Sashe 47
Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
,yace inyee tau yayi dadi? Tace yayi fa auntie ma tace yayi dadi sosai yace wacece auntie? Tace auntie hafsa yayi murmushi yace kinyi kokari, littafin ki fa kin duba? Ta gyada kai tace erh naduba, Yace tau sai anjima “tace “to” kashe wayan yayi kafin ta ajiye wayan ta mike tsaye tadawo parlor tana jiran dawowan dr hafsa, knocking akayi aydarh tabude tasan dr hafsa ce shiyasa bata ma tsaya tambayar waye din ba, tana budewa taga inna tsaye tasha mayafi ga uban jikka ta rataya aydarh na ganin inna tayi murmushi kafin tace oyoyo inna “andawo lapia ya hanya? Inna tayi shiru bata amsa Aydarh ba kafin aydarh ta bata hanya tace shigo inna “anan parlor suka zauna kafin tace ina wuni sai sannan inna tace lahiya lau asiya, ya gidan? Aydarh tace Alhamdulilah inna dai tayi shiru ta tsuke baki ta zubawa waje daya ido aydarh ta mike tashiga kitchen ta kawo mata ruwa da abinci ta ajiye, inna ta kalli abincin kafin ta dauke ido,aydarh tace inna lapia? Inna tace duniya tazo karshe asiya aydarh tayi shiru tana kallon inna kafin inna tayi kasa da murya tace fisabillahi yanzu ita hafsa miye ruwanta dazuwa na wajan dangi na sabga? Aydarh tayi shiru bata ce komai ba kafin inna tace tau nida yanzu idan audu na nan ki shiga ki kira man shi nakai kararta wajan shi gaskiya,aydarh tace kiyi hakuri inna ita auntie mi tayi maki? Inna tace rashin mutunci da wulakanci sai wanda ta manta kawai ke batayi mun ba ,ina cikin fameli kawai ta kirani wai nataho ruwa zai mun banna, dayake ita kowa yayi shaidar bata kaunar Allah “ina dawowa gidan babu abunda yafaru “Aydarh tace gaskia ba dadi “ inna tayi kasa da murya tace shiyasa kingani bana shiga abunda yashafeta babu ruwana da ita “yanzu tashi ki shiga ki kira mun audu ya bige Mata wonin,babu ruwanta da rayuwata tunda nima bana shiga rayuwarta “Aydarh takalli “inna” tace ki yiakuri baya nan ma “inna tayi shiru kafin tace yana ina shi audun? Aydarh tace sun tafi auran Doctor ibraheem “ inna tace wanene haka kuma?aydarh tace wanda suke aiki clinic daya da auntie hafsa inna tayi shiru tace ibrahin wai? Aydarh tace erh shi, inna bata sake magana ba ta cigaba da cin abinci ta, har tagama kafin ta kalli Aydarh tace hafsa din tazo nan?aydarh tace erh amma yanzu ta tafi zata dawo anjima inna ta tabe fuska tayi yi shiru.malik yace tau ai baki daya zamu tafi ba?dr ibrahim yayi shiru kafin yace eh ai an riga da anyi jere so babu need din kuma ace hadda wasu yan rakiyan amarya,kawai da ita kawai zamu tafi malik yace tau Allah yakaimu asabar din “dr ibrahim yace Ameen “ , da sallama yaron yashigo hannu shi rike da jug da cups ya ajiye kafin yace ina wunin ku? Dr ibrahim yace lafiya lau malik ma ya amsa, can dr ibrahim yakalli malik yace naji baka kira, ta ba yau malik yayi wani murmushin gefan baki kafin yace ai nasan yanzu safiya ce dr hafsa na clinic ita babu waya hannunta “ dr ibrahim yace eh haka ne dazu nurse saratu ma takirani malik yace ohh, ringing wayar malik tayi number ce ke ta kiransa tun jiya baiyi niyyar dagawa bas ai kuma yadaga yayi sallama daga can