Sashe 55
Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ba itama bata sake magana ba,ta tashi ta koma kitchen, kusan 20mins sai gashi yashigo kitchen din hannunsa rike da bakin leda kwara biyu ya ajiye ya fita,ledan ta bude salad ne sai tomotoes da cucumber da green pepper dayan ledan ta bude taga five eggs sai gasasshan kifi babba kwara daya, Fido su tayi daga ledan kafin ta wanke shinkafan da ta sa a ruba ta zuba a tukunya salt tasaka sai ajino moto kaman yanda taga yayi ranan, one hour thirty minutes yadauke ta kafin tagama abinci lokacin har ya tafi sallan magrib daki tawuce itama tayi sallarh kafin tadawo kitchen ta gyara shi tass kaman baayi girki ciki ba, knocking akayi tasan shi ne ta bude, parlor ya zauna ta wuce kitchen,yarda yake kallon abinci kaman yau ne first time dayafara ganin irin sa, can yace kinci abinci ta girgiza masa kai tace ah’ah sai mundawo “ya ajiye spoon din hannunsa yace ina zamuje?sai sannan tace ohh auntie ce bata da lapia zamuje dubata hadda ita nayi girkin ma shidai malik bai ce komai ba yacigaba da cin abincin sa ,har sai daya kusa gamawa kafin ta wuce gida,bayan yagama ya kwashe yakai kitchen kafin yawanke bakinsa ya wuce masallaci, tunda tagama sallarh ta fito da warmer nan parlor tana jiran shigowan sa sallama yayi ta amsa kafin ta mike tace muje ? Malik yace aaa. Tace ah”ah fa kace tafada tana kallonsa,can yayi kasa da murya yace eh aaaa babu inda zamuje kaman zata kuka tace to ai sai natafi ni daya “yace tau shknn sai kindawo har ta dauki warmer tanufi hanyan kofa kafin yasa hannu ya jawota ta dawo baya kaman zata fashe da kuka tace masa “miye haka kikeyi wai? Bai ce komai bay ace miyasa baki tambaye ni tun jiya bas ai yau? Tace ai namanta ne kuma aie shiyasa nace naje ni kawai tunda kai baza kaje ba , malik baice komai ba yasake ta ya dauki warmer din, yayi gaba tana ganin yafita tayi saurin biyo sa rufe kofan yayi suka jera tare suna tafiya, dasauri ta iske su kofan gidan duk irin warnings din shi baya shigan ta tunda ta biyo su Aydarh ke lura da ita shima ya ganta amma sukayi tafiyan su,har sun kusa gidan inna kafin tace yallabai tsayawa malik yayi kafin ya juyu yana kallonta,cike da kilbibi tace ina wuni? Ya aiki malik yace Alhamdulilah ykk?ai yau Ramlah kaman zata mutu tsaban dadi wai malik ne ke ya tambayarta ya take,tawani shagwabe masa kafin tace not fine “yace eyyerh mike damunki? Yah rabbil alameen Aydarh juyawa tayi kawai ta cigaba da tafiya “ bata tsaya sauraron su ba malik nagani ta juya daman saboda gabanta ne yayi haka shima ya bi bayanta saboda bazai iya cigaba da magana da Ramlah ba yau ma sa’a taci kawai akwai abunda yake so yayi ne yasa shi magana da ita,anan zauran inna ya tarar da ita alaman bata shiga ciki ba jiransa take hade rai yayi zai wuce ta sa hannu ta jawo ya dawo kafin ta bata rai ta hau saman wani dan dakali dake nan zauran yanda tsawon ta zai kamo nashi duk da ta hau din bai kamo ba amma ahakan tasa hannu ta kama kunnan sa ta wani ja,ba zafi yaji ba amma sai dayayi yar kara bata saki kunnan ba tace idan ita bata da hankali tasake ma magana a waje “ tasaki kunna kafin tayi wucewan ta ciki ya kusa 5mins nan a tsaye yana maimaita magana “har bai so ta saki kunnan ba shafa kansa yayi yarasa miyasa yarinyan nan bata tsoronsa ba, wani zuciya tace itama ke tsoronka amma sturbborness dinta bai barin ta dinga jin shakkar ka,yanda maza da mata ke shakkansa ke tsoron sa a gida daya shigo kowa zai nutsu haka ma mutanan waje ko a kanon ma sosai mutane ke girmama sa saboda kwarjini dayake musu amma ita aydarh rashin kunya sai wace ta manta ke bata yi masa (kaji karya😂😂) binta yayi cikin gidan inna na zaune tsakan