← Book details Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 197

Sashe 32

Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da dr hafsa sai saka take da warwara.Da sallama yashigo gidan dr hafsa ta amsa masa,bai san inna bata nan ba kawai yasa kai yashiga dakin dr hafsa tace ahh yallabai sannu da zuwa ina wuni?malik yadanyi murmushi kadan yace lapia hafsa sannu da aiki dr hafsa tayi yar dariya tace yawwa ai dole kamun sannu,haka kuke da gashi tabarakallah,shidai malik murmushi yayi ya dinga bin gashin kanta da kallo calaban tayi mugun kyau masha Allah kamar karya dauke idonshi daga kallon calabar mutun ne shi mai mugun son gashi yana masifan son yaga anyi kitso kuma a da har parking gashinsa yakeyi ko kuma su aysha suyi mashi kitso sai daga bayan nan ne ma yake aski ya ke dan rage ta kadan, can yayi kasa da murya yazuba wa bayan ta ido murya babu wasa yace ko baki ji na shigo ba dabazaki gaishe nib a ko kicemun sannu da zuwa,Kamar daga sama taji maganar sa tayi niyyar daya shigo ta rufe kanta amma bata son dr hafsa ta fahimce komai yasata barin kan aka cigaba da kitson, sai da murda masa baki duk da bata ganin sa kafin ahankali tace in anima baka gaishe niba da kazo ?bai san ranin datayi masa ba har yakai haka ba,yayi tunani zata gaishe sa din ko dan dr hafsa din,bai ce komai ba yayi shiru,sai dr hafsa ce tayi dariya tace tau ai kinsan rijalu su kullun sun fi son ayi masu,aydarh dai tayi shiru,malik din ma bai kara cewa komai ba kuma bai fita ba,har suk agama calaban tass Allahumma bareek bakaramin kyau calaban yayi ba akayi parking dinshi can kasa tasa hannu tayi mashi wani irin style kafin ta mike ta dauki gashin da ya zuba kadan zata zubar a dustbin sai yanzu dr hafsa taga yarda dinki ya zauna a jikinta sai yanzu ta sake ganin wacece aydarh sai tunanin ta yabata ko dai sake p-test din zasuyi, maybe akwai cikin ko boyewa yayi tunda alama yanuna kamar hips ya shiga da boobs dinta yarda shape din jikinta yafita kallo daya malik yayi mata ya dauke ido yarda take tafiya kamar da gayya yasa shi dauke kai , shigowa dakin tayi ta zauna kusa da dr hafsa idan ta ajiye hijab dinta kallabinta take kokarin daurawa dr hafsa ta kalli malik tace yallabai nace ko sake mata p-test din zaayi naga kamar akwai shi maybe ko shigewa yayi ba? Malik ya shafa kasa yace anya kau ina ganin no need,dr hafsa ta gyara zaman tayi kasa da murya tace aa yallabai kamar fa akwai cikin ko dai shigewa yayi cikin hips da boobs ko kuma ranar ansamu matsala ne aydarh dai kalli malik suka hada ido sai kumayi tayi kasa da kai,malik yace ma dr hafsa tau shknn zamu zo din dahaka ya mike yayi ma dr hafsa godiya yace ki same ni a kofan gida, dr hafsa tayi mata sallama aydarh tace thank you auntie “dr hafsa tace don’t mention aydarh sai anjiman ku,ku gaida gida,a kofan gida ta same sa tsaye yana jiranta yana ganin ta fito yajuya yatafi ta bisa baya daidai kofan shiga gidan suka hadu da Ramlah tsaye ta tare kofan gidan tana ganinshi tawani washe baki cike da bariki tace welcome sir malik yace thanks a takaice yayi hanya zai wuce ta wani sha gabansa wani kalan wawan kallo yayi mata yahada fuskar sa yawani hada giran sama da kasa billahi yarda yayi din kamar zata suma, gathering courage tayi tawani lankwasar da murya tace karar matarka na kawo maka aydarh najin haka tawani hada rai tayi wucewanta tana tafiya kamar batasan taka kasa, batasan raini ita kunyar kanta ma zataji ace ta tsaya tana magana da wannan trash din,malik ya ja da baya ya gyara tsayuwar sa bai ce komai bay ana sauraron ta tace kofan part din ku ta sakar mun a fuska daga naje duba ko kana nan malik bai ce komai ba yayi wucewar sa yabar ta nan tsaye kamar status. Toilet tashiga tayi alwalla kafin tafito ta chanza kaya ta hau prayer mat ta kabbara sallarh shigowa yayi dakin ganin tana sallarh yasa shi zaunawa kan katifa har sai da ta gama sallan ,yace miyasa kika buga mata kofa a fuska aydarh tawani hada rai ta juyo tana face dinsa sai kuma ta juya kai tace to ita miya hanata ka tambaye ta abunda tamun,shi wallahi dariya ma ta basa yarda tayi din yayi kasa da murya yace ai nasan ita ke da gaskia shiyasa kuma ni naso ma ace ta rama,aydarh ta mike tsaye tace to ai sai ka turo ta tarama din, bata tsaya jin abunda zai fada ba tayi fitan ta parlor ta bar masa bedroom din. Kitchen ya shiga ya zuba mata pasta daya dafa a plate yazo parlor ya ajiye mata gabanta without saying a word ya shige toilet din nan parlor yafara wankin kayansa jiya yayi mata nata wankin,bin bayansa tayi da kallo ta kafin ta mayarda idonta kan plate din ahankali take cin abinci cikin nutsuwa har tagama kitchen ta kai plate din ta ajiye ta dinka bin kitchen din da kallo ko dauke ido babu maganar dr hafsa ce ke dawo