Sashe 12
Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tabata ba ya dai daure ya dauke ta yanufi hanyar waje hajajju ta gwalo ido ta kalli rufaidarh tace anya kau ba mutuwa tayi ba?rufaidarh tashare hawayenta tace aa hajajju ina tunani rudun da tashiga ne in sha Allah zata tashi tau Allah yasa dai mudai bara mutafi sai kuma tayi kasa da murya tace yau dan dole kawai zai sa na kwana wannan kuturun gida na ibrahin gashi audul din dake siyo man abubuwan da bazaa rasaba yau ko bindiga aka bashi ni zai harba yoo Allah natuba daga taimako sai abu yadawo kai na shi hwa taimakon shi nayi dana sa aka bashi yarinyar ita dai rufaidarh kallon hajajju kawai take batayi magana ba dasauri hajajju ta bi bayan ummi. Babu yarda rufaidarh batayi ba su bari driver ya mayar dasu abby yace babu komai sun gode zasu samu dan sahu, hajajju da bata so haka ba tayi mitsi mitsi da ido tace kai kuji tababbe tau a ina kaga alamar dan sahu anan anguwar salon aganmu cikin dan sahu kamar wasu yan iska ace manah mayu yan kwakwa munzo maula kamar wasu zararru ina dalili da kyar dai aka shawo kan hajajju suka samu napep suka tafi ummi da abby suka shiga daya Malik dake dauke da aydarh kamar baby a kirji wanda riqe ta dayayi yanayin shi ya chanza bai fahimce komai abun dunia ya taru yayi mashi yawa tare suka shiga da hajajju,fuskar nan tashi kamar hadari dinki tsab idonshi kamar zaiyi aman wuta turaranta ya takurawa rayuwar shi.Assalam babyn habeebe’s 💖nace bara na gaya muku ina yan mata? Ina haddadun mata?ina manya mata?ina yan gayu? Da zawarawa baki daya 🥳💖nesa ta zo kusa kina neman musulmin turare mai kamshin rahama turare mai musulmin kamshi💖💃🏻👌wanda zai sa duk idan kikaje a kalli ki domin kamshin shi cikin nutsuwa yake fita 💃🏻tau nesa tazo kusa come one ☝️ come all to real scent perfumes💃🏻nake gaya muku karshan kamshi ake magana just dm me and purchased yours 😉💖muna da air fresheners masu kamshin oud 👌💃🏻 Turaranta ya takurawa rayuwar shi, hajajju ta kauda fuska tace uhm “ tau banda ma neman bala’I irin na ibrahin mi yayi zafi daga wannan dan abun sai ya danna maka auran yarinya “tayi kasa da murya tace tau wai da kake ta wani daura fuska kamar wani afta mi zakayi aure ne an riga an cuce ka an Baka ma yarinya ,ga yarinya kuma ba lafiyaya ba , Allah na tuba ita kuma asiya ta dauka da zafi tasaka gaba da masifa kamar wani dan iska shidai malik bai ce komai ba domin bai ma da abun cewa , hajajju tace ohh dan ka daukeni zararra ina ta magana kayi shiru kana ta bina da ido kamar wata tababba Still malik was quite da tasan yanda yakeji da bata dameshi da wannan surutun nata ba marar kan gado ba da tasan yarda yake ji datayi shiru, har suka sauka gida hajajju na mashi masifa wai tana magana yayi mata shiru, suka sukayi abby ya biya masu keken kudinsu ko gida bai shiga ba ya wuce masallaci ba lokacin sallarh bane amma yana bukatar dayaje ko yasamu nutsuwa ‘ko kallon shi ummi batayi batace ya wuce ya kai aydarh dakinta aysha da su halime kallon ikon Allah kawai suke sun rasa abunda ke faruwa Yarinyar da suka zo dazo da hajajju ce tau ya akayi yayansu ya dauke ta miye hadani su da ita dazo ta shigo da kafanta yanzu kuma an kawo ta? Basu san wanda zasu tambaya ba hakan ya sa suka zubawa ikon Allah ido , ummi da still idonta ke jawur ta kalli aysha tace daura man ruwan zafi yanzu ta sa kai tashiga dakin kan gado ya kwantar da aydarh har yanzu kuma bata bude ido ba! Ummi ta cire hijabinta ta linke ajiyar zuciya ta sauke har yanzu bata gama dawowa daga shock din da ta shiga ba abu ne wanda ya faru tamkar a flim lalle Allah abun tsoro ne shike juya alamari a duk yarda ya so ,ahankali taje kusa da aydarh tana kare mata kallo batasan sanda murmushi ya kufce mata ba hawaye ke zuba a idonta tana kallon yarinya wani irin kaunar ta ke bin duk wani sashen jikin ummin bata so hukunci ya kasance hadda na nesa dasu da abby yace ba amma babu yarda zatayi dole tabari a nuna masu kuskuran su dole taba zuciyarta hakuri a hukunta malik din. Ahankali take buda idonta kanta yayi mata nauyi sosai jikinta kamar ba nata ba zuwa yanzu tafara jin sassaucin ciwon da maran ke mata,wata irin ajiyar zuciya tasauke tana tuno yarda komai yafaru gata kuma a wani daki na daban wani irin azababban kuka tafashe dashi da sauri ummi ta riketa kallonta take batasan ta inda zata fara mata magana shiru tayi tana kallonta , kuka kawai take har sai da ummi ta lura da yarda take wahalar da kanta ga numfashin ta na janyewa yasa ta fara lallashinta yau ne karo na farko da ta zauna da wata mace babba bayan oum da rufaidarh kuma