Sashe 78
Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yana cigaba da shafasu jin ana taba jikinta yasata bude ido,tana kallonsa dasauri ta maida idonta ta rufe, tana turo baki murmushi yayi baice komai ba ya dauki singlet dinsa yana sakawa, jin yabude kofa yasata bude ido tana kallonsa har yafita baki daya bata dauke idonta ba ta dinga kallon kofan kaman zata fiddo shi daga ciki ahankali ta maida idonta ta rufe moment dinsu na jiya nadawo mata fresh akai wani yarr taji tasake datse idonta da karfi wani irin kunya take ji idan ta tuno yanda ta dinga supporting dinsa yana taba mata jiki, jikinta duk yayi weak daurewa ta ta dauki flask tahada ruwan ko zataji dadi a jikinta,time din daya shigo saka kaya bai ganta ba sai saukan ruwa dayaji a toilet jallabiya yasaka sharp sharp jin anfara salla yawuce masallaci. Yana lura da ita tun da gari ya waye “taki hada ido dashi duk yanda zaiyi ta kallesa takiya shi fa kunyar yarinyar har mamaki take basa ga wani saka hijab datayi tun salla asuba bata cire bas hi dariya ma take basa Wallahi,bayan sungama gyaran gidan as usual ‘suka shiga kitchen hada breakfast, knocking akayi har ta fita zata bude yace come back zan bude “bude kofan yayi yaga inna tsaye tasha mayafi ga wata katuwar jikka kaman wacce zata saka mutun a ciki murmushi yayi yashafa kansa yace sannu da zuwa hajiya inna “inna tace aaaaa tsaya audu ba maganar wani sannu da zuwa ba ashe duk abun nan kana kano matar tahana ka zuwa wajena?malik yayi shiru yana kallon inna kafin tasa kai ta shigo tabar sa tsaye kofan ya rufu kafin shima yadawo parlor yazauna kusa da ita tayi mitsi mitsi da ido tace tau da dai nayi tunani kana tsoron Allah shiyasa ma kaga ina shiga harkan ka amma yanzu na fahimce babu Allah a ranka kwata kwata lamarinka ba gaskiya ahh “malik yayi murmushi yace yanzu dai yaushe kika dawo?inna tayi wani iri da fuska kafin tace tau kuma wani dogon munahukin ne yagaya maka bana nan,tana fadan haka yasan da dr hafsa take,murmushi kawai yayi yace ai naje gidan bakya nan fa”tun shigowan inna taji muryan ta karasa bare cubes din kafin ta wanke hannunta ta fito murmushi tayi looking very good,a hijab din tace oyoyo ga inna “nayi missing dinki inna beyond your imagination “inna dake kallon aydarh baki bude tace nifa bana son firitanden “Aydarh dai cannot hold it but to laugh jin yanda inna tayi pronouncing pretending “ inna ta daure fuska tana kallon malik tace kadai audu kaji tsoron Allah nifa yanzu lamarinka tsoro yake bani “sai yanzu nafahinci abunda ke hanaka fitar”yoo Allah na tuba ba dole ka zauna gida ba ahh tau ai dole ma kau ka dubi yarda yarinyar ke kara wani haske kaman dai tana mai barakallahu giba ma take “sai kuma tayi kasa da murya tace tau wai mi take ci haka “naga kai duk kayi tsawo ma ka fada,malik yayi murmushi yana daga murya yarda aydarh zata ji yace inna ki tambaye ta “ aydarh dai ta zauna kusa da inna kanta kasa tace inna sannu da zuwa ina wuni?inna tace lahiya lau asiya “ashe kuna kano?aydarh tayi murmushi tace erh inna aie muna zuwa bakya nan inna tace haram haramun kar kuyi man sharri,kauye fa naje sai jiya nadawo tau yaushe ma har kuka zo bana nan ni banda kuma dai kun zama irin waccan matar ‘malik yace kinga inna ita fa dr hafsa ba ruwanta ba ita ta gaya mun ba dakaina naje na tarar da gidan a rufe “inna tace wacece kuma haka?malik dai yayi shiru bai sake magana yaga yau innar halin take ji aydarh dai ta mike tashiga kitchen ta sauke noodles din dasuka dafa da boiled eggs kwara uku, a warmer ta juye kafin ta dauko wani clean bowl bayan ta bare eggs din ta saka plate ta dauko kwara uku, da fork tafara kawo wa parlor kafin ta koma ta kwaso sauran ta hado da flask sai cup biyu da kayan shayi ‘inna dai tasaki sai surutu take shima malik din yabiye ta indai kana son kaji surutun sa tau su hadu da inna serve inna tafara yi ta daura mata two eggs kafin ta zuba ruwan Lipton a cup ta hada mata tea ta mika mata gabanta inna ta bi abincin da kallo kafin ta rage murya tace wannan ma sai ace shi yakawo ni da safen nan,malik yace waye zai fada?tace mutanan anguwar nan tunda duk ba Allah a lamarin su malik yayi murmushi yace muyi breakfast inna babu ruwanki dasu, aydarh dai tayi murmushi kafin tacigaba da serving malik murya can kasa tace nahada maka tea?yagyada mata kai tea din tahada masa kafin tasaka indomie kadan a plate ya dinga kallonta kafin yayi kasa da murya yace bazaki sha tea din bak e ?kai kawai ta gyada masa ya cigaba da break din inna dai tayi shiru sai cin noodles dinta take tana hadawa da shayin “can inna tagama tace tau Alhamdulilah “bara kaga daman cewa nayi bara nazo na duba ku, can kurna zani