gida sai faman wanke zogale take,malik ya duga kusa da ita ya ajiye warmer kafin yace innana ni kadai “inna ta washe baki tace audu ashe hadda kai nayi tunani ita ce kawai ya girgiza kai yace waya na tsaya amsawa,inna tace oho ‘malik yace ina wuni inna ya gida?ya mai jiki kuma? Inna tace ah lafiya lau yakuke? Malik yace alhamdulilah inna ta rage murya tace nidai baa haka dani Wallahi malik yace tau mi yafaru? Inna tace ban sa fa tana ciwonta ba sai dai naji takira shi saurayin nata likita ne shima ai na baka labarin sa ko? Malik yace ki gaya mun wannan wanda yake da mata ko? Inna tace eh shi,can babba asibiti yake aiki ai malik yace oh oh Allah sarki,sai fa kawai naji ance tazo can asibitin kar taje tasu wai ayi maidical chakof, malik yace a ina zaayi mata medical checkups din? Inna tace can babbar asibiti fa malik yace tau ai hakan yafi kila ba malaria bace kawai maybe ma hadda stress na wajan aiki inna dai tayi shiru bata sake magana ba ta cigaba da wankin zogalenta malik yace suna parlor?inna ta gyada kai yace tau bara nashiga na dubata warmer yasake dauka yashiga parlor dr hafsa na kwance kan three siter sai aydarh dake zaune kan one sallama yayi ya ajiye warmer dr hafsa ta tashi zaune kallo daya zakayi mata kasan bata da lafiya duk da taji sauki amma tadan fada, gaishe sa tayi ya amsa yana yi mata ya jiki ta amsa nan kujeran da aydarh take ya zauna duk one siter yasan bazata ishe su ba amma neman rigima yasa shi zama,dr hafsa na gani ta janye ido “ Aydarh kam wani kallo tayi masa kaman zatayi kuka tana nuna mashi direction din dr hafsa kaman ma bai gani ba yasa hannunsa ta cikin hijab dinta yana kama wrist dinta yarike gam,Wallahi kaman zatayi fitsari saboda zafin dataji har sai datayi kwalla amma ta daure,duk abunda yake dr hafsa na kallo ta fuske tana godiyan abinci bata iya amsa taba saboda kunyar datake ji kaman zata nutse a wurin dr hafsa ta mike tace bara, na juye daman dazu nagama ce ma inna tayi mana ta dinga fada wai dambu za tayi malik da kaman bai san miyayi ba yace, sannu dr kinsan halin yan kayanmu ai,dr hafsa na murmushi tafita mamakinsa ya cikata,a rai take fadin “maza fa basu da kunya daman wannan yarinya yarda take ai tabani dashi ko da kau cikin mutane ne, dr hafsa na fita tasa hannu tana kokarin ciro hannunsa dake hijab dinta hawaye nabin cheeks dinta tace what’s all this sir? Malik yaware ido yace what? Wani abu akayi ne? Still hannunsa na a hijab dinta yana shafa bayanta,tace ka cire idan auntie tayi tunanin wani abu fa? Yace tau hala ita auntie batasan ni mijinki bane? Aydarh tace amma aie babu kyau , yace minene babu kyau kuma? Tace abunda kakeyi din, yace eyyerh na daina tau yafada yana fito da hannunsa daga hijab dinta tace to ka Chanza wuri yace right now ma yamike yafita daga dakin baki daya yana komawa wajan inna, dr hafsa tadawo aydarh tak’I daga ido ta kalleta dr hafsa ta girgiza kai tana murmushi kafin tace kwantar da hankalinki babysis su fa maza babu ruwansu ki daina damuwa ma,sai sannan aydarh tasa hannu ta goge hawayenta tass kafin tace auntie kiyi masa magana “dr hafsa tawaro ido tace maganan mi? Aydarh tana wasa da hannunta tace matan nan kullun sai tayi masa magana hadda ma abinci tayi masa dr hafsa na kallon aydarh ko dauke ido babu yarda take magana cike da yarinta zaka san bawai kishi bane aaaaa kawai tsantsar shagwaba ne bata saba sharing abu da mutane ba tun asali, komai nata nata ita daya “ shiyasa bata son yana magana da Ramlah, dr hafsa tace kiyi hakuri idan naji sauki sai nagaya maki abunda zaayi, bani ce zanyi masa magana ba, ke ce zakiyi masa kinji koh?aydarh ta gyada kai tace na fa yi masa auntie amma bayaji har fa tambayