Sashe 76
Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ai gashi yafito da karamin towel a hannu yana goge sumanshi alaman wanka yayi kara tafasa tana saurin saka rigan shidai mutuwan tsaye yayi yana kallonta kawai “kafin ya lumshe ido yana cigaba da yamutsa suman kanshi billahi Ko kallonta yayi sometimes sai yayi loosing shiyasa yanzu kullun cikin wanka yake kaman duck, tana gama sakawa ta juya masa baya gabanta na sake faduwa ita dai tashiga uku yariga da yagama da ita yanzu inda yayi saura bai gani a jikinta ba bai da yawa gashi ko kunya kallonta bai yi ahaka ita ko da singlet da boxers bata iya kallonsa,hawaye ya taru a idonta tana turo baki bai ce mata komai yazo yabude wardrobe ya fiddo jallabiya yakasa kafin yakoma toilet din ya shanya towel din yafito, shimfidansa yayi ya kwanta yana juya mat abaya itama can karshan katifan ta koma ta kwanta tayi lamo tana rufe har kanta da duvet sai kusan bayan 10mins kafin yamike ya tafi kitchen maganin daya siyo jiya yasake sha yadawo yakashe wutan ya kwanta. Tunda gari yawaye haka kawai yaji sa duk wani kala bazai ce fargaban haduwa da dr usama bane aaaaa kawai tunanin makomar rayuwarsa yake idan ya cigaba da zama ahaka zai halaka kanshi ya lura ita yarinyar har yanzu da sauranta dole ya ajiye nashi miskilancin domin shi ke cutawa ba ita ba sonta na neman kasara shi, duk wani aikin gida atare suka yi sa yau,ruwan tea kawai suka dafa taci basai sunyi breakfast bas ai su hada da cake din “tun safe ta lura da yanayin sa duk bayan seconds sai ta kama sa yayi shiru yana satan kallonta,yanzun ma nan suke kan carpet ‘ suna breakfast duk tana lura dashi yanda yake shan shayin kaman an ma sa dole yayi shiru looking so disturb,ahankali ta matsa kusa dashi tace sir “nakara ma ka sugar a shayin ne? Sai sannan ya dago ya girgiza mata kai kawai,takasa dauke ido kanshi ita fa seeing him like this didn’t suit her mind, tayi shiru kafin can tace are you sick? Ya girgiza mata kai kafin ahankali yaja long pointed nose dinta yace am okay dear just eat badan ta gamsu ba kawai dai ta gyada masa kai, domin bata son takura sa, wayan shi yayi ringing yana dubawa yaga dr ibrahim ne picking call din yayi suka gaisa kafin dr ibrahim yace dr faisal yakira ka?malik yace aaaaa bai kira ba, dr ibrahim yace kila wani abun ne ya dauke masa hankali malik yace ba mamaki, wani abu?dr ibrahim yace no yace muje after isha’I lokacin ne dr usama yace muje din “malik yace tau Allah yakaimu dr ibrahim yace Ameen kafin yace mu hadu bakin clinic zai fi kusa right?malik yace ohk kafin sukayi sallama yakashe wayan “Aydarh na juya teaspoon din hannunta cikin kofin shayin takallesa tace ko nasake hada ma wanda babu madara? Yace eh hada mun mikewa tayi ta nufi kitchen after five minutes sai gata tafito da wani kofin rike ahannu a gabansa ta ajiye kafin tasa sugar ta mika masa karba yayi idonshi kanta yace thanks cuddle bug ‘tayi murmushi kadan tace anytime sir “mayar mata yayi kafin ya cigaba da sipping shayin kadan kadan itama p cake din ta cigaba da ci,hankalin ta nakanshi haka nan taji bata son ganinshi a wannan mood din. Ta dinga bin kofin shayin da kallo ganin ya ajiye ko rabin shayin bai yi ba,kallonsa tayi fuskanta cike da