dubiya “malik yace tau muje sai na rakaki ki hau keke inna tace da dai ka barshi naga wannan matar baso take kana fita ba aydarh tayi saurin yin kasa da kai tace lah inna nifa babu ruwana kuyi tafiyan ku “inna tace tau sai anjima har bakin kofan parlor aydarh tarakata kafin tadawo inna da malik suka fita,har suka samu keke har tashiga inna batayi shiru ba, malik yabiya mai keken kudin inna nayi masa godiya, ya juya yawuce “cikin gida har yanzu bata gama cin indomie ba ya dinga kallonta ko dauke ido babu kafin ya zauna yace hala sai na fara miki dura a gidan nan tana turo baki tace zan ci fa yace tau in the next five minutes ki gama cinye noodles din nan. Malik yace zance nake rakasa,aydarh ta dinga kallonsa tace tau ita auntie hibban fa?malik yaware hannu yace nima dai bansani ba, tace uhm “malik yayi murmushi yace sai mun dawo “Aydarh tamike ta bisa baya tace karku je please yace tau shknn kinga ma envelope na dauka café zanje ma aydarh tayi murmushi tace don’t stay long please yace in sha Allah kafin tace sai kadawo yace Alright dear bye yayi mata waving hannu itama tayi masa kafin ya wuce, Yau ma kaman jiya a parlor suka zauna can sai ga dr usama yafito yauma side hug yabasu “ dr usama nasake gyara gilashin idonsa,ya karbi envelope din dake hannun malik kafin ya bude ya dinga kallon result din malik din yayi loosing words ma bai san abunda ma zai fada ba kan result din kana dawani result din amma kana zama ba aiki,shi ke basa mamaki maida result din yayi yarufe kafin ahankali yakalli malik yace congratulations son this is the first time dana ga irin wannan result din in suchs course kasan for how long muke neman irin masu course dinka?malik ya girgiza kai dr usama yace almost 5yrs back sai yanzu Allah yayi nasameka, what about your parents son? Malik yayi shiru kafin cikin ladabi yace there are all alive there are in adamawa state “dr usama yace masha Allah are you married or you are still single? Malik yashafa kansa yace inada aure sir? Dr usama yayi dariya yace nasani aie handsome guy kaman matan Nigeria baza su barka ba “dr ibrahim yayi murmushi yana kallon malik dr usama yace end of this month zan koma congratulations you are employed in the federal hospital of Washington in United state of America without any interview “ malik tunda ga kafansa har kansa yaji wani irin abu ya tsarga masa lumshe ido yayi don Wallahi yayi mutun zaune he didn’t even know what to say dakyar ya fizgo tasbihi yafara yi kafin yakalli gabas ya sako kasa yayi sujjad yama rasa irin addua da godiyan da zai ma Allah daga dr ibrahim har dr usama kallonsa suke dukkan su da murmushi a fuskan su komawa yayi yazauna kan cushion still idonsa a rufe bayanson bude ido ganin yake kaman all this is a dream kaman ba reality bane “wani irin kwalla yaji ya taru a idonsa he wished abby is present here he wished a gaban abby da ummi komai yafaru a yanzu ahankali yasa hannu yagoge kwallan sa kafin yabude idonshi da har sunyi jaa “yace am speechless sir “I didn’t have any words to say “Allah yasaka maka da gidan aljanna Allah yabiya maka duk wani bukata naka na alkhairi I appreciate sir “kafin yamike yakama hannu dr ibrahim dake kallonsa very emotionally yace ibrahim bansan mi zance maka ba amma “dr ibrahim yayi saurin rufewa malik baki yana girgiza masa kai yace you deserves all this buddy kayi ma abby addua saboda kokarin sa ne har kaga irin wannan ranan “dr usama yakama malik ya zaunar dashi cike da kaunar dayake ma malik din yafara patting bayansa yakasa dauke idonsa daga kan malik he wished yanada diyar dazai ba malik ya aura ‘haka kawai yake jin malik har cikin ransa bakaramin tuna masa da yaronsa daya rasu ba yake tunda matar sukayi fight accident da yaronsa kusan 20yrs back shine har yanzu bai sake aure ba har yanzu bai samu wace zata maye masa gurbinta ba for the first time a rayuwarsa yaji ya yarda dawani for the first time a rayuwarsa ya yabi hankalin wani ‘shi kansa dr usama wani irin dadi yaji ganin yasaka malik din farinciki .one hour later sai da dr usama yagama duk wani cike ciken files kafin yatura komai na malik can asibitin turo mail,kafin yawuce kitchen ya bude fridge fresh juice ne yakawo musu sai few biscuits kan wani karin tray kafin yadawo ya zauna ya kalli dr ibrahim yace son kafin na bar Nigeria sai kayi providing plot wanda zaa gina maka private hospital not longer clinic kuma again you will owned a hospital you will be the MD. Shidai dr ibrahim kallon dr usama kawai yake amma jiyake kaman irin da wasa nan komai ke faru ashe haka malik yashiga shock da dr usama yayi masa albishir shikam mi zai sakawa dr faisal dashi a rayuwa ,dr usama dai