Sashe 24
Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ko kallon sa batayi ba” ledar maganin ta ya dauko ya ajiye mata tareda pure water ya juya yafita yana tafiya kamar wani boss “ sai daya cika plate da indomie yazuba ruwan Lipton din kafin ya zuba sauran da ta rage a warmer ya rufe ya koma parlor kan shimfidar dayayi ya kwana domin bai dauke ba” tafara samun appetite hakan yasata cin almost half of the plate ba karamin dadi indomie tayi mata ba ruwan zafin ma tasha ba laifi saidai bata shanye ba raurau tayi da ido sadda tana ballar maganin ta tsani magani miye ma abun ya dinga ajiye mata magani while ta warke , da kyar dai tasha magani ta ture ledar. Agogon wayarsa ya kalla 10:00am daidai tashi yayi Sai da yafara kwashe shimfidar daya kwanta akai kafin ya share parlor tass, kitchen din yashiga ya share yayi arranging abubuwa dayayi amfani dasu kafin ya hada wanda ya bata wuri daya, fitowa yayi ya dauke bargon da bedsheets din da pillow ba waenda yasiyo bane duk a gidan yasame su, dakin yashiga yanzu ma da sallama,can ciki ta amsa shi sai dayayi da gaske kafin yaji ta amsa din bargon hannunsa ya buda wardrobe ya saka can gidan kasa inda babu komai da bedsheet din da pillow, ahankali yabude ledar magani sai da ya tabbatar da tasha din kafin da dauki plate din da cup din ko ina ta rage, ya wuce kitchen ya wanke 2 plates din da few kwanunin, ko ‘ina a parts din nasu looks very neat and tidy babu dirty ko’ina saboda baya son kazanta tun can mutun ne shi mai son tsafta, zama yayi yana ta juya wayarsa babu number ko ciki sai ta dr ibrahim tun bayan tahowar su daga adamawa ya fida sim din ya yar ya siyi sabo a tasha dialing number dr ibrahim din yayi bugu biyu ya daga cike da barkwanci Doctor ibrahim yace balarabe mijin balarabiya, dariya sosai dr ibrahim yaba malik, yace wai waye balaraben kai yanzu fisabillah idan larabawa suka ji ka ai sai su sa akamani, dr ibrahim yace a kama ka sukoma da kai kasar su ko? Daman can Daga can din ka gudu “ malik bai sake cewa komai ba “ dr ibrahim yace ai nayi tunanin duk kamar yanzu baka tashi ba ,malik ya girgiza kai yace aa ni ai bana ranar bacci da asuba tayi shikenan da anga nayi ranar bacci tau a tabbata banda lapia gaskia “dr ibrahim yace kace kai ma iri na ne, malik yace naji kamar ma ba ka fita aiki ba lapia dai ko? Dr ibrahim yace lapia lau alhamdulilah am off today kasan daga karshan month din nan ma zan dauki hutu sai kuma bayan biki “malik ya ware idonshi yace no kabari dai sai can irin ya rage one week haka amma kace tun ending this month kusan wata daya da sati daya fa zakayi kana hutu “ hakane kuma tau shikenan yallabai na dauki shawarar ka malik yayi murmushi yace tau nagode “ ya mai jikin takara ji? Da sauki alhamdulilah dr ibrahim yace tau masha Allah in sha Allah nan da 20mins zan shigo gidan naka, malik yace tau Allah yasa daga haka ya kashe kiran. Dr ibrahim sai bin parlor da kallo yake koina tsaf tsaf sai kamshin turaran tsinke yake,kasa hakuri yayi har sai da yace wai har taji saukin fara gyaran gidan malik dai yayi shiru kamar bai ji sa ba, kitchen ya shiga ya zuba mashi sauran indomie da yasaka a warmer cikin plate ruwan Lipton din daya dafa ya huce saboda babu flask a cikin tukunya ya barshi hakan ya daura masa pure water biyu a wani plate ya kawo masa “ dr ibrahim yace sannu kace rabon naci dadi yasani zuwa gidan nan dawuri fara cin indomie yayi,can yayi kasa da murya yace kai fa abokina Allah yabaka wannan iya girki haka ko dai a catering tayi degree ne,shidai malik murmushi kawai yayi kafin yace kadai kar ace santi ne ya ruda ka,Kaci abinci kawai malam,tass dr ibrahim yacinye indomie bai rage ko kadan ba sunyi suna fira, har wajan 12:00pm dr ibrahim bai ko ji motsin aydarh ba “kuma bai ji malik yayi zancanta ba, kasa hakuri yayi yace ma malik,yallabai wai ina mai jikin ne ko bacci take sai sannan malik ya tuno ma da ita danshi sam ma ya mance da ita, malik yace kasan cikin drugs dinta kamar akwai na bacci , tunda tasha na safe bayan mun gama breakfast take bacci gashi yanayin garin akwai sanyi damuna kwara ta zauna a cikin dakin saboda yanayin lafiyanta kasan masu asthma “dr ibrahim daya gama sauraron malik yace “sure”fira suka cigaba dayi kamar waenda sukayi shekara 30 da sanin juna wannan ne karo na farko a rayuwar malik daya taba wani irin dama da matsayin daya ba dr ibrahim lokaci daya yaji ya yarda dashi kuma bugu da kari ma jinin su ya hadu;Dr ibrahim yace like I was saying before clinic din nan da chemist ne ahankali ya mayarda wurin clinic nida dr hafsa mun riga da mun