← Book details Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 197

Sashe 37

Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kamar mai irga numfashin ta, kusan 5mins yana ahaka sai yau ya lura da kunnata bula ne har uku kowani a jiki akwai hadaddan barima gold bakaramin kyau bariman yake dashi bad uk duniya ya matukan son bula shiyasa a gida ma yake yawan ba su aysha kudi yace su siya earring su saka a bulan su, gajiya yayi da tunanin dakuma binta da kallo dayake faman yi kuma yana son magana da ita,kafin ahankali ya mike yaje saman kanta yatsaya sai kuma ya duka ya buga pillow datake kai,jin ana buga pillow yasata bude idonta dake cike da bacci ahankali har takarasa bude idonta a kanshi,sai kuma ta juya kafin ta mike tana kallonsa,yace ki daina barin wutan dakin nan kunne batace komai ba tayi maza ta dauki hulan kanta ta mayar, ya dauki plate din fruits din ya daura mata a laps, ta dinga bin kankanan da apple din da kallo can kuma sai ta dauke ido, bata fara shan fruit din ba shima kuma bai tashi ba,kuma baiyi magana ba ya dai dinga kallon waje daya kafin ya mike tsaye ya zuba duk hannunsa biyun a pocket din jeans dinsa yace ki shirya gobe zamu fita dasafe,taji abunda yace haka yasata dago kanta ta zuba masa ido kafin tace, ina kuma zamuje?kamar ba zaiyi magana ba har yakusa fita daga dakin kafin yace, zuwa zanyi na siyar dake,daga haka yafita hararar bayansa tayi ,kafin ta dauki fork din ahankali tafara daukan apple din ta kai baki , tass ta shanye kafin ta dauki plate din walking slowly ta tura kofan kitchen din ta shiga plate din ta dauraye tana mamakin inda yaje don bata gansa a parlor ba, yana shigowa yasa key ya rufe kofan kafin yayi switching off din globs din parlor,tana sa kafa ta fito daga kitchen din ta ga ankashe wutan parlor tasan shine dan har yanzu akwai wuta tana ganin hasken globes din compound din duk da hasken baya shigo har cikin part din nasu, bata son duhu hakan yasata dinga bin bango, lafiyan sa yake hankali kwance dan bai kawo ma ransa tana parlor ba, wani irin karo suka ci dashi har sai da kafanta yayi bending tafadi kasa,the incident cames suddenly shiyasa he can hold it kawai yabita suka fadi itace akasa shine a sama,jinsa kanta yasa hankalinshi yayi masifan tashi bata ma ji zafin faduwan batasa hannu iyakan karfinta ta dinga ture sa tana hawaye yayi mata nauyi sosai har kirjin su daya hadu waje daya nasa numfashin ta yin sama sama,malik kau da bai masan yanayin dayake ciki ba ko gizau bai yi ba jin shi plate a jikinta bakaramin birkita sa ba yayi,yama kasa yin komai he already lose his weight, hankalinsa bai dawo jikinsa ba sai dayaji tasaki wani kara sannan cikin hanzari yayi saurin tashi akanta,ahankali ta mike ko juyuwa batayi ta shige bedroom din kan katifan ta kwanta ta rufe idonta da karfi still hawaye ke ta zuba a idonta,tun daya kwanta yakasa bacci,sai dawo masa abunda yafaru keyi akai.Kallonta yake ko kiftawa babu ta yafa mayafin gown din, still tak’I yarda su hada ido sai kallon waje daban take,yayi kasa da murya babu wasa ko kadan a fuskan sa yace ai da baki yafa mayafin ba ma kin tafi ahaka “ sai yanzu tajuyu ta kallesa batace komai ba ta dauke kanta,ta nufi hanyar kofa,har takusa fita kafin yabude wardrobe ya dauko mata hijab dinta daya goge mata, bai ce mata komai ba ya warware abayan ya mika mata bata karbi abayan ba kuma bata kallesa ba ganin tana bata masa lokaci yasa shi zare mayafin kafin yasaka mata hijab din duk abunan dayake ko motsawa batayi ba har yagama yafice yabarta nan tsaye ajiyan zuciya kawai ta sauke kafin ta bisa ba,kofan part din ya kulle ya saka mukullin a aljihun wanda yard dinsa yayi matukar karban jikinsa zaka rantse da Allah yaron wani babban ambassador ne ko kuma wani minister kudi duk da yard ne mai karamin kudi ne amma bakaramin haduwa malik din yayi ba cikin yard din, baby pink din hijab din daya saka mata ya hau sosai da touches din flower gown din nata Sosai yahau da gown din, daidai kofan gidansu suka hadu da dr hafsa itama ta fito daga gida tana neman keke zata tafi clinic,murmushi tasake tana kallonsa tace Good morning my couples malik yayi murmushi yace morning dr yah inna?dr hafsa tace inna lafiya lau,aydarh ta kalli dr hafsa kafin tayi wani cute simle tace Good morning auntie,dr hafsa tace morning mrs malik mun tashi lafiya yajikin yallabai? Aydarh tace Alhamdulilah ,dr hafsa tace yau fitan safe za’ayi ba? Aydarh ta kalli malik ta gefen ido hankalin sa na kan keken dake tahowa kafin tace Erh dr hafsa tace wannan kauna haka aydarh dai tayi murmushi ta saukan da kanta kasa dr hafsa tace ni bara na kara gaba maybe nasamu keken a can tunda kila ba hanya damu mukayi ba right?Aydarh taware hannu kafin tace bansan inda zamuje ba,ko ki tambayesa,dr hafsa ta girgiza kai tace