← Book details Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 197

Sashe 31

Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

su ba yabar su, kitchen yawuce ya daura jallof din pasta da kifin da yasiyo sai daya gama kafin ya daura mata ruwan wanka sannan ya zuba pasta a plate wanda favorite dinsace ya zuba sauran a warmer, yaci ya shiga yayi wanka ya gaji bacci yake son yi dan akwai nepa sai daya juye mata ruwan zafin a sabon flask din dasuka siyo ya kai mata bedroom kafin ya dan kwanta. Inna tashirya ta dauki mayafinta da jikka,tasaka sabin takalmin da malik yakawo mata tace tau ni natafi asiya nasan kafin na dawo kun tafi gida in sha Allah gobe na shigo, aydarh tace to inna dr hafsa takalli inna tace tau hala idan kikaje wajan suna can zaki zauna?inna tace ina ruwanki nifa bana so shishigi da neman wajan zama dana tashi fita na kinga nayi magana dake baiwar Allah?dr hafsa tace Allah yabaki hakuri sai kin dawo na daura maki girkin ne kafin ki dawo?inna bata tanka ta ba tasa kai ta fice,dr hafsa tayi murmushi ta kalli aydarh tace haka nake fama da ita amma kullum cikin cewa take hakurin zama nake da ita,aydarh tayi murmushi tace she is really funny,dr hafsa tace ai ina tunanin mijinki ne kawai ke iya zama da ita shima kuma dan dai Allah yasa tanaji dashi ne aydarh batace komai ba dr hafsat ace mu fara ko? Aydarh ta gyada kai tacire hijab da dankwallin kanta tana warware uban tulin gashinta daga cikin ribbon dr hafsa ta dinga bin gashin da kallo tace masha Allah shiyasa bakya son kitso, aydarh tayi raurau da ido damuwa kan fuskanta tace akwai zafi hannunki ko?bakaramin dariya aydarh taba dr hafsa ba yarda tayi maganar kamar wata yarinya she always behaves childish dr hafsa tace no ai calaba bai da zafi ko kadan yallabai ma dan bai iya bane da ko shi ai sai yayi maki calaba aydarh bata fahimci abunda dr hafsa tace ba shiyasa tayi shiru, cikin few minutes aka fara tsagan calaba aydarh dai hadda kanannun kwallan ta a ido tasa bayan hannu tashare su,saboda dariyar da dr hafsa ke mata,dr tace nikam dai aydarh naso naga ranar haihuwanki ai wannan sai Doctors din Nigeria sun taro a kanki,kice hakanan ma yallaban ya matsu a samu cikin ashe matar tasa ragowa ce, aydarh batasan time din datace shi ne yace haka? Dr hafsa da har yanzu da sauran dariya a fuskarta tace eh cewa yayi nayi maki p-test ashe ashe ba jaruma bace matar tasa,aydarh batace komai a ranta take tunanin time din daba ta da lapia kenan hadda abunda yasa akayi mata kenan?babu mai bata amsa yasata yin shiru tana cigaba sauraron labarin da dr hafsa ke bata,dr hafsa tace wallahi aydarh wasu matan auran sai ahankali aydarh tayi murmushi dr hafsa ta cigaba dacewa wata friend din ace fa suka rabu da mijin kuma fa laifinta ne shiyasa yanzu duk ta zauna labarin sa takeyi,aydarh dai na sauraron dr hafsa tana fahimta labarin amma batasan ma’anar labarin ba dr hafsa tace kiji fa a zamanin nan wane namiji ne zai dauke ma shara wanke wanke girki ke hadda fa wankin bayi da kayan sawa,kiji fa ai wallahi indai ba shanye shi tayi ba babu namijin da zai maka irin wannan a yanzu,aydarh dai tayi shiru aranta take juya maganar dr hafsa din yanzu ita malik dakeyi mata duk wannan itama shanyesa tayi tau miye shanye war?sai kuma wata zuciya tace mata aa ai auranku bakalar na kowa bane,dr hafsa tace tau the worst part of it ma abunda yasa har maganar divorcé yashigo ciki fita take bata tambaye sa ba shikuma yaji bazai iya ba,aydarh tayi shiru kafin tace auntie hafsa minene shanyewan? Dr hafsa tayi murmushi tace eh gaskia ke ba lalle bane ki sani idan aka ce mace. Aydarh dai tayi shiru sai sauraron bayanin da dr hafsa ke mata take, batace komai ba har sai da dr hafsa tayi shiru kafin tace,idan matar ke yin komai fa?shine mijin ya shanye ta dr hafsa tayi wani irin dariya tace wallahi ke ma aydarh tau a normality na alada da addinin musulunci shi ya daurawa mace wannan nauyin na girki shara wanke wanke kula da yara a gida shi kuma mijin ya tafi office Ko wajan sanaar shi yafita ya nemo maku abunda zaku ci da duk wani abubuwa na yau da kullun,aydarh ta sauke wani irin ajiyan zuciya,tau ita miye matsayin auran su da malik shima ai aure tunda tasan aure dole sai da sadaki kuma aie aure aure ne,sai kuma wata zuciya tace mata aaa aurenki dashi ba kalar na kowa bane, bakya sonsa ko kadan sai ma tsoronsa da haushin sa dakike ji shima bakya sonki wannan ai ba aure bane,ta tura baki ahankali can ciki tace Mugu kawai,tunanin ne fal aranta so take dai tasan miye matsayin auran su da malik miye kuma sharudan auran da dr hafsa tace duk macan da bata cika su ba makoman ta wutan jahanama,bakaramin tsoron wuta take ba tun tana yarinya tana iya tuna time din rufaidarh ke gaya mata zafin wutar duniya ba komai bane kan lahira 1%din wutar lahira ne,wani irin yankewa gabanta yayi ya fadi batasan ta yarda zata fara tambayar dr hafsa ba shiyasa tayi shiru,wani irin kyau calaban keyi ba fatar kan fari tass yarda take fitan da tsagan kamar sai tasaka ruler tayi ta daidaita ita kanta dr hafsa duk zaman ta boarding bata taba sanin ta iya calaba ba kamar yau datayi wa aydarh masha Allah, yi ake yi ake amma gashin kamar ana kara masa yawa,duk da manyace akeyi, tun dasukayi magana da dr hafsa take ta juya zancan a ranta so take ta tambayi dr hafsa amma batasan ta yarda zata tambaye ta ba “can wani dabara ya fado mata a rai,tayi kasa da murya kafin tace auntie sai kuma tayi shiru ganin haka yasa dr hafsa cewa ina jinki aydarh,ajiyar zuciya ta sauki kafin cikin nutsuwa tace daman auntie a can akwai wata friend dina ita da mijinta basa son juna kwata kwata sun tsani juna ko magana ma basa yi kuma duk wani aikin gida shi keyi komai fa har ruwan zafi shi ke dafa mata tayi wanka,idan kinga sunyi magana sai idan batada lapia kawai fa, dr hafsa tace subhanallah amma gaskia wannan bata son ciwon kanta ba wait ba ma wannan miyasa sukayi aure while basa son juna?aydarh ta ware hannu tace nima ban sani ba kawai dai a daura ma su aure babu biki babu komai kawai anan take aka biya sadakin akayi komai a gabansu, dr hafsa tace duk da haka bata da wayo dai ai aure aure ne duk da bata son shi ai aljannarta nakasan kafar sa,kuma aure dole mata tayiwa miji biyayya ko da bata sonsa kinga shi ko da baya sonta alama ya nuna cewa yana tausanta kuma ya rike amanar Allah ita kuma ranar gobe kiyama sai Allah yakamata da laifi,aydarh naji duk abunda dr hafsa ke fada tayi shiru tana tunani tau ita ya zatayi? Har ga Allah bata son ma abunda zai dinga haddata da malik sam,dr hafsa tace tau kuma shi bayan haka baya siya mata komai?aydarh ta girgiza kai tace he is trying his best ya mata abubuwa ,dr hafsa tace kingani ba that’s means shi yasan hakkin aure kenan yasan miye aure ,ita kuma da bata da hankali saboda bata son sa kuma bata neman rahamar ubangiji ai ni atunani duk wani rashin kauna yakare daga ranar da aka daura ma aure da mutun,ba kamar idan yana kyautata maka kamar yarda wannan mijin kawar taki keyi mata shikenan rashin so ya kare ko da bata sonsa tayi hakuri ta dinga sauke hakkin aure yarda ta hakura har tayi biyayyan iyaye haka ya dace ta hakura tayi biyayyan Allah tasauke hakkin mijinta a kanta ta sauke hakkin gidan auranta,ta sauke ajiyar tace tau auntie ita fa batasan komai na aure ba tace,dr hafsa ta saki calaban datakeyi yanzu ta zagayo ta kalli fuskar aydarh tace daman akwai macan da batasan miye zaman aure ba aydarh? Aydarh da gabanta keta bugawa tace nima dai bansani ba amma haka tace batasan komai na aure ba dr hafsa ta dinga salati tace tau bata da yan uwa ke bata da mahaifiya ma forst? Aydarh ta girgiza kai tace bata da yan uwa tanada mahaifiya,dr hafsa tace tau miyasa ba a fada mata ba?aydarh tace itace bata tsayawa ta saurara kullun bata zama inda kowa yake idan ta tafi school shikenan wani time enma har sai tadawo nan kasar sannan zatayi magana dawani,dr hafsa tace gaskia kam ta cuce rayuwarta bata kyauta ma kanta ba kuma duk mai daure mata kugu tayi wannan abun shima ya cuce ta,ta tubar ma Allah ta fara shirin koyon rayuwa saboda batasan komai ba,aydarh tasauke ajiyar zuciya har zatayi magana sai kuma tayi shiru,can dr hafsa tace yawa mu’amalar aure fa? Aydarh bata gane tambayar da dr hafsa tayi mata bah akan yasata cewa na’am? Tace kina nufin wani abu bai taba shiga tsakanin su ba like sex or something like that?aydarh tawani zaro ido ta daga kanta tana kallon dr hafsa sai kuma tayi maza ta saukar da kanta kafin ta girgiza kai tana wasa da hannunta tace aaa dr hafsa ta rafka salati tace yau mun shiga uku ke yanzu a matsayinki na kawarta kuma ke kinada aure kinsan komai na aure zaki barta tana wannan rashin hankalin da wannan ai hauka ne , aydarh tace ranar ne ma tana shafa yazo yaganta da towel shine fa ta dinga kuka,dr hafsa da bakinciki ya cikata tace tau Allah ya kyauta amma tanaji tana gan isai ya auro wata,ko gwal ce ita ai sai haka wallahi kuma ranar lahira sai Allah yakamata red handed tunda ita shashasha ce wawiya har ga Allah dr hafsa bata kawo aydarh bace tayi tunanin kawar ta tace dagasken,Aydarh dai bata kara magana ba jikinta duk yayi sanyi tau ita yazatayi kenan babu abunda yafi firgita ta irin wutar dazaa sata kamar yarda dr hafsa din tace, gabanta sai faduwa yake tayi lamo dr hafsa ta cigaba da mata calaban babu wanda yasake magana cikin su aydarh hankalin ta baki daya ya koma kan maganar dasukayi
Chapter 31 · 0% Book details