damuwa “tayi kasa da muryanta tace you are not okay sir just tell me what’s wrong please,malik yayi murmushin karfin hali ya girgiza kai kafin yace am okay dear ,tayi shiru tana dai kallonsa amma bata tasake cewa komai ba shima bai sake magana ba yayi shiru ya lumshe idonsa tunani fal aransa, can ta mike ganin kaman shayin ya ishe sa don ya ma barsa har ya huce, kwashe kayan tayi ta wuce kitchen ta kai sai ta wanke kafin ta sake goge kitchen din ta fito ‘ ta sake kallonsa for few seconds, kafin ta dauke kai ta shiga bedroom din kan katifa ta zauna jikinta a sanyaye haka kawai tasamu kanta da rashin jin dadin yanayin dayake,ahankali tazame ta kwanta tana rufe idonta zuciyanta na mata ba dadi, kawai seeing him in suchs situation duk sai taji itama jikinta babu dadi,duk bayan few seconds sai taji kaman ta tashi taje ta duba sa sai kuma ta zauna kasa hakura tayi kawai ta mike, walking very slow tabude kofan tana kallonsa zaune yake yahada kansa da gwiwa,ta dinga kallonsa ko dauke ido babu,gently ta dinga tafiya kaman mai counting steps dinta har ta karasa kusa dashi ta zauna kafin tamika hannunta ta dago kansa, ya zuba mata idonsa yana kallonta kaman wanda ke ciwo, tace sir wai mike damunka hannu yasa ya jawota jikinsa ya kwantar da kanshi a shoulder dinta,ahankali yake sauke ajiyan zuciya yana fesar da numfashin mai zafi a wuyanta lumshe ido tayi tana sauraron bugun zuciyanshi kusan 30minutes suna ahaka babu mai magana cikinsu kafin gently ya zare ta daga cikinsa kaman wani ciwo yakara ma kanshi mikewa yayi yawuce toilet ta dinga kallonsa ko kiftawa babu yanda yake tafiya kaman wanda yayi ciwo, har sai da yashige toilet din kafin ya janye idonta,mikewa tayi kawai ta shige bedroom. Tace tau ai bansan baka son chili dayawa a noodles ba,yayi shiru kafin yace ai ba yawa yayi ba kawai dai ina jin zafi kadan kadan a chest dina,tace ko dai ulcer ne sir? Malik ya girgiza kai yace ai bana jin sign din ulcer kawai dai yanayi ne tayi shiru tana kallonsa kafin tace to na Chanza maka wani abincin ko shayi? Ya girgiza kai yace zan ci ahaka ai kin sha aiki kuma just rest now tace “to”shiru yayi yana cigaba da cin indomie dinsa, kafin can yadago kai su hada ido tayi saurin dauke kanta,murmushi yayi kadan yana girgiza kansa this is not the first time a yau da ya kamata tana kallonsa sai kuma idan suka hada ido tayi saurin janyewa tana pretending as if ba kallonsa tayi ba,kanta kasa ta cigaba da fidgeting fingers dinta,ita bata masan ya akayi ba those this kawa isai ta shagala tana kallonsa yana dauke mata kewan abbanta sosai saboda kama suke ba nawasa ba da abba,karasa cin indomie yayi yasha ruwa,kafin ya mike da plate din zai kai kitchen dasauri ta mike tana karban plate din tace sit sir I will do it murmushi yamata ahankali yace thanks cuddle bug, batace komai ba ta karasa kitchen takai plate din kiran salla la’asar yasa shi mikewa yashiga toilet sai dayayi wanka kafin ya dauro alwalla yawuce masallaci, itama dakin tashiga tanada alwalla sallarh ta kabbara. Farin shadda dasuka dinka a auran dr ibrahim yasaka “ kayan cikin kawai yasaka bai daura babban rigan ba,ita dai sai satan kallonsa take ya bude kwalban perfume dinsa ya fesa,Allahumma bareek billahi malik ko yaron qatar president sai haka he looks more than handsome,yayi wani irin kyau kaman balarabin qatar, black shade yasaka yah rabbil alameen, yafi kyawu kyau “Aydarh dai takasa hakuri,muryanta very calm tace sir ina zakaje?da har zai jata sai kuma ya tuna wani abu sai yafasa,yajuyu yakalleta kafin yayi cute smile yace zamuje wani waje da Doctor,aydarh tayi shiru kafin ta gyada kai ta cigaba da wasa da yatsun hannunta, har yakai kofa zai bude kafin ya juyu yace say a prayer for your handsome husby “Aydarh tayi saurin janye kanta kafin tace Allah yadawo da kai lapia “yace Ameen yace tau kuma baki ce nayi kyau ba ,murmushi tayi ahankali tace Tabarakallah masha Allah Allahumma bareek yayi murmushi yace Ameen yah rabbi sai nadawo take care waving hannunta tayi masa kafin tace you too.kaman yanda suka tsara haka malik ya tarar da dr ibrahim bakin clinic yana jiransa,Doctor ibrahim dai yakasa rufe baki yana kallon malik ‘yace ni wannan kyau haka karka firgita mata kano fa,wannan kyau haka kaman dai zamuje gasan kyau ko hula ya bazaka saka ba kenan nan gaba zaka dinga parking gashin nan naga yau suman yafi kama da nalaraba ko indiyawa ma zance,malik yashafa kansa yace it’s already late muje kawai baka rabo da abun dariya, keke suka samu har nasarawa G.R.A aka kai su bakin wani mad mansion aka ajiye su,malik dai yakasa dauke kansa daga gidan,bawai kauyanci yake ba aaaa kawai dai gidan yayi masa kama da gidansu Aydarh dr Ibrahim ya kallesa kafin yace kodai kiransa zamuyi da kyar securities din gate dinnan su barmu mu shiga,malik yayi shiru kafin yace no kawai muje maybe yana tare da iyalinsa fa,dr ibrahim yayi murmushi yace ai baida iyali shi malik dai yayi shiru amma yana mamakin magana dr ibrahim din,hanya hadaddan gate din suka bi,yayi knocking securitie yabude yana kallonsu already dr usama ya sanar masa da zuwansu, murmushi yayi yabasu wuri suka shigo gaisawa sukayi kafin yace su jira sa nan yaje ya sanar masa,bayan security yatafi dr ibrahim yakasa shiru,yace yallabai kaji gida kaman baa mutuwa kuma fa daga sh isai securities dinnan suke rayuwa ko maids babu idan baya Nigeria su kawai ke zama a gidan nan fa,malik yace Allah sarki “kafin yayi shiru shima dr ibrahim shiru yayi can sai ga securitie yadawo kafin yawashe baki yace bismillah ku iso,daga bakin gate din zuwa main entrance din gida Akwai tafiya ba laifi tunda gidan kusan anguwa guda ce, malik da ya lumshe idonsa tasbihi yakeyi har suka isa cikin wani babban parlor dake nan kaman show room wani mahaukacin royal cushions ne a parlor babu hayaniyan kayan decoration sosai sai babban t.vplasma dake aiki koi na kal kaman a turai babu dirty ko kadan sai kamshin wani freshener mai sirin kamshi ke tashi a parlor ga a.c dake nasa aikin securitie yace musu bismillah ku zauna yanzu yashiga cikin in the next five minutes zaku gansa ya fito shi yace ku shigo dr ibrahim yace tau badamuwa mungode, securitie yasa takalman shiga kitchen din tsaban zaman turai yasa ko ‘ina zaka shiga a gidan da shoes din wajan kitchen din yashiga kafin yabude fridge din ya fiddo da fresh apple green manya masu kyau yayi sliced dinsu kan wani clean bowl sai daukan ido yake kaman irin sabo dinnan dagani