mata fresh a brain tama rasa kalar tunanin da zatayi,juyawa tayi tafita bedroom din ta koma ta zauna ta zubawa waje daya ido,yanzu haka na nufin ita zata cigaba dayin duk wani aikin dayake yi?sai kuma ta girgiza kai a ranta tace ai Allah bai kamaki da laifi tunda shi keyi bake kika saka shi ba dawannan tunanin ta zame ta kwanta amma sam zuciyanta bai yarda da wannan conclusion din,ahaka har bacci yayi gaba da ita da tunanin a ranta.Tun safe yake jin yanayin jikinsa babu dadi yasan kuma cewa maybe ciwonsa ne zai taso sam sai yabar hakan a ransa ya cigaba da addua domin bai san yarda zaiyi ba idan ciwon nashi yataso a yanzu,ko daya dawo sallan isha’I da kyar ya kwanta kan shimfidar sa dayayi anan parlor wani irin yanko masa zufa keyi lips dinsa har hadewa sukeyi yarda ciwon ke masa a yau sai yaji kamar ransa zai fita he is seriously in pain his condition is much critical babu abunda yake iya furtawa sai inalilahi waina illahil rajiun zuwa wani lokaci he is trying much to breath in and out numfashin sa ya toshe waje daya salatin ma yakasa bakin shi yahade waje daya.So take yashigo ta tambaye sa inda littafin azkar dinsa da take karantawa yake shine kawai abunda takeyi yanzu zuwa yanzu har tafara fahimtan wasu abubuwa daga ciki tafara gyara kura kuranta na sallarh shiru shiru taji sa bai shigo ba yasata bin kofan bedroom din kallo kamar zata hango sa ta kofan tashi tayi ta yafa mayafin abayanta tana tafiya ahankali har tafita parlor ganinsa tayi a kwance yayi facing wall tasan ba bacci yakeyi ba maybe da gangan ya dauke littafin daman dan yasan zata zo nema shine yake wani pretending as if he is sleepy,batace komai ta zaune can karshan parlor tayi raurau da ido kafin murya can kasa tace ni kabani,shiru bai tanka ta ba bakaramin haushi abun yabata ba,bata gaji ba tace ai nidai babu ruwan ka dani tunda bana taba ma abu wallahi,still malik bai tanka ta basai wani irin numfashi da yasaki kamar wanda aka zarewa numfashi gabanta ya yanke yafadi ta mike tsaya batasan abunda yasa yayi numfashin amma numfashin dayayi Kamar wanda ke struggling da breath ensa ahankali ta matsa kusa dashi tana kallon shi,juyuwa yayi jikinsa ya jiqe sharkaf da zufa ganin yanda yake zufa yasata binsa da kallo ahankali ta daga idonsa da kyar yayi mata alama da hannu nata zo,yarda gabanta ke faduwa kamar zai fito waje yasata bin bango har ta karasa kusa dashi ahankali yake fadin ruwa ruwa bataji da kyau bah akan yasa cewa baka da lapia ne hankalinta a tashe gyada mata kai yayi ahankali kuma yasake buda baki yace ruwa dasauri tashiga kitchen ta dawo hannunta rike da pure water yakasa daga hannunsa balle yakarbi ruwan yasha ganin hakan yasa ta fasawa ta kai ruwan daidai satin bakin sa daga nan kwance tabasa ruwan yama kasa sha sai zubewa yakeyi ta gefen bakinsa, yarda jikinsa yake kyarma bakaramin daga mata hankali yakeyi ba tarasa abunda zatace masa,ahankali tace sannu,hannu yasa ya rike nata hannun tanajin yarda jikinsa yayi mugun zafi he is running temperature ahankali tace sannu mike maka ciwo?kanka ne?you are running temperature mike damunka yarda take maganan muryanta very slow and innocently kamar zatayi kuka ,daurewa kawai yake amma ji yake kamar zaa zare mashi rai cikin shi nawani irin masifar ciwo har yanajin yarda jinin shi ke gudu a veins dinsa ,aydarh dai tarasa yarda zatayi banda bin sa da ido babu abunda take bata son taga wani na ciwo tana da mugun tausai wayar dake flashing light wanda a silent take ta kalla kiransa ake da kamar kar ta dauka sai kuma ta kai hannu ta dauki wayar kallo daya tayiwa sunan mai kiran tagane ko waye sallama akayi cikin sanyin murya ta amsa daga can dr ibrahim yace ahh madam ina wuni,ina wuni tace masa kafin yace baya kusa ne?aydarh ta kalle shi ganin yarda yake kyarma na yanzu yafi na dazu can kasa da murya kamar zata fashe da kuka tace bai da lapia dr ibrahim yayi salati yace subhanallah tun yaushe miyasa me sa?Tace nima bansani ba yanzu ne kawai nasame sa ahaka dr ibrahim yace karki damu ganin zuwa yanzu,15mins sai ga kiran dr ibrahim yasake shigowa tana nan zaune ta zuba masa ido ko daukewa babu hankalinta idan yayi dubu yatashi bata kowa batasan kowa anan ba sai shi,a duniyar ma baki daya yanzu bata da kowa sai shi,daukan kiran tayi yafada mata yana bakin kofan part dinsu dasauri ta koma bedroom tasaka hijab dinta kafin ta bude masa kofan,tun daga bakin kofa ya hango malik din ya hango yarda yake kyarma ga zufa yanayi dasauri yashigo ya durkusa kusa dashi yarda jikin yayi zafi yana zufa ga kyarma ba karamin dagawa dr ibrahim hankali yayi ba dasauri yasaki gudun fan din parlor,yakalli aydarh yace tun yaushe yake haka madam kuma miyasa baki kirani tun dazu ba sai dakika bari abun
Chapter 32 · 0% Book details