← Book details Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 197

Sashe 51

Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yace ki tashi ga kayanki nan ki shirya mu tafi wajan wuni bai jira amsarta ba ya fita, kusan five mins bata motsa ba, wani irin azaban tsoron sa takeyi yanzu amma da Wallahi babu abunda zai sa ta tashen toilet tawuce ta sa soap ta wanke fuskanta tass kafin tasa towel ta goge tafito Ledan ta bude ta dinga kallon kayan har sai daga gabanta yafadi saboda irin atamphar ta exactly har sai da taga daga dinkin kafin tasauke ajiyan zuciya ta dai dinga bin atamphar da kallo tau shi yasiya? A ina yasamu kudin wannan atamphar? Ta dai yi shiru can ta ajiye ta nufe wardrobe wasu inners din tasake kafin shafa perfume najiki tasaka rigan sosai dinki yayi mata kyau har sai datayi murmushi duk da tana cikin bacin rai ita da salmerh ke da atamphar tanajin sau daya tasaka shi,shima salmerh ce ta matsa mata tasaka suyi photo suna gamawa kuma ta cire bata sake sakawa ba, powder tashafa sai lipsticks tasaka massacara kafin ta daura kallabin ta yafa mayafin a shoulder side daya tasaka perfume,bude kofan yayi yashigo da sallama ta amsa masa Ko kallonsa bata son yi, ta dauke kai tausayi tabashi ya girgiza kai kafin ya kalli shaddar jikinsa ash itama kuma kayanta ash kamar irin an hada bakin nan,murmushi yayi kafin yace Allahumma bareek you looks good batace komai can ciki tace thank you haka kawai yaji baya son ta fita da veil amma babu yarda zaiyi biki ne sai kuma can murya ba wasa yace ki mayar akai sai data dauko ta kallesa kafin ahankali ta yafa akai,gaba yayi tabisa baya kafin ta harari bayansa tace mugu Allah ranta ‘bakin kofan part din suka fita kaf yan gidan na nan zaune a compound,malik ya mika mata hulan shi dake rike ahannunsa zai rufe part din karba tayi ta rike tana juyo suka ido hudu da Ramlah dakamar zata zauce wajan kallonsu, ba ta sake kallonta ba har yagama rufewa ya juyu yasa hannu zai karbi hulan tak’I basa ya kalleta kafin yace bani hulan manah tayi shiru sai yace ko kadana sa ne?ta gyada kai batare da tayi magana ba yace tau shknn mu tafi fito sukayi yarda suke kallonsu kamar sun samu t.v yarda malik ya Hade rai babu rahama a fuskan sa kawai zai saka shakkar shi,aydarh kau kanta nakasa saboda ta tsani wannan kallon nasu,a kofan gida suka samu keke. Dr hafsa ta kalli aydarh tace ashe zaki zo baki gaya mun ba ai,aydarh tace sai yanzu yace zamu zo bansani ba,dr hafsa tace eyyerh,kafin ta kalli aydarh tace kinga yarda kikayi kyau kam?aydarh tayi murmushi batace komai ba kafin tace naga ma anko kukayi ai aydarh tayi shiru kanta kasa dr hafsa tayi murmushi tace shy shy wannan kunya har tayi yawa ai kafin aydarh tace komai sai ga inna tashigo hannunta rike da plate din shinkafa sai sobo “ ta kalle tace yoo ni asiya ai nayi tunanin baki zuwa, mutane sun cika gida yunwa ta ishe su sun cinye komai ina ma amfani mata ku kwaso yara ku taho wajan hidima saboda kawai a ci abinci kamar jikokin kamtaka ina ma dalili aydarh batace komai ba sai murmushi kawai takeyi dr hafsa ta kalli inna tace tau ke miyayi ruwanki ba ina gayyatar su akayi? Inna tace yau naga jafa’I daga