aaa fa sai kundawo kawai sallama tayi da malik kafin tawuce, keke suka shiga yayi masa kwatancan inda zasuje,shiga sukayi mai keken ya sauke su har kofan islamiyan da babu wani nisa sosai daga anguwar su, aydarh dai sai bin makaranta take da kallo bayan sun sauka malik yakalleta yace muje ciki, office din Headmaster suka shiga already sunyi waya tun a hanya kafin su iso suna shiga cikin mutunci suka gaisa da malik da headmaster, kafin aydarh ta gaishe sa ya amsa ta batare da ya kalle ta ba, headmaster dake sauraron bayani da malik ke masa yayi shiru kafin yace tau shknn yallabai in sha Allah babu abunda zai gagara nafahimce ka kuma mostly sauran daliban ma duk hakan ne shiyasa ma aka gina islamiyan,malik yace Tau Alhamdulilah,ita dai aydarh tayi shiru sai sauraron su take,nan akayi komai malik yabiya bill din komai kafin ya karbi kalan yard din uniform din kafin sukayi sallama cikin mutunci yafada masa ranar da zata fara zuwa makaranta.saidai sukaje kasuwa anan suka yanke yard din uniform din kafin yatambaye inda ake dinkawa mai siyan da yard din yace anan din ma suna dinkawa hijab aka dinka mata har kasa sai doguwan riga marar hannu,light blue ne uniform din hakan yasa shi siyan mata light blue din inner cap anan shagon har zasu tafi sai ya juyu yace amm a ina ake siyar da nikkab? Mai shagon yahada su da yaron yace yaraka su wajan dake siyarwa, kala biyu ya siyan mata kafin su hau keke suka tafi gida, suna isa gida time din har ankusa azahar,sharp sharp yadaura macaroni fari sai stew already suna da cefane cikin 40mins yagama komai ya juye a warmer kafin yashiga toilet yadauro alwalla yawuce masallaci, shigowar sa kenan daga masallaci duk yau bai ganta ba sai yanzu ta gefenta yarabe zai shiga cikin gidan tayi saurin tara gabansa, hakanan kawai yaji yau yana son mata warning , chewing gum take chewing irin yarda cikakun mararsa kunyar nan ke ci wani irin baci ransa yayi bai dai ce mata komai yana jiran yaji abunda zatace din, inna ranka dade?ya karfin jiki? Kar ka damu fa kan abunda yarinyar nan tamun jiya ni bai dameni ba sam saboda ni bama da riko ko kadan,malik dake tsaye nan fuskar sa babu alaman wasa cikin isa yace “hey”quiet “ sai da gabanta yafadi yarda sound din muryansa yafita, yace this should be the first and last time dazaki dinga mun irin haukan nan, don’t repeat this mistake again karki sake shiga gabana idan ina tafiya not only me,even my wife she is not your mate, wucewa yayi yabar ta nan tsaye baki bude, yana shiga ya tarar da ita kofar bedroom da alama yanzu tafito, sallama yayi ta amsa kafin kuma ta juya takoma bedroom ,kitchen yashiga ya zuba mata abinci a plate yakawo mata sharp sharp yagama cin nasa abinci daman uzuri ya dauka yace zai je wani waje bazai dawo da wuri ba, yau ma bashi ya gyara mata bedroom din ba ita ta gyara abun ta tsaf kafin kuma ta shiga kitchen ta wanke few plates din da yabata bai tsaya wankewa ba.. Malik yace tau fa bai kai nan ba tun farko ai laifinka ne mi zai sa kace musu zakayi event daga baya kuma ka fasa?dr ibrahim yashafa kansa yace aie ni fa banma san lokacin da nace haka ba , malik yace au haba? Giyan soyayya ya dibeka kenan kayi musu karya,dr ibrahim yayi dariya kafin yace wallahi fa,malik ya gyara zamansa yace tau gashi ai yanzu ta sake ka,kaga dagaske hidiman zaayi dr ibrahim yace wallahi fa,kafin yace ni yanzu ba wannan ba number yarinyar nan zan baka ka kirata please kadan bata hakuri saboda yanzu haka fa fushi take dani,Malik yace aaa ni na aike ka kayi musu karya? Dr ibrahim yayi kasa da murya yace kai fa matsala gareka,ka taimaka please kasan fa yarda auran zumunci yake malik yace nikam taya zan san yarda yake,dr ibrahim yadinga bin malik da kallo baki sake yace ina kaima auran zumuncin ne,malik dai yayi shiru bai ce masa komai ba sai can yace yanzu naji zan kirata nabata hakuri nace mata yau har masu ciwon ido ma allura ka basu, su biyun babu wanda baiyi dariya ba,dr ibrahim yace nidai najib a komai idan zaka bata hakurin, Aydarh tabude kofan bedroom din tafito ahankali har tazo tsakiyan parlor taga dr ibrahim,ahankali tace ina wuni,dr ibrahim yace lafiya lau alhamdulilah madam ya gida ya mai jiki? Aydarh tace Alhamdulilah dr ibrahim yace madallah, malik dake kallonta ko dauke ido babu ya mike tsaye ya kalleta yace nazo ne? Batace komai ba ta girgiza kai murya can kasa tace “inna” yafahimce abunda take nufi mamaki take basa yarda take abu kamar wata yar yarinya nufinta fa gidan inna zataje, malik bai ce mata komai ba ya juya ya kalli, dr ibrahim yace dr bara na rakata gidan inna ina dawowa yanzu dr ibrahim yayi murmushi yace tau shknn, tunda nan da gidan innan ma bazaka barta taje ita daya ba, malik bai ce masa komai ba yabi bayanta har ta riga tayi gaba,kowa na
Chapter 37 · 0% Book details