← Book details Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 197

Sashe 25

Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

wanke kwan ya saka kafin ya yanka tomotoes din da albassan kanana yarda yaga ummi nayi idan anyi dan wake tass ya hada komai kafin ya zubawa aydarh a plate ya bare kwai kwara uku ya zuba mata a nata plate din,zaune take kan carpet, kallonta yayi ya dauke ido kafin ya aje mata plate din agabanta bata dago ba kanta nakasa amma taga abunda ke cikin plate din, this time ma kamar dazu ledan drugs dinta ya kawo mata kafin yaje kitchen ya dauko mata ruwa . Inna tace oyoyo ga audu ga audu ga audu maraba, ganin har angama la’asar baka shigo ba nayi tunanin ma baka zuwan,malik yace aaa zan shigo daman barin nayi yamma tayi kafin nazo, daki tashiga ta sai gata da jug da cup a hannu fura ce ciki mai kyau tasha Nono sai kamshin kayan yaji ke tashi ta zuba masa a cup tace gashi kasha daman kai na dama ma ita,karba malik yayi yabi furar da kallo yace nagode kwarai inna, da sallama dr hafsa tashigo cikin shigarta tsaf da lab coat sai jikkarta da wayanta a hannu masa mata malik yayi inna ta tsaya tana kallonta ko kiftawa babu, sai ta dauke kai,dr hafsa tayi murmushi daman dr ibrahim yabata labarin komai itama kanta ba karamin mamaki tayi ba jin wai har inna taraka malik din siyan gas,tace yallabai ashe dai anguwarmu daya,ina wuni ya mai jikin?shima malik dan sakin fuskar sa yayi yace Alhamdulilah Doctor,inna tace wacece wannan kuma, sai kuma tayi kasa da murya tace ina kasan wannan kuma?ita fa haka take a duniya burinta taga nasan wani itama tace tasan shi,malik yayi murmushi yace a asibitin su aka kwantar da mai dakina,inna tace ohh ,sai kuma ta kalli Doctor hafsa da ta daure fuska tace nan dakika tsaya kamar wata yar sanda bazaki shigo ba komi? Doctor hafsa batace komai ba tawuce tashiga daki “inna tasake kasa da murya tace itace nake gaya maka dazu nidai ba ruwana jikata ce diyar babban dana ce daya rasu,nake riko Malik yace Allahu akbar Allah yayi masa rahama inna tace Amin, babu ruwanka da ita rashin mutunci wanda ta mance ne kawai ke bata mun ga girman kai,kaii hakuri nake kawai billahi amma daya yanzu na kai kaina gidan marayu na bar mata nan din, malik yayi murmushi yace bazaayi haka ba ai. Inna tace yanzu fa nan da ta shiga kafin ta fito sai wani iko daga Allah, malik yace hutawa take kinsan gajiyar aiki “inna ta bi malik da kallo kafin ta kalli kofan dakin dr hafsa tace tau mutun idan iko da sarauta yake ji ai sai yatafi can gidan sa yayi “Amma babu katuwar da ta isa ta dinga man mulki a gida “malik dai yayi shiru yana sauraron inna,mikewa tsaye tayi tashiga daki,can sai gata ta fito hannunta rike da kula da kuma jug “tayi kasa da murya tace bara nashiga na kai mata abinci saboda idan bani na kai mata ba saidai fa yunwa ta kashe ta wallahi bazata fito ta dauka ba,malik dai nata kallon drama inna, inna ta kalli dr hafsa tace nasan daman dawuri zaki taso shiyasa nace bara nayi kokarin gama girkin da wuri ita dai dr hafsa bata kalli inna ba ta cigaba da linke lab coat dinta, inna tayi kasa da murya ta kalli kofa tace wai zararra ce ni ko mi ina magana kinyi shiru kin maidani kamar wata yar iska dai, dr hafsa tace wai ba naga bak’o gareki ba? Ki fita ki same sa manah abinci ne dai kin kawo kuma nagode, sai nafara yin wanka kafin,inna ta tsuke bakin ta tace tau Allah yabaki hakuri bara na fita kafin ki zage ni kuma”,tana fitowa tace yawa daman ai na gaya maka nice daidai da ita, malik yace ayi hakuri dai ni bara na koma naga magrib ta kusa, inna ta washe baki tace tau ba laifi ka gaishe da mai dakin naka nima nasamu lokaci sai nashigo na dubata, har kofar gidan inna ta rako sa labari kau kamar kar yatafi inna takasa shiru. 6:00pm daidai yashigo gidan ,Ramlah na zaune a ventilation dinsu ita da mahaifiyar ta sai dayar matar part din fadila da yaranta biyu maza da mata, su biyar ne wurin amma kamar mutun dari fada suke sosai kan Ramlah ta bige yaron fadila musa aiken sa tayi bai je ba tayi magana yace bazaije aiken karuwa ba,ta dakesa uwarsa tace bazata yarda ba ai gaskia ya fada, shine suke faman wannan masifar, ko kallon su bai yi ba yayi wucewar shi part dinsa, dawani irin mayyan kallo Ramlah ta bisa ta mance ma shaf da abunda sukeyi, har sai daya shige building din part dinsa ta daina hango shi domin an zagaye ma kowa ventilation dinsa, fadila tayi gyaran murya tace haka fa aka yi, Ramlah ta maka mata wata wani shegen harara tace tau uban miye yayi ruwanki da ni?maman Ramlah tace duk ba wannan ba kuyi shiru, tayi kasa da murya