Sashe 26
Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yayi ya ganta tana salla,murmushi yayi iya lips dinsa yafice daga dakin a plate ya saka mata awaran kafin ya zuba tasa a warmer , sallama yayi ta amsa sa can kasan makoshi kamar wace throat din ta ke ciwo mamakin halin yarinyar yake,ta idar da sallan still kuma tana zaune kan prayer mat din “ bata tashi ba ajiye plate din yayi ya fita. TWO WEEKS LATER Zuwa yanzu malik ba karamin sabo yayi da inna ba sosai suka saba kullun ne da yamma sai yashiga gidan indai kau baije baya tare da dr ibrahim suka fita wanda yanzu ya zamar masa kamar wani dan uwa tsakanin sa da aydarh har yanzu babu mai ma dan uwansa magana, kullun ne sai yadafa ma ruwan wanka ya kai mata abinci kau babu fashi kullun sai ya girki duk wani gyaran gida shi yakeyi,ya fuskanci abubuwa dayawa game da ita,wani lokacin idan tayi wani abun dariya take ba sa akwai ranar da inna ta matsa mashi sai sunje ta ga mai dakin sa, suka tafi tare shiga yayi daki yasame ta tsaye inda take tsayuwa kullun tana kallon mutanan gidan,bai san mi zai ce mata ba kawai yasa shi cewa ga innata nan zaku gaisa batayi magana ba dan batasan wace inna ba. Kayan ta kala biyu ne daga gown din atampha sai abayar ta wllh ta gaji da saka su bra daya take using idan tayi wanka ta wanke sai ta zauna haka har sai ta bushe sannan ta mayarda,abayar ce jikinta ta daura kallabin akai fita parlor tayi wanda bata cika zama a nan din bas ai idan baya nan ko kuma an dauke nepa tazo ta tukure kanta waje daya shidai yana ganin abunda takeyi baya tankata ya fahimce yarda take tsoron duhu hakan yasa shi siyan mata torchlight indai babu nepa ta dinga haske haske kenan, Ahankali take tafiya har ta iso cikin parlor kasancewar yamma ce akwai nepa hasken globs din parlor sun haske fuskarta tarr kullun kara kyau take sometimes malik har mamakin ta yake yakan tambayi kansa wai mata haka suke ko kuwa? Wani lokacin dr ibrahim neke yawon kawo masa zancan mata da zamantakewar aure har wani zakewa yakeyi shima yakusa shigo daga ciki yaji abunda suke ji, shidai malik saidai yayi murmushi kawai har mamakin dr ibrahim yakeyi shi baya kunyar ko wace magana “. Murmushi kadan a fuskar ta,ta zauna kan carpet din parlor tana gaishe da inna dake ta faman zara ido kamar wacce aka tsikara haka inna ta mike tsaye tana kallon malik da aydarh tasake bude idonta sosai kafin ta koma ta zauna tace Allah mai halitta sai kuma ta kalli malik tayi kasa da murya tace audu ashe kafini gaskia danace boyun matarka kake ashe dole ka boyeta, masha Allahu sai kuma ta washe baki tace tsali yo Allah na tuba audu ku wannan kamar dai ku aka hada ma wa, sai kuma taja bakinta tayi shiru tace ah babu ruwana balle ace nayi sabo amma wannan dai wannan dai sai kuma tayi shiru,shidai malik sai kallon inna yake aydarh ma tarasa abunda zata ce mata, inna tace ya sunan ta kace?ahankali malik yace ASSIEYERH yarda yafadi sunan kamar da larabci yasa inna kasa fahimta yarda yafada , zata sake magana akayi knocking kofan part din nasu malik yace waye muryar dr hafsa suka ji tana fadan ita ce, bude mata malik yayi inna tadafe kirji tana kallonta tace yanzu kuma haka kika zama ni hajara nabani, tayi kasa da murya tana kallon aydarh tace kiji bala’I daga taji labarin nazo nan har ta biyo ni, dr hafsa dake gaisawa da malik ko ta kan inna bata bi ba, ta kalli aydarh tace patient daga rana ban sake ganinki ba kuma saidai yallabai murmushi aydarh tayi tace ina wuni dr hafsa ta amsa tana tambayar ta ya jiki, labari sukeyi duk da inna ce mai labarin ita dai aydarh murmushi ne nata,malik kau da har yasaba fira da inna biye mata yayi suna fira, ana labari da dr hafsa tayi magana sai inna ta kwale ta sai wajan six suka yi sallama zasu tafi har waje suka rako su dr hafsa da ta daga waya tayi gaba sai inna a bayanta aydarh a bayan inna malik ke can bayan su, har suka fito building din parts dinsu inna batayi shiru ba, ganin tana neman fita yasa shi jawo……… Kallonta yake ko kiftawa babu itama ido cikin ido take kallansa ,kasa yayi da murya cikin tsare gida yace duk ranar da kika kara kokarin fita a haka babu hijab sai na karya ki,yasake ta yafice “anan tsaye yabar ta mamaki ya cikata har kofan gida ya raka inna sannan yadawo, bata parlor yasan cikin daki ta koma, hakan yasa shi yin zaman shi a parlor kwana biyun nan kudin hannunshi sun kusa karewa,shiyasa yake so idan anjima suyi shawara da dr ibrahim kan abunda zaiyi.Dakin yashigo ko kallansa batayi ba yana tsaye kanta “ta turo baki “tace nan da ka tsaya mun akai fa? Malik mamaki ne ya cikasa, sai yaji kamar bai ji da