharp take rikewa, murmushi yayi yace sake yi naji,babu wani mistake ta sake biya karatun dayayi mata kafin yace that’s my gurl ki cigaba da yi har time din dazakiyi bacci zanje na kalli ball din online a waya yanzu tace alright yace sai da safe yace sleep like a new born baby,wani cute smile tayi tace I will, kofan ya rufe ya fita. dasafe ma ruwan tea kawai suk asha sai irish zuwa yanzu tayi noticing baya zuwa aiki tana so ta tambayesa amma bata san abunda zatace masa ba,har bakin gate yarakata yau a kafa sukaje duk da bawani nisa sosai amma sai sannu yake mata yasan bata taba tafiya irin haka ba da kafa, a bakin gate din suka tsaya baya barin tayi late shiyasa time din dasuka iso lokacin sauran students ke ta zuwa “kallonshi take da farin idonta dayasha kajal dake cikin nikkab kafin tace sir wajan aiki zakaje,ya girgiza kai yace no tace tau miyasa? Yace ai mutunmin yayi tafiya batace komai ba tayi shiru kafin yace idan antashi kaman jiya sai nazo mudawo tace alright, har zai tafi sai gasu maman noor da maman baffa,jiya yafara ganin su din da haka bai wani gane su ba hade baki sukayi wajan gaishe sa,ba yabo ba fallasa yace lafiya “yafada yana ce mata sai nadawo ayi karatu yafada yana mata waving hannu shima tayi masa su maman noor baki bude suke kallon su kaman zasu hadiye su tsaban kyau da haduwan dasuka yi tareda da Aydarh su ka shiga class din sit din datafara zama ranar daaka kawo ta shine har yanzu yama zama permanent sit dinta ita kawai ke zama front sit din , maman noor ta zauna a sit dinsu tana kallon maman baffa tace Wallahi fa lamarin yafara firgitani maman baffa tace mi kawata? Maman noor tac eke mutanan nan fa ba kananan masu kudi bane Wallahi Maman baffa ta sauke ajiyan zuciya tace gashi duk irin bugun cikin da zamuyi ma yarinyarta can bata bamu amsa “ ni fa abun nan na daure mun kai kiji haduwan mijinta fa Kamar irin bai saba da rana ba kullun rayuwarsa cikin a,c yake kuma sau dayawa a keke fa zuwa balle nace ko yanada mota Wallahi bashi da mota,maman baffa tace ai shine kawata kodai tun tabayin kudi suka talauce ne? Maman noor tace aaaaa gaskia ke kam baki da id oki duba fa har yanzu skin dinsu na nuna alaman kudi da hutu bugu da kari wani irin nutsuwa kamewa da kuma aji, ki dubi fa flat shoe din datake sakawa na islamiya ma ta mayarda su naga kullun dasu take zuwa kunsan 38k fa suke, kuma ma a kanon nan bazaki samesa ba sai dai kiyi order lagos kuma ki sake bata kudin shipping ga kudin shipping yafi na products din,’maman baffa tace eh fa kawata yanzu ta miye abun yi maman noor tace Allah kabashe maman baffa tace Ameen Ameen, sun dai kasa dauke ido kanta sai faman kallonta suke ,itace ta farko wajan bayarda da hadda,malamin yace kinyi kokari malama Aseeya a sake dagawe ALLAH YAYI albarka tace Ameen , line by line aka bi har yagama karba kafin ya koya saboda lokacin tashi daya gabato Kamar kullun ma yau tun anan ta iya larabcin hausan shine ke fassara mata shi. Yau ma kaman kullun tun kafin lokacin tashi yayi yakara so anan office din headmaster yazauna har sha biyun yakarasa,bakin gate ya koma ya tsaya kasan wani bishiya yana jiran ta,tare da su maman noor suka fito sai faman labarin da ba kai ba kugu suke hadda cewa ai zasu zo gidanta ita dai aydarh batace komai bat ace Allah yakawo ku lafiya can ta hangosa kanshi kasa yana taba wayarsa,ahankali tace masu maman noor sai anjima “maman baffa ta washe baki tace yar gata ai shi can na hango ohhni bazai ma iya bari ki koma da kanki ba tsaban soyayya, maman noor tace kedai bari kawata amma ki jira nan da anfara yara duk sai abun yaja ba,ita dai batace musu komai batayi gaba tana amsa bankwanan