Sashe 14
Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sauya yasa oum fahimtar bacci yadauke shi,ahankali ta kwantar dashi kan gadon tareda rufe shi da duvet zuba masa ido tayi tana kallonshi ko zatayi karya kan komai banda soyayyar dake wa habib wani irin so take mashi wanda ita kanta basan adadin shi ba , har yanzu kallon yarinya yake mata ko dawasa bai taba hada ta dawata mace ba a rayuwarshi duk girman kai izza wulakanci dakuma isa ta abba idan yana gabanta komawa yake tamkar yaro ganin yarda yake bacci da alama sam baya jin dadin shi yasata zare veil din da ta daure kanta ta ajiye kwanciya tayi saman gadon itama ta shigewa jikin shi. 7:35 daidai ummi ta kammala pepperoni catfish din da kewa aydarh yaji kayan kamshi sosai sai kamshi yake a warmer ta juye mata shi ta kwashe sauran a plate ta hada da bread aka mikawa hajajju, hajajju dai sai kallon ikon Allah take can takalli aysha dake warware mata ledar bread din tayi kasa da murya tace ahhh gaskia a Lamarin asiya akwai gyara mamadin ta tayi ma ita yarinyar horon yunwa shine ta dage ta rasa inda zata tsoma rayuwarta tun dazo ta daura waccan ta sauke waccan an mayarda gida kamar rastaurans Ahh tau mu dai ba ruwanmu iyaka a dafa a debar manah namu rabon ahtau aysha batace komai ba har tagama warware mata bread din ta ajiye ta tashi bin bayan aysha da harara hajajju tayi tana kallon maryam,tace duk cikin su naga ke kadai ce kawai ba tababba ba ,hala a mutanan gidan akwai mai sasirikat din hauka Allah natuba bai dan ba zararru ba kana magana kowa ya dinga ma shiru, dariya kawai maryam keyi batace komai ba tace tau minene wani sasirikat? Certificate fa ake cewa kuma ma naga ke ina ruwanki ba an dafa an baki kinci ba miye wani abun complain ? Hajajju dai abunda ke gabanta tacigaba da ci bata sake bin ta kan maryam ba. Ummi tace zauna ahankali ASEEYA ki daure ki ci ko kadan ne bayan spaghetti din nan dakikayi cokali biyar babu abunda fa kika ci aydarh dai kanta na kasa bata sha’awar cin komai domin cikinta ma cunkushe yake can ummi tabude flasks din ta tsiyaya kunun a cup tamikawa aydarh karba aydarh tayi Still bata sha ba sai kallon kunun take ummi tace daure ki sha zaki ji dadin jikin ki, ahankali ta kafa cup din a bakinta tayi sipping kunun har cikin ranta taji zafin kunun yayi mata dadi Sosai a baki ba i ta ta ajiye ba har sai da tasha rabin cup kafin ta ture sannu ummi tayi mata tareda mika mata bowl din da ta zuba mata pepperoni a ciki shima dai bata ci dayawa ba ta ture, kallonta ummi keyi ko kiftawa babu da alama dai halinta ne na kin abinci bata takura mata ba da dole sa ta cinye ta rabu da ita, so take suyi magana so take ta fahimce wani abu daga bakin aydarh amma bata san taya ba a ganinta yakamata a bar aydarh ta huta da taso mata maganar amma idan tayi shiru kila wannan ne dama nakarshe dazata sake samun irin wannan lokacin ita da aydarh hakan yasa ummi fara magana cikin hikima da dattako tace ASEEYA! Aydarh bata dago ba kanta na kasa kuma bata amsa ba ummi na lura da ita a wunin dasukayi tare ta fuskance abubuwa da dama daga halin aydarh, “”hakan yasa ummi cigaba da magana “” bansan kaddarar da ke sake bibiyar rayuwarmu ba basan ta yarda komai yafaru ba a wannan karon kila wannan ce hanyar da muka jima muna addua akai,a kullun adduar mu shine daidaito da kuma gyaruwar tarwatsewar da ahalinmu yayi ,sai sannan aydarh ta dago kai ta kalli oum dasauri kuma ta mayar da kanta kasa wani irin nauyi da kunyar ummin take ji,ganin abunda datayi yasa ummi kamo hannunta tace Allah shike kaddara duk abunda zai faru da bawa tun kafin fitowar shi daga cikin-cikin mahaifiyar shi duk abunda yafaru yau da ma wanda zai faru har abada yana cikin littafin rayuwarmu,wani birkitacan alamari ne mai wuyar fassarawa nayarda da kaddara nasan cewa wannan wani hanyar ce Allah ya billo manah dashi domin mu karyata tunaninmu da kanmu domin ya nuna manah iyakar mu akan zunubin da mahaifinki ya saka mu,mukuma mu kabada hadin kai wajan aiwatar dashi ZUMUNCI ba abun wasa bane amma ahaka muka sa kafa muka ruguza mafarkin kakanin ku! Hawaye ke zuba a idon ummi,share su tayi tacigaba dacewa ASEEYA nasan baki san suwaye mu ba a cikin mu bayan ABDOOLMALIK sai hajajju kawai kika sani, ni nice mahaifiyar ABDOOLMALIK Wanda kika ganmu tare shine mahaifin shi kuma yayan naki mahaifin uwa daya uba daya wani irin zabura aydarh tayi tareda mikewa tsaye hankali tashi tace yayan abbana kuma? Daman abbana ba da wani dan uwa? Zaunar da ita ummi tayi tace ki kwantar da hankalinki ASEEYA yanzu ba lokacin sanin komai bane na fada maki wannan maganar ne domin kinsan waye malik a wurinki domin ki san su waye mu, aydarh