ina kike kuma? Dr hafsa tamike tace aydarh sai kin fito bara naje naga nr saratu tashigo yanzu aydarh tace to inna tabi bayan dr hafsa da kallo tawani tabe . Inna tasake baki tana kallonsa kafin tace aaa kai kau audu baka da tsoron Allah taya ma zakace taje su gaisa dawata katuwa Bayan zuwan ta kenan yanzu Ko abincin bikin ma bata ci ba banda ma Allah yataimaka jarababbun da aka gayyata nayi kokarin samo abincin basu karasa cinyewa ba, malik yayi shiru kafin yace aa inna zata ci a can dakin ma “inna tayi mitsi mitsi da ido kafin ta kalli aydarh tace, kodai bai gane abunda nake nufi ba?aydarh girgiza kai tayi murmushi tace ah’ah fa inna ki ajiye zan ci anan,inna ta tabe baki tace ku dai kukasani ai ni bana kaunar wahala shiyasa ta dinga yawo ana biki kuma ga ciki kasan mai ciki ba’ason tana zama da yunwa Allah, aydarh tayi kasa da kai malik ya dinga kallonta ko kiftawa babu,inna ta mike tace ahh nikam bara nafita naga alamarin naka kaf babu kaunar ma’aiki a ciki miye wani kaman zaka fadawa yarinya, shidai malik bai ce komai ba wani irin kunya yaji kamar zai ruga Allah ya taimaka ma ba kowa,har inna tafice kafin yayi kasa da murya yace Hala daukanki zanyi ?bazaki taso ba,batace komai ba ta mike tsaye tana gyara yafin veil dinta wanda ta mayar a shoulder sai kallonta yake bai ce komai ba yayi gaba ta bisa abaya ,rabiah zuciyanta fitowa kawai ke batayi ba amma yanda take bugu kaman zata fito bilki kau idonta har bushewa yayi wajan kallon aydarh already sun ga malik har sai da rabiah tadawo daga nata shock din tasa hannu ta bugu bilki,kafin bilki tace bala’In nan kawata Allah yayi hallita a wajan nan ke kiji sequences a jikinta kuma fa babbar kalli shantili dan manzon Allah kawata ji wannan uban gashi shi kansa ture kaga tsiyan ji fa yarda tawani kifan dashi a kanta yoo wai wannan yana ma ganin wata bayan ita kam?rabiah ta banka mata wata shegen harara tace uban haka ai Wallahi banga wani abunda tafi wani ba,bilki ta gwalo ido tace ke kau bakin ciki ne aljalinki Wallahi,rabiah tayi tsaki tace zaki tashi mu bisa da abincin har can bangaran yayah ibrahim din gabanta ko nayi tafiyata?bilki ta mike tace aa Wallahi kawata gabana zaayi komai ni wallahi tsoronsa ma fa nake rabiah tayi dariya tace ai babe fuskan nan ba wasa bilki tace waye haka? Rabiah tace shi yayah malik din bilki tace owoo na fahimta, ahankali suke tafiya har suka isa bangaran amarya wanda aka cikin gidansu dr ibrahim din ne aka deba akayi mata gida daidai mai kyau furnitures din ta daidai karfin su masu kyau bangaran tsit shiru babu kowa sai kamshi sabon paint da sabon furnitures dr ibrahim ne tsaye yana waya bakin parlor malik ya dinga binsa da kallo kafin ya kashe wayan,dr ibrahim ya kalli aydarh yana murmushi kafin yace ina wuni madam?ya gida kuma?aydarh ta dago tace ina wuni Doctor Allah yasa alkhairi Dr ibrahim yace lafiya lau Ameen Ameen nagode sosai,malik yace kuma bazaka iya wucewa daga nan ba sai ka nuna halinka? Dr ibrahim yace yanzu fa nazo nan din kuma yougurt ma nakawo mata bata ci abinci ba, malik ya kalli Aydarh kafin yace ki shiga tana ciki batace komai ba tawuce sallama tayi ahankali daga can hibba ta amsa