kyau ba, yace dani kike duk yarda gabanta ke faduwa na masifan tsoron shi da yanzu ta yarda tanayi bai hanata ,mikewa tsaye ba tace erh, bai ce mata komai ba ya fice daga daki “ . Kallonshi yakeyi har sai da yayi shiru yace tau shknn na fahimta Allah yakaimu lapia, dr ibrahim yace Ameen “shiru ya biyo baya dr ibrahim yamike tsaye yace bara na fita na jira ka kar time ya wuce,malik ya kalli watch din hannunsa yace har na kusa mantawa ma fa ashe yau ana wasa “ dr ibrahim yace sure kayi sauri mu tafi, fita dr ibrahim yayi kofan gida,shi kuma malik ya juya yashiga kitchen indomie daya dafa masu ya zuba mata a plate sauran tasa kuma ya zuba a warmer, salla take sai da yatsaya kallonta yake ko dauke ido babu,ganin yarda take salla ajiyar zuciya ya sauke tareda girgiza kai kwata kwata ba a daidai take sallan ba hakan na nufi bata iya ba ko mi? Har tagama kafin ajiye plate din hannunsa yace ki kashe globs kuma din kafin ki kwanta bazan dawo da wuri ba, batace komai ba shima daman baiyi tunanin zata ce din ba,yayi ficewar sa, kusan five minutes tana kallon plate din indomie hawaye yazo mata a ido tashare ashe zata iya saba wa ahaka ashe zata iya rayuwa dasu ashe zata iya cin cimar su?zuwan inna yau sai ya wanke mata kashi ashirin cikin dari na damuwan ta ashe suma suna rayuwa cikin farin ciki, kullun sai ta tsaya bakin window bedroom dinta tana hangen yarda yan cikin gidan ke shiga da fice zuwa yanzu ma tasan fuskokin su,sau dayawa zataji suna fada wanda kullun ma cikin haniya suke, share hawayen ta tayi ta jawo plate din tafara cin abincin kaman bata so, halinta ne rashin cin abinci shiyasa bata ci dayawa ba ta mayar kitchen ta rufe kamar yarda taga yanayi, shimfidar shi da ya fito ta bi da kallo tana karamin tsaki ta shige daki haka kawai taji bazata yi abunda yace din bas ai taga yarda zaiyi, a ranta tace shi kullun Kamar wani force ya dinga daure fuska yana magana Kamar baya so, trash tafada kasa kasa, ta je ta kwanta kasa bacci tayi domin ba ta iya bacci cikin haske ka’ida ne shi ke kashe mata glob,yau kuma daya sata kashewar bazata kashe ba so take ya dawo taga abunda zaiyi tunda shi komai na masifa ne bala’i’a kawai ta fada kasan ranta. Bayan yagama duk wani aiki da shi keyi na gidan ya kai mata ruwan wanka tayi, sai da yabari ta shirya kafin ya shiga dakin ya jingina da kofa yayi folding hannunshi a kirji straightly yake kallonta da waennan idon nashi , kanta na kasa bata dago ta kalle sa ba tana dai jiran abunda zai ce, babu wasa a muryar shi yace I asked you to off the globs yesterday and you refused to do sures why, wani banzan kallo tayi mashi sai kuma tayi saurin janye idonta ta juya masa kai, tace I can’t “ wallahi banda umarnin ummi ba yarda yake da zuciyar nan baya son raini da rashin kunya da yau kam sai ya balla yarinyar nan,shiru yayi yana cigaba da kallonta still bata juyo ba tana yarda take,takawa yake ahankali kan carpet har ya kusa zuwa inda take,dawani irin mugun speed ta mike ta manne a can karshan wall din dakin tace wallahi’bada kai nake ba don’t beat yarda jikinta ke shaking yagane ba karamin tsorata tayi ba amma rashin kunya bata hanata murguda masa baki ba, sai dayazo towards her sun kure ma juna sosai numfashin ta na barazanar fita ta rufe idonta gam yana iya hango yarda gaban ke over racing kirjinta na dagawa sama da kasa,wannan bakaramin daman kare mata kallo yabashi ba kallonta yakeyi ko kiftawa babu yah rabbi,dasauri ya dauke idonshi,yace this should be the last time da zanna saki abu bakiyi ba I will surely deal with you and your mate ko kuma na kai ki can wurin wanda yayi maki cikin aka like mun sharri sai ki cigaba da mashi ranshi kunyar bani ba idiot, wallahi har cikin ranta taji zafin kalmar dandanan idonta ya kada yayi ja bude ido tayi fuskanta har yayi ja kuka na kwace mata cikin wannan shagwababiyar innocent voice din nata da dan karfi take maganar tace ni babu wanda yayi mun ciki ban san kan abunda suke magana ba kuma duk wanda yasake ce mun wannan abun ban yafe masa ba kafin ta fashe da wani irin kuka tana silalewa kasa kan tiles ta hade kanta da gwiwa tana kuka mai shegen karfi numfashin ta har sama sama yake,daga yarda tayi maganar kawai yasa kan malik sarawa he cannot lie or deny anything yaga tsabar gaskiya a idonta inalilahi waina illahil rajiun wannan wane kalar alamari ne, kusan 10minutes bai tashi ba ita kuma batayi shiru ba har sannan kukan take,hankalinsa baya jikin shi tunani ne kala kala aransa, can yaji tana wani kalar numfashi kamar tana kokowa ma da numfashin, dasauri yasa hannu ya dago kanta fuskar tayi ja sosai idonta