dasuke mata sai kuma next week, tana karasowa gabansa ta dauke nikkab din duk tayi sweat a forehead handkerchief yafido daga aljihunsa yana goge mata kadan kadan tareda hura mata iskan bakin sa,lumshe ido tayi sosai take jin kunya saboda har yanzu baa karasa watsewa ba a bakin gate din dasauran few students wanda cikin su hadda su Maman noor waenda daman ladan su anan suke zubar da rabi da quarter saboda sai an tsaya gulma kafin a tafiya,yarda ta lumshe idon lashes dinta “kaman irin an kara sun kwanta sosai yarda shape din idonta yake yana tafiya da imaninsa kusan 3mins suna ahaka kafin ya dauke,itama ta bude ido tana sukunyan da kanta kasa, keke ya tarar musu sai dasuka tsaya yasiya few ingredients din dabasu dashi kafin suka wuce gida, a kofan part dinsu suka tarar da rabiah zaune hannunta rike da warmer tasha wani shadda duk yaji ruwa ga ubansu dauri da calaban attach blue da green tayi kaman irin karuwan nan,tana taunar chewing gum “ Aydarh ta tsaya tareda kare mata kallo,ledan dake hannunta ta mika masa “kaman wani yaronta haka yasa hannu ya karba, cikin wani irin tone, tace you are stupid and you most be stupid ma,I thinks I have passed this to you time without numbers you should start out of him, and you refused ta dawo daidai side dinta tana kallonta cike da raini kaman taka abun kyama tace , idan kina neman sa kibari yafita kar na kara ganin waennan kafan naki a apartment din nan “Ramlah ta dankaro wani uban zagi ta maka wa Aydarh,duk zagin da hausan yayi girma amma ba karamin ciwo abun yayi mata “cikin wani Irin voice kaman Asad (na cikin auran ajiya) ya kira sunanta ranshi yayi masifan baci ba Ramlah ba hatta Aydarh sai da gabanta yawani fadi ganin yarda cikin few seconds yakoma haka kaman lion, idonsa har wani wuta wuta yake alaman ran maza ya baci ( Nagode mijin ASSEIYERH ) yace how dare you! Do you know who is she ?kinsan abunda kikayi yanzu kam,idan baki bar gurinan ba I can remove out the stupidity out of your head “Wallahi Ramlah har kyammar take ta gudu ta kwashe warmer dinta ta fice ya kalli aydarh kafin yasa hannu zai riko nata hannu ta kwashe tayi baya tareda fashewa dawani kuka cike da shagwaba, har wani Jan lumfashi take alaman ranta ya baci, kaman zai yi hauka haka yakara matsowa kusa da ita tasake zillewa,ahaka Allah yabashi daman ya cafko ta yariketa gam kafin yasa key yabude kofan suka shiga ya rufe anan ya ajiye abubuwan hannunsa still kukan take wanda yake jin sa har cikin ransa, bag dinta yasa hannu yacire kafin yakarasa cire nikkab din, hannunsa yasa ya kwashe hijab din, yau batasa hula bas ai hadddan gashin kanta nan tayi parking can keya tare mashi wani style a ribbon, camisole din uniform din ce jikinta sai black lace foam bra dake jikinta wuyan ba babba babe shiyasa baka iya hango bra din said ai hannunta ,ta shoulder dinta kama ta yayi suka zauna, Still kuka take tak’I yarda su hadda ido,shi bai masan abunda zai ce mata ba can yace kiyi shiru bana son kuka, batayi shiru ba ta cigaba,yasake cewa kije kiyi wanka ki fito muyi girki nan ma batace komai ba shima shiru yayi yana kallonta can yace mi kike so kuma?sai sannnan tayi magana kaman wata yarinya tace to ni sai karama mun “yarda tayi maganan yasa shi jikin zaiyi loosing control daf ya daurata kan laps dinsa yace mi zan rama maki? Ta tasake fashe masa dawani kukan tace hala bakaji ta zageni ba? Malik da hannunsa ke kan shoulder din bayan yagama jin ta yace shknn abunda kike so? Ta gyada masa kai yace tau shknn anjima idan nafita sai na rama maki,tayi sauri rike hannunsa dayake mata tafiya dashi a shoulder tace saidai mutafi tare ka rama mun
Chapter 57 · 0% Book details