yau ne karo na farko dataji tanajin masifar nauyi da kuma kunyar wata hallitta batasan miyasa ba batasan ya akayi ba yi shiru kawai da ummi ta ce mata sai taji kamar wani abu aka hura mata a zuciya. Zuwa yanzu tagama saddakar da kanta tagama sallama ma rayuwa bata dawani saurin gata ba abbanta ba oum ba auntie rufaidarh babu salma Komai kallonshi take bako a rayuwarta duk yanda tak’I gidajan talakawa duk yarda take kyamar gidaje irin haka wannan sam bataji komai game dashi bata ma da nutsuwar fahimtar komai , da sallama aysha tashigo tana kallon aydarh ita dai aydarh ko sanin shigowar aysha ma batayi ba,aysha tace ummi nagama “ ki zuba a bocket ki kawo shi toilet din dakin nan da to aysha ta amsa sannan ta fita. Ummi ta taimaka mata tayi wanka domin sam jikinta ba kwari bata da kayan da zata chanza kuma ka’idan ta ne idan tayi wanka ba ta mayar da kayan da ta cire ,ummi takalle ta tace al’ada kike? Sunkuyar da kanta kasa tayi domin bata fahimce abunda ummi tace ba ganin hakan yasa ummi cewa mp kike ? Ahankali ta gyadawa ummi kai batareda da tace komai ba ta share hawayan dake zuba a idonta, mamaki ne yakama ummi period kuma? Mi zai kawo mata period yanzu a halinta da take ciki wannan wani alamari ne mai wuyar ganewa? Duk iya tunani ummi takasa gane komai hakan yasa ta mikewa ta fita. Hajajju tayi shiru tace wllh kun dai ji tau Allah na tuba ai daman abunda yadace ayi masu kenan a kori yan banza daga cikin mu baki daya nan da shekara hamsin haka sai su dawo,aysha was so confused the three of them are speechless kallon hajajju kawai suke babu ko dauke ido can halime tamike tace yanzu hajajju kun yarda duk anyi hakan gaskia yayah bazai wannan abun ba,hajajju ta kankace ido tace minene kuma yayah tau shi audul din wanene zaayi mashi sharri kai kuji wata rubabba nan tau dan uwwaki haka akayi yanzu haka anbaka masu aure kuma ance su kwasa subar cikin mu,Allah sarki audul ko wacce duniyar zai kwashe ta su shiga oho ta karasa maganar tana tafa hannu,ni tsorona Allah tsorona karsu shiga cikin mutane ayi tunanin daga wata kasar aka watsu su ahtau yara kamar su aka tara ma kenn dunia to kila daga ni sai su dai akayi ma wannan kyautar , Maryam dai so take kawai taje wajan aydarh bakaramin dadi taji bai to amma taga su aysha da halime duk sun wani damu duk da babu dadi amma ai ance cikin ya bare kuma ma har an daura masu aure babu wanda yasan ma da zancan cikin haushin ta daya da akace wai zasu tafi subar Adamawa tau ina zasu,daga haka babu wanda yasake magana cikinsu hajajju kwanciya tayi taba su baya “ummi tace tau tsayawa zanyi jiranki bazakiyi sauri ki kira shi ba? Da sauri halime tayi hanyar dakin malik,shiga tayi ta iske shi kwance idonshi a rufe ahankali tace yayah yayah yayah har sai da takira shi sau uku sannan ya bude runanni idonshi ya zuba mata su sai data tsorata ganin shi ahaka sannan tace ummi nakira ka bata jira amsar shi tafita domin tasan bazai ma amsa din ba. Da sallama yashiga dakin kasa hada ido yayi da ummi itama ummin bata kalleshi ba kallo daya yayi ma aydarh dake kwance cikin bargo ta nade kamar wata baby tsaki yayi ya dauke ido still ummi bata kalleshi ba kuma batayi mashi magana ba “can tace bakin layi zakaje kasiyo mata pants biyu da sanitary guda daya kasan maganin daya dace da ita ai daga haka bata sake kallon inda yake ba ta dauke ido domin wani irin zafi da quna take ji da har wai ta haifi dan dazai iya cin zarafin mace inalilahi waina illahil rajiun! Har yanzu maganar na mata yawo a kai babu wani adalci ko rahama da malik din yacancanta daga gareta shiyasa har kagara take gari yawaye ya dauke aydarh su tafi ko taji sauki da sassauci har ga Allah har cikin ranta take son yarinya har cikin ranta take tausayinta ba karamin mamaki abun ke bata daga malik din har aydarh babu wanda yayi kama da abunda akace sun aikata din amma miye dalilin waenda suka bada shaida akan abun nayi musu sharri bata ga dalilin yin hakan ba shiyasa ko tana so ko bata so sai ta amince ko kadan bata ga laifin aydarh batasan babu abunda ya isa yayi forcing malik ya aikata abunda baiyi niyya babu kudi ko mutanan dasuka isa su sa shi yin abunda baiyi niyya ba, wani irin haushi da daci take ji kan abunda malik din yayi.shagon yashiga suka gaisa sama sama daman kuma wannan halinshi ne sam bai dasakin fuska saboda baya son raini 2k ne kaf kudin shi bai san nawa kayan suke ba hakan yasa shi yin shiru yana nazari kafin yace Malam musa dan Allah pants nake so na mata guda biyu sai sanitary pad kwara daya shi kanshi wani irin nauyi da kunya yaji sadda yayi maganar