san juna tun muna yara babana Allah yajikan sa malik yace Ameen ,da babanta tight friends ne a tare suke komai na rayuwa tare da ita mukayi primary school har sai da muka kai secondary kafin ita aka kaita boarding school ni kuma aka bar ni day,malik yace Allah sarki, dr ibrahim yacigaba dacewa Bayan munyi graduation ne daga secondary government ta dauki scholarship ciki har da sunayen mu ni da ita , saboda parents din mu daman sunyi kokarin ganin mun samu din saboda basu dawani karfin daukar nauyin mu,munyi jami’i anan BUK mukayi medicine kafin na karasa babana ya rasu itakuma bayan graduation dinmu da month daya mahaifinta da mahaifiyarta suka rasu yanzu haka tana zaune da kakarta inna daga nan gida daya ne tsakanin ku da gidansu,dr ibrahim na fadin sunan inna malik ya tuno da tsohuwar da ta rakasa siyan gas jiya sai sannan ya tuna daya ce mata zai shigo yau ma da basuyi wannan firan ba ya manta ma da zancan ta, malik yace indai innan dakake nufi ne jiya mun hadu da ita a kofar gidan nata har ta rakani siyan gas, Dr ibrahim yace kai haba? Malik yace am serious,dr ibrahim yace lallai kam ajiqa ka asha innar da kowa hakuri yake da ita,ita kanta dr hafsa dan bata biyeta da tuni kowa ya kama gabansa fa,malik yayi murmushi yace nima a jiyan na fahimce haka, dr ibrahim yace kasan yanzu government din aiki wahala yake sai idan akwai wanda ke tsaya maka, malik yace hakane, dr ibrahim yace wannan bawan Allah mai clinic din shine yayi employing dinmu nida ita duk karshan wata ana biyanmu 30k nurse saratu kuma yarinyan wani abokinsa ce diploma ne da ita a chew 20k ne salary duk month dan dai kawai kar mu zauna ba aiki amma mutumin dake da degree a med yafi karfin 30k as salary malik yayi murmushi yace in sha Allah komai mai wucewa ne, dr ibrahim yace tunda dai madam tak’I farkawa na duba jikinta bara na wuce akwai inda zani daga nan din, malik yace tau shikenan dr muje na taka ma nagode Allah yasaka “ dr ibrahim yace babu komai ai an zama daya har kofar gida ya rakasa anan suka tsaya dayake center ce har yasamu keke yawuce, har ya juya zai shiga gida yaji ana tafa hannu ga salati ana rabkawa,juyuwa yayi suka hada ido da inna dake tsaye da katuwar jikkarta da uban mayafinta da alama daga anguwa take,malik yashafa kansa yayi murmushi yace ina wuni, inna tayi mitsi mitsi da ido tace aaa haram aaa haramun miye wani ina wuni bayan baka kaunar Allah ina zaman zamana kace mun zaka zo hadda saman lambarka a waya dana kira lamba yan kamfani suka ce man layin waje ne bana najeriya ba,bacin ina tsoron Allah karya ba halina bane ai da yanzu nace daman baka da gaskiya,nagaya ma hafsa yarda akayi tayi banza dani kamar wata tababba daman can niba shiga harkanta nake ba tunda na lura babu Allah a ranta tak’I fito da miji tayi aure ina jin fa yanzu zata iya 50 zuwa hamsin da,samari duk wanda yazo sai ta koresa tau irin wannan mi zai sa ka dinga shiga harkar mutun? Malik yace babu gaskia,inna tace tau nan da kake ta sauri daman dai ba kayi niyyar zuwa gidan nawa ba kenan? Malik ya girgiza kai yace aa fa daman dai da yamma nayi niyya zanzo aie, inna tace tau shikenan amma yanzu sake sa man lambar sai ka kirani gabana naji kar ka sake sa wata kuma na kira ama kulle layin baki daya ka cuceni, malik yayi murmushi yace tau shikenan,sabowar number shi yasaka ya kira sai da tayi ringing inna ta yarda kafin ya kashe tace tau yi man sebin yace tau mi zan saka?tace rubuta audu kawai da manyan baki daman hafsa ce ke gano man, itama dai sai ahankali ba yarda nake da itama ba,sai kuma tayi kasa da murya tace inaga itama fa ba wani iyawa tayi ba karatun nan Amma kafin tagano man lambar mutane sai nashiga ukku shidai malik yayi shiru bai ce komai ba,inna tace tau sai anjima sai kazo ka gaishe da mai dakin naka,bata jira amsar sa ba tayi gaba. Suna fitowa daga sallar azahar shago ya wuce yasiyo flour da yaji dakake a rubber sai groundnut oil da star kwai yasiya kwara 4 yabiya kudin yatsaya wajan mai cefanan daya siya dazu suka gaisa dashi dan ya gane sa,fresh tomatoes ya siya da albassa anan yake tambayar mai cefanan idan zai siyi kuka da kanwa mai cefanan yace masa yaba yaron sa yashiga gidan dake kusa dasu ana siyarwa ya siyo masa,10mins sai ga yaron yadawo yasiyo godia yayi ya karba ya wuce, ruwa ya tara ya daura kafin ya kwaba flour danwake zaiyi wanda favorite food din sa ne ya iya danwake sosai abubuwan da bai iya ba kadan ne a girki yana tafasa ya jefa dan waken 30mins ya dauka yagama ya wanke tukunyar tunda kwara dayace Bayan ya juye danwaken a warmer ya mayarda da tukunyan ya