← Book details Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 197

Sashe 91

Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

hafsa tace aydarh,Aydarh tace ina kwana auntie ya inna dr hafsa tace lafiya lau y yallabai aydarh tace he is fine auntie yace dasafe zamuje dr hafsat ace alright idan kingama shiryawa ki kirani sai nafito mu wuce bara nakirata yanzu aydarh ta gyada kai kafin tace thanks ta mika masa wayansa ya karba” yace tau mukarasa breakfast din tunda kinyi wanka kaya kawai zaki saka ta gyada masa kai “tea da bread sai fried eggs sukayi break dashi “dakin tashiga bayan sun wanke kayan dasuka bata for breakfast “ black abaya tasaka tayi rolling veil din hadda powder tashafa da kwalli tasaka lipstick wanda yayi masifan yiwa lips din kyau ta saka perfume kafin ta fito da flat shoe shima wani mad black color wanda suka siyo yanda kafan yayi cikin takalmin yah rahamanu ya Allah daga parlor ya dan daga murya yace lokaci naja fa fitowa tayi ahankali tana ce masa ai nagama ma “yah rabbi mikewa kawai yayi yakasa rufe bakin sa ma yazai misilta kyawunta yazai kwatanta kyaun datayi tabarakallah har ta karaso yakasa ko kifta idonsa ahankali ta busa masa iskan bakinta firgigi yayi kafin yashafa kansa yana murmushi yace kinyi kyau tasaukan da kanta tace ka kira auntie wayan yamika mata da kanta tayi dialing number dr hafsa na dauka aydarh tace auntie nashirya dr hafsa tace tau bara na fito takashe wayan “malik yace muje kofan gida sai mujira ta atare suka jera masha Allah duk da jallabiya ne kawai jikinsa amma sai ka dauka shima shiryawa yayi fita zasuyi “he forgets when last yaga Ramlah sai yau kallonsu take kaman zata cinye su malik ya dauke ita kuma aydarh tayi kaman bata ganta ba “suna fita sai ga dr hafsa ta fito malik yace anyi adaidai kenan gaisawa sukayi kafin dr hafsa ta kalli aydarh tace barakallah matar yallabai aydarh tayi murmushi malik ma haka kafin yasaka hannu aljihu yafiddo 10 thousand yamika wa dr hafsa yace ga dubu goma nan idan basuyi ba you should call me sai ko tura muku nayi “dr hafsa tace ahhh yallabai Wallahi yayi har yama wuce aie Allah yasaka da alkhairi malik yace Ameen “keke suka shiga aydarh tayi masa waving hannu shima yadaga mata yace take care love ta gyada masa kai har sai dasuka kusa fita layin kafin yajuya yashiga cikin gida “yau ma kaman ranar matar kaman zata goya su don murna sai taga yau aydarh ta fi rikita ta da haduwa kyau gayu aji “see shape dan Allah kaji kyau malan gawani kamshin kama rasa daga wani duniyar aka aiko sa jikin yarinyar nan babu bata lokacin a fara warware long hair din masha Allah ahankali tace auntie ayi mun wash kafin ayi kitson kawar dr hafsa din tace tau badamuwa ,said aka fara mata wash masha Allah wannan gashin kaman dai sake fitowa yayi ko ?aydarh tayi murmushi dr hafsa tace daman haka yake kin hadu dashi ne shiyasa “zubby tace tau bara a fara daura lallan kafin time din gashin yazama set sai a fara kitson “dr hafsa tace yauwa, aydarh tace ta kalli dr hafsa ahankali tace auntie yace kada ayi black red only,dr hafsa tace ohk tau shknn Jan lalle akafara suna yi suna fira duk da ita dai aydarh sauraron su kawai take duk kuma labarin rashin aure suke “dr hafsa tace ni fa Wallahi kawata baya damuna shi fa aure lokacin ne zubby tace duk da ahaka fa 30something it’s not a joke fa kawata ko ba komai kowa nason yayi auran nan dr hafsa tace haka ne Allah yakawo nagari tace Ameen kusan 1hr ya dauka aka gama zana mata yayi kyau masha Allah bana wasa ba “lokacin gashin ya bushe aka shafa mai “Aydarh tace auntie bazaiyi zafi bako?zubby tayi murmushi ta gyadawa aydarh kai tace in sha Allah “ba zafi ma “Aydarh tace to “kitson aka fara yah rabbil alameen wani irin kanana ne zubbyn ke mata style din shuku mai azaban kyau fatan kan fara tass ga shi hair din very black yah rahaman dr hafsa tace tabarakallah yau yallabai bazai gane wife dinsa ba ina kina kina kitson aydarh tace auntie zafi yake muni dan nayi Allah dr hafsa tace ehhh ai daurewa zakiyi tunda mai gidanki naso aie “ zubby tace eh manah daurewa zakiyi ki dinga yi ni fa everything for my husband duk wahalan dazai bani dr hafsat ace watau biyayya zata kasheki kenan (damsel biyayya zata kasheta 😂🤭)zubby tace Wallahi kam biyayya zata kasheni “Aydarh dai murmushi kawai tayi batace komai ba sun kai 3hrs ana zuba kitson nan fadan ma kalan kyaun dayayi is something different yahadu har yagaji tabarakallah “ dr hafsa sai yaba kitson take bayan angama kafin aka cire lallan “shima yayi ja sosai sai kamshi yake lallan “har yama gaji da haduwa da kyau aydarh dai tasha zama yau har tagaji salla sukayi zubby tace bara nayi manah order abinci dr hafsa ta girgiza kai tace nidai zanyi takeaway a hanya clinic zanje yanzu dr ibrahim bai fiye zama ba saboda gini da akayi busy yake ita kuma nasan mai gidan I will preferred something for her zubby tace tau badamuwa dr hafsa tafiddo kaf kudin da malik yabata tace gashi “zubby tace noo yau anyi sa free dr hafsa tace Wallahi kawata aaaa shi kansa bazai ji dadi ba yafi so ace kin karba “basu suka fita bas ai wajan 3:30 saboda da kyar suka samu zubby ta karbi kudin har a keke dr hafsa nata faman yaba kyaun da lallan da kitson sukayi “sai dasuka kai aydarh har kofan gida kafin mai keke ya wuce da dr hafsa clinic. Tana shiga gidan sukayi clashing da Ramlah saukan da kanta kasa kawai tayi ta cigaba da tafiya Ramlah dawani irin gudu tazo tasha gabanta aydarh ta dakata kafin ta dago tana mata wani irin wawan kallo sai tadauke kai zata wuce Ramlah tasaka hannu ta fizgo aydarh har sai da veil dinta ya zame aydarh da ranta yayi masifan baci ganin yanda Ramlah tasa hannu a jikinta “still bata iya jin zata bude baki tayi ma wannan kazamiyar magana “Ramlah ta washe dawani banzar dariya irin full karuwan nan tace yau gaki gani ke daya “batare da ogan naki ba wanda kike wa mutane iskanci da dagin kai saboda shi” kin dauka kyau gayu aji ko surar jiki ko kuma kyaun fatar da duk ke gareki shi zai saka wata takasa shiga rayuwar mijin naki? Tau Wallahi ganin dama ke bamu yi ba wawiya shashasha “yau zanyi maki bugun dazai kasa gane kamanin ki sai na lalata wannan tsadadiyar abayar jikin naki sai na lalata wannan cikaken kyau da fuskar ki dashi “Aydarh dake mata wani irin wulakantacan kallo from head to toe “ganin bazata iya cigaba da yin shiru ba yasata cewa “as a married women I will never fight with a prostitute like you very low level lady like you ,you are nothing but a trash just allow me to past before I show you bake kawai ne mad ba “Ramlah tayi wata dariya tace oh haba wannan turanci naki ai ko daga British Columbia sai haka “ Aydarh tayi gaba Ramlah ta dinga binta “ har bakin kofan part dinsu kafin ta fizgo aydarh har sai da buga kanta da bangon wurin tabata wani irin lafiyayan mari har sai da jini ya fito kadan ta gefen cute lips dinta nakasa “malik dake parlor yagama girki da duk wani gyaran gida duk da sunyi dasafe sai daya sake gyarawa yanzu after he finished cooking,wanka yafito ya shirya lokacin sallarh la”asar ne daidai ya buda kofan zai fito Ramlah tasake daga hannu zata sake wankawa aydarh second slap “ai billahi ji yayi duniyan nayi masa upset down jiyayi ana hajijiya ana juyasa whatttttt?matarsa ta rike haka zata mara his ASSEIYARH his cuddle bug his everything “dawani irin bala’In speed kaman wani asad (lion)kamar wani wanda zai tashi sama fuskarshi kaman hadari “yasa hannu ya fizgo aydarh da ganinsa yasata fashewa dawani irin dan mahaukacin kuka “malik kam jin kukan aydarh yasa jin zuciyarsa kaman tana barazanar fitowa kaman tana barazanar fashewa “ wani irin wawan fizgar Ramlah yayi ya wurgo ta kasa kafin ya kwance belt din jikinsa ya dinga jibgarka ta kaman jakka ya dinga sa kafa yana harbata billahi yanda yake bugun Ramlah kaman irin yan sanda na bugun rikaken criminal din nan “yah rabbil alameen yanda yake bugun Ramlah kaman daga sama aka aiko sa yin hakan kaman aikin daya zo yi duniyar nan kenan “sai da aydarh taga yana neman halaka Ramlah domin yayi loosing temper ta lura bai san ma abunda yakeyi ba “gashi Ramlah ma har ta suma ma,domin tun tana ihu har ta sume “gidan babu kowa sai Ramlah daman sun fita,barka sai lokacin su maman Ramlah suka shigo gidan suka tarar da abunda ke faruwa wani irin kara uwar Ramlah tafasa,kaman mahaukaciya ta rugu tayo kansu tana jijiga Ramlah ‘aydarh da wani irin tsorata dashi ahankali tasa hannu tajasa suka shiga daki “idonsa kaman zaiyi aman wuta yajawo ta jikinsa yabada wani warm hug “kaman zai hadiye ta cikin jikinsa ahankali yasa hannu yadinga shafa bayanta kafin muryanshi na rawa “yace am sorry mamanarh kiyi hakuri it’s my fault kiyi hakuri dan Allah can’t protect you am very sorry yanda yake ta zuba mata words din he his sorry kaman ya haukaci ahankali ya zare daga jikinsa ta rike hannunsa kafin tace it’s not your fault nayi hakuri amma dukan dakayi mata yayi yawa sir “ajiyan zuciya ya sauke yace yayi yawa?yawa I wished I kill her!!dasauri aydarh tasa hannu tana rufe masa baki ta girgiza kai tace it’s very bad for you to beat a lady ba a dukan mata malik yazare hannuta daga bakinsa yace ita kuma ta dage ki?aydarh tayi shiru kafin ta kwantar da kanta a chest dinsa tana sauraron yanda zuciyansa ke bugawa kusan 5mins malik yaji kafansa har tayi masa wani nauyi ahankali yacireta a jikinsa “kafin yasa hannu yakamata suka shiga bedroom ruwa yahada mata a bucket kafin yafito da very clean towel ya dawo bedroom din tana zaune kan katifa yasa yatsan sa yana shafa inda bakinta yadan fashe kadan ga alaman jini
Chapter 91 · 0% Book details