tace ma fadila “ shin fadila kinga abunda nake gani kam? Fadila data saki baki tana kallon maman Ramlah tace nagani tun jiya abun ke ci na hakuri nayi kawai banyi magana ba wallahi, maman Ramlah tace tau wai balarabe ne ko mi wannan din? Fadila tace wallahi tun jiya dana ganshi nake tambayar kai na tau baki nan shiyasa na ja bakina nayi shiru (kamar basu bane ke fada yanzu) Ramlah ta tabe baki tace ba fa balarabe bane kawai dai haka yake, maman Ramlah tace ki bari baban musa yadawo kila ma ji magana daga wurin shi,fadila tace in sha Allahu saidai idan basu hadu dashi ba amma nasan sai ya tambaye shi wayeshi,kin fa san halin sabo, Ramlah tace ku kwantar da hankalin ku zan binciko maku komai ni fa ai naga miji wurin nan, fadila ta tabe baki tace ko makaho yasan wutsiyar ragumi tayi nesa da wuyan zakara “ maman Ramlah tace aa fadila mi kike nufi?fadila tace babu komai bara na tafi kafin sabo ya shigo, Sai daya fara shiga kitchen ya daura ruwan zafi kafin ya fito knocking yayi saboda ya taba kofar yaji ta a rufe, sai dayayi almost 8mins atsaye yana knocking kafin a bude kofar ahankali ta bude masa kofar ta juya ciki, bin ta yayi da kallo ganin abunda tayi masa a rayuwa baya son raini ya tsani rashin kunya,bai ce mata komai ba itama hakan ko kallon sa batayi ba kanta na kasa tana wasa da Expensive diamond ring din hannunta,plates din daya kawo mata abinci yabi da kallo ba laifi taci sosai saidai ga yajin nan gefe guda da alama bata son yaji dan bata ma taba shi ba saidai star din kawai eggs din kuma daya kawai tace ga sauran two din nan danwaken ma gashi nan ledan maganin ta ya dauka yanzu ma tasha daga yau ya kare daman na 3days ne kawai, kallonta yake ko kiftawa babu so yake ta dago idonta yayi mata concrete warning kan rashin sallama amma tak’I baya jin kuma sai iya yi mata magana tayi shiru ta kyale sa saboda ko saar maryam auta bata wuce ba bazaiyi tolerating shits ba, bai ce komai ba ya kwashe plate din ya fita dasu da harara ta bi bayansa a ranta tayi karamin tsaki , kwanciya tayi ta rufe idonta daman can bata saba zama cikin mutane ba ,shiyasa bata jin kadaici ‘Ko a gida sai ta wuni bata fito ba,a can school Cyprus daman idan ba lectures zatayi attending ba bata fita daga campus dinta, her life is always private bata da friends bata jin magana ya hada ta ko sau uku ne dawani a school din tun zuwan ta duk da yanda school din yake akwai yara masu yawa yaran masu hali ne,amma bata gani akwai wanda zata iya zama dashi balle har a kai da wani abu wai friendship.sai da ruwan yatafasa kafin ya dauko bucket ya juye mata, this time ma bata amsa sallaman shi ba, bai ce komai basai da ya kai ruwan toilet yafito ya zuba mata ido mistakenly ta bude idonta suka hada ido dashi wani irin fadi gabanta yayi tayi maza ta saukar da kanta kasa, ya kafe ta da waennan idon nashi , cikin tsare gida da muryan nan tasa babu alamun wasa yace “baki iya amsa sallama ba hala ? Sai taji wani iri da tambayar tasa abun yazo mata wani kala,shiru tayi batace komai ba, yace “daga yau kar nasake sallama naji kinyi shiru “ bai jira amsarta ba yayi ficewar sa daga dakin, sai time din ta dago kanta idonta cike da kwalla , umarni yake bata kenan? Ita yake ba umarni ? Saboda yaga bata da kowa sai shi babu inda zata je sai wajan shi? Who is he? Mi yake daukar kanshi? Mi ma yake nufi da ita ne wai? Tayi ma kanta tambaya kusan goma amma bata da amsar ko daya,hawayen ta tasa bayan hannu ta share tass tayi ma kanta alkawarin baza ta sake takura kanta ba ko daura ma kanta damuwa,kuma shima bai isa ya daura mata damuwa ba ko ya juya ta,idan girman kai yake ji dashi ta fisa idan izzgili yake ji dashi ta fisa, hararar datayi ma kofan dakin sai ka rantse da Allah malik ne tsaye a gabanta, toilet ta shiga nan taga bucket din ruwan zafin da ya ajiye mata, kallon bucket din take ko kiftawa babu ita yakawo ma wa kenan? Tunda taga shi baya using da wannan toilet din,tsaki ta saki kafin ta fito cikin dakin ta cire kayanta ta dauki towel ta daura, Sai da tayi wanka tsarki dan tagama period kafin tayi wanka ta fito, kamar dazu yanzu ma Vaseline da tashafa da perfume din abayar ta mayar ta koma ta kwanta. Daga masallaci daya fito garin dinke yake da hadari tunanin abunda zai yi masu na dinner yake mai awaran daya gani a gefen gidan su kawai ya yanke shawaran siyan masu,sallama yayi yarinya ta amsa wurin a share yake tass da alama awaran na da tsafta na 500h yasiyan musu ya wuce. Kofar dakin ya tura this Time bata saka key ba sallama yayi yaji shiru bata amsa ba,karasa shiga dakin
Chapter 25 · 0% Book details