was shock and speechless at thesame time iyakar abubuwan da zasu firgita mata tunani ba wanda bata gani ba a yau har zuciyarta ma ta kai da bushewa ta riga da ta sallama komai na rayuwa a yau din nan shiru tayi kawai tana cigaba da sauraron ummi. Malik yayi shiru yana sauraron hajajju har takai aya tace tau sai kayi hakuri ka rungume kaddara ka yafe man amma kaji duk yarda akaiyi sannan ta fashe da kuka tace tau bacin ma ba kaunar Allah ni miye laifina dan matan can sun gaya man abunda kayi nikuma na gayawa ubanka an daura muku aure da yarinyar sai kuma tayi kasa da murya tace wai kau kaga kenn yarinyar da zaka dinga bakin rai kana irin wannan mugun abu dan Allah yataimake ka na shige maka gaba an baka auranta ? Yanzu taimako daya zanyi ma nagaya maka garin dazaka ku dinga istigifari Allah ya yafe muku,tashi yayi ya fita domin bazai iya cigaba da sauraron hajajju ba “daidai zai shiga daki yaga ummi tafito rike da hannun aydarh wace ke tafi ahankali tamkar bata son taka kasa, yarasa miya aiko ta cikin rayuwarshi ya rasa hadin kaddara da yahada shi da ita kalmar ciki yamaimaita a ranshi wai yayi mata ciki har ya zube an kuma daura masu aure a yanzu haka wai fa matar shi ce !! Da sauri yashige daki ganin ummi na kokarin juyuwa abunda bai sani ba shine tunda yafara kallon su ummi ta lura da shi . Shiga sukayi dakin hajajju tamike tsaye ta dafa kirji tace wacece wannan? Ummi dai tayi shiru ahankali ta zaunar da aydarh kan cushion din dake cikin dakin tace barka da dare , hajajju tayi shiru tayi kamar bataji ba tace tau waennan rubbbun dasuka samu gaba suna kwala manah idanun kamar larabawan daji bazaki sallamai su ba ki kirawo ibrahin da audul din ba? Fita su halime sukayi kafin ma ummi tayi masu magana malik tasa aysha takira mata sannan ta tafi dakanta kiran abby, tsaye yayi kamm bakin kofa ya sukunyar da kanshi kasa, can sai ga ummi tashigo abby na biye da ita duk zama sukayi abby nama hajajju barka da dare fuskar nan tashi babu yabo babu fallasa kallo daya yayiwa aydarh yadauke ido takure take zaune a dakin kamar wata baby ta lafe jikin cushion din alamar zazzabi da kuma tasowar asthma dinta take ji daurewa kawai take amma ita kadai tasan halin da take ciki,hajajju takalli malik da kauda kai still a tsaye yake bai zauna bas ai kanshi da har yanzu na akasa “Tace ibrahin akwai wani bawan Allah can a kano a rimin auxunawa yake aikin gini yake shine nake rokon alfarma ka taimaka kabar audul ya dauke matar tashi su tafi can kano din yabashi aiki da dan kuturun gida su zauna suyi rayuwar su a can babu wanda yaji babu wanda yagani sai kuma tayi kasa da murya tace saidai ayi mai wonin kafin su tafi kar aje can yarabu da yar mutane a shiga uku saboda gaskia habibu ba yarda zaiyi ba wannan karon dai nasamu na tankwara shi ya hakuri da yanzu duk muna can muna zance da karkata kai a caji opus,bayan abby yagama sauraron hajajju tass sannan yace tau ba laifi hajiya ko 5 seconds bai kara ba ya tashi ya fita,hajajju ummi ta bishi da kallo , tarin da aydarh keyi ahankali yasa shi dagowa ya zuba mata lion eyes dinsa ko kiftawa babu wannan ne karon farko da ya tsaya yana kare mata kallo dasauri ummi ta nufeta tana mata sannu domin ganin yarda take rike kirjinta, hajajju tace tau nan daka tsaya kamar dan karota kana kare mata kallo baza ka iya taimaka manah da komai ba ko duk abunda kuka yi bai. So babyn habeebe’kuna neman uniques turaran wuta,turaran dana kaya baki daya? Tau faduwa tazo daidai dazama 💃🏻come one come all to real scent ,haddadun mata,manya mata,yan mata da zawarawa baki daya kuzo mu hadaku ku dinga musulmin kamshi,kamshi marar tadda hankali kamshi mai kwantar da hankalin bawa and munada room fresheners masu kamshin oud just dm me and purchased urs ❤ Duk abunda kukayi bai ishe ku ba sai ka dinga zuba mata ido kana kallo shidai bai ce komai ba ya juya ya fita daga dakin, sannu ummi ke ta jera ma ta ba karamin tausayin ta ummin ke jib a tasan tunda take bata taba shiga irin wannan yanayin ba “taga kokarin yarinyar sosai, har tarin ya lafa hajajju na gefe tana wurga ido,can tace tau wai wannan wani irin tari ne ko daman bayan anyi bari tari na biyo baya? Ummi dai batace komai still tana kan aydarh ta jata jikinta tana shafa mata baya kusan 7mins kafin ummi takama hannunta suka koma dakin ummi, sannu ASEEYA kinada asthma ne? Gyada kai aydarh tayi batare da ta amsa ummin ba,gyara mata kwanciya ummi tayi still tana kallonta, addua tashafa mata kafin tashiga toilet ta dauro alwalla.Kiran sallarh asuba yasa ta bude idonta ahankali tana bin fuskar abba da kallo,yatsanta daya ta daura kan lips dinshi tana zagayewa ahankali shima yake buda idonshi