mata har bedroom din tashiga kafin hibba ta fito da kanta daga cikin hijab din da ta rufe jikinta pink sai lace din jikinta ash mai touches din kasancewan ta fara yasa tayi kyau masha Allah ga idonta ya bushe alaman tayi kuka,tayi murmushi kafin aydarh ta zauna kan gado hibba ta gyara zamanta tace Aydarh ko? Aydarh ta gyada kai kafin tace sannu amarya ina wuni? Hibba tace Alhamdulilah yakike? Tace alhamdulilah hibba dai sai kallon aydarh take yau dai sai ta tambayi dr ko dai larabawa ne mutanan hibba idonta Still akan aydarh tace ah dole yayah malik ya dinga daukewa mata kai a can ashe yasan abunda ya ajiye a gida tabarakallah aydarh na murmushi kafin tace ah’ah fa,hibba taji dadin shigowan aydarh daman tun dazu ita kadai ce har wani sanyi taji da dr ibrahim yace mata yanzu aydarh zata zo,tace amma daga qatar kuke ko saudiyya ba? Aydarh ta girgiza kai tace ah’ah a Adamawa muke,hibba tace kai haba har ina cewa sai na tambayi Doctor yau,aydarh tayi murmushi tace basai kin tambaye sa ba tafada tana dariya,hibba dai sai kallonta take bakaramin burgeta tayi ba nan hibba taja aydarh da fira kaman irin sun saba din nan itama aydarh sai taji tafi sakewa da ita more than dr hafsa duk da ita hibba ta girmeta amma bazai fi da shekara biyu ba kawai,duk da hibba ke kawo labarin tana da saurin sabo sai labari take kaman ba itace amaryan ba,can ta kalli aydarh tace nikam wannan turare naki tunda kika zauna naji kamshin sa yayi mun dan Allah anan ake siyarwa?aydarh tace ah’ah shi yasiyo ma,amma idan kina so sai nabasa yakawo miki hibba ta rike baki kafin tace aaa ah gaishe ki yasiyo abun dan ki dinga sawa sai ki bayar aaaa gaskia,aydarh taware ido tace babu komai fa shi baya ma magana bazai ce komai ba Allah hibba tace aaa dai kawai ki gaya man sunan sa sai Doctor yasiyo mun wannan ai dole yallabai ya dinga lallibe Ko cikin jama’a ne tafada tana dariya aydarh dai batace komai sai murmushi da tayi dan bata fahimce hibban ba. Dr ibrahim yace tau mu shiga sai ka fada mata said aran zaka zo ku tafi lokacin mun dawo ko?malik yace tau muje har bedroom din suka shiga malik yasake gaisawa da hibba tana mashi tsiyar wannan hurul ‘in haka shiyasa yaki yanmatan garinsu kenan dr ibrahim nataya ta shidai malik murmushi yake kawai kafin yace nafahimce mijin da matar halinku guda Allah ya yaye muku tau, dr ibrahim yace ba Ameen ba da karfi duk akayi dariya ita dai aydarh kanta na kasa sai faman smile take, rabiah dake tafiya kaman irin fashionista din nan ansha straight gown ta lace maroon da coffee wanda sukayi irin daya da bilki na wunin bikin ga uban parking gel anja kallabi baya makeup dinsu duk tayi melting saboda zufa,rabiah tafara shigowa dakin sannan bilki sunata wani kamshi mai karfi irin na karamin perfume din nan dan robber dr ibrahim dake magana da hibba yabi su da kallo malik kau bai dago ba haka ma aydarh da duk ya takura mata yanayin zaman kaman zai shige cikinta ko kunya baya ji ma, rabiah tace ina wuni auntie hibba ya gajiyan hanya bilki ma tace haka hibban na murmushi take amsa su kafin ta mayarda dubanta kansu malik har sai da gabanta yafadi kafin ta daure bilki dai
Chapter 51 · 0% Book details