aka amsa cike da yanga tace ina wuni ranka dade bai gane mai magana ba hakan yasa shi cewa lafiya, kafin tace ya nasarawan? Yace Alhamdulilah “kafin tace sunana rabi’ah kanwar dr ibrahim abokinka malik ya dage giranshi kafin babu yabo babu fallasa yace oh Allah sarki ykuke? Tace Lafiya lau alhamdulilah kafin yace ga ibrahim din,dasauri rabiah tace aa bashi nake nema ba kai nake nema daman nakiraka naji ko ranar daurin auran dawuri zaku taso saboda ayi muku girki dawuri saboda abokanan ku kamar bai gane tambayar datayi masa ba “ yace okay “ tasake cewa dawurin zaku taso? Ehhh kawai yace mata kafin yakashe wayan tacigaba dacewa hello hello taji shiru takalli bilki tace yafa kashe wayan bilki tace ai Alhamdulilah tunda wahalar mu bata tashi abanza ba daman malan yace ko sau dayane kukayi magana dashi shikenan aikinmu yaci,rabiah tayi wani irin tsalle kafin tace Wayyo dadi waya ga rabiah a matsayin matar bawan Allahn nan kafin ta mike tsaye tayi wani juye tana fari da ido, sai kuma ta zauna tana kallon bilki tace bilki matarsa fa?bilki ta tabe baki tace tau ke miyayi ruwanki da ita? Rabiah tawani zaro ido kafin tace baki da hankali bilki baki da kan gado kin kau san yarda take wannan yarinyar? Wllh ganin kanki zaki dinga yi biri idan kina kallonsa shida matarsa wallahi,kinga duk kyau yayah ibrahim dashi yabiyo iya ko?tau komawa yake wani kwa’do kwa’do bilki ta babake da dariya tace amma fa rabi baki da mutunci yayah ibrahim din?rabiah ta saukan da ajiyan zuciya tace bazaki gane bane bilki wallahi ko a mazan indian flim ban taba ganin mai irin haduwar shi ba kin ga tsawon sa kam?kinga fadin sa kam?ke Wallahi kalan fatar sa ma kawai ya isa ya ruda mutun bama kiran jiki ko kyaun fuska ba wand ani ban ma san yarda zan misilata miki kyaun sa ba, bilki ta saki baki tana zara ido tace kai haba ? Ita fa matar? Rabiah ta tabe baki,kafin tac eke wannan yarinyar fa tsoro zata dinga baki ban taba ganin abu mai kyau irin taba ke billahillazi ban iya ma hada ido da it ani kwarjini take mun ga isa raini hankali da shegen girman kai wai kinji muryarta da yarda take tafiya bala’In nan “bilki dai sai binta takeyi da kallo tace Allah natuba rabiah kuma shine kike son kai kanki inda Allah bai kaiki ba?kiji yanzu fa tsabar girman kai da isa ko sallama bai maki ba ya katse kira ke ko amsar kirki bai baki ba ‘anya rabiah bazakiyi ma kanki fada ba? Ki fta harkan su kiji yarda kika bani labarin abayan jikinta fa kika ce hannunta hadda diamond rings biyu ga dayan English gold kin kau san ko a can kasar wajan sai babban mai kudi ke siya?rabiah ta mike tsaye tayi ma bilki wani kallo tac eke Wallahi ko ma mi zai faru sai dai yafaru amma idan kika ga baayi auranmu dashi ba sai dai idan mutuwa nayi ko shi ya mutu, bilki ta rike baki tace tauuuuuuuu ban taba sanin abun har yakai haka ba yanzu ki tashi mu wuce kasuwan yarda zamuyu cefanan da wuri har mu hadu ma iya danata wanda zasuyi na wuni,rabiah tace tau shknn mutafi sai mu siyo kayan sobon ma baki daya tunda malan yace a zuba masa maganin a sobo bilki ta dau mayafin ta tace tau mu wuce kinga daga nan ma sai muyi wankin kan a daura man bakin lalle tunda munyi jaa rabiah tace tau shknn mu tafi. Dr hafsa tace kinga yau nace mata zamu zo,aydarh tace erh ‘dr hafsa tace idan muka je can aka saka miki lallan sai na warware miki calaban a wanke maki gashin right?aydarh ta gyada kai kafin dr hafsa tace tau ki shirya tunda munyi breakfast basai munyi lunch a gida ba a can munyi nima bara na shirya nadawo yanzu inna ta wuce gidan iya,aydarh tace ina ne haka?dr hafsat ace ohh gidansu dr ibrahim wajan biki sai angama biki tadawo nidai sai gobe in sha Allah wuni kawai zanje aydarh tace Allah yakaimu dr hafsa tace Amin kafin ta mike tace sai nadawo kiyi sauri ki shirya kema,aydarh tayi murmushi tace right now auntie dr hafsa tayi murmushi, dr hafsa na fita tashiga tayi wanka kafin ta fito ta shafa vaseline da powder kadan sai kajal a idonta tasaka lipstick kadan shima kafin ta dawo dinki da tabaro gida sanye dashi a jiki yarda fitted gown din ya zauna a jikinta sai taga kamar na yau yafi na kullun kafin ta shafa perfume ta fito da well iron baby pink din hijab dinta ta ajiye kan katifan dan kwallin kayan ta dauka ta daura shi akai masha Allah “ knocking kofan akeyi tayi tunanin dr hafsa ce tafito bata ce waye ba kawai ta bude kofan, tunda ta bude suka zuba mata ido kamar sun samu cartoon kallon su tayi kafin tace ku shigo Wallahi bilki duk tunanin aydarh bata kai kyaun haka ba duk sai taji sun muzanta duk yarda suka taho suna wani yauki, bilki dai takasa dauke idonta akan aydarh ta dinga kallonta ko kiftawa babu ga wani masifan kamshi dake neman zauta su,Rabiah tace sannu kin gane ni ai ko tafada tawani irin fizga kaman irin yan local champions dinnan (yan ghetto idan zasuyi abun yan gayu lol🤭) aydarh tayi wani irin abun da ido cike da isa ta tsaya bakin kofan ta rike Handle din ta girgiza kai bata ce komai ba kafin rabiah tace sunana rabiah kanwar dr ibrahim abokin yayah malik ,aydarh tace ohh ku shigo ta basu wuri takalmin su suka cire suka shiga yarda aydarh ke tafiya bilki ta dinga bin da kallo duk ta sha jinin jikinta da niyyarsu sai sunyi abunda zai ma aydarh ciwo tun yanzu tasan rabiah naso malik, kitchen aydarh tashiga zata kawo musu ruwan rabiah nata wani tabe baki bilki ta dafe kirji tace rabiah see shape dan Allah wai kinga yarda take tafiya kiji maganar ta fisabillahi,rabiah ta bangawa bilki harara ta dauke kai,fitowa tayi hannunta rike da plate din ruwa sai fruits da tayi musu slicing bilki ta washe baki tace ina wuni bamu gaisa ba babu yabo babu fallasa aydarh tace Alhamdulilah “ rabiah dai kamar zata mutu dan bakin ciki,kamar zai kasheta, aydarh tawuce bedroom tayi zamanta,kusan ten minutes suna zaune bilki nat asha kankana ita dai rabiah ko abu daya bata dauka ba, knocking akayi aydarh naji adduan ta daya dr hafsa ce domin haka nan taji batasan zaman su a gidan,fitowa tayi walking slowly ta isa bakin kofan kafin tace waye? Dr hafsa tace nice budewa aydarh tayi kafin tace auntie tun dazu nashirya fa, dr hafsa tace sorry sai danayi ma babyn neighbor din mu allura aydarh tace eyyerh kafin ta bata hanya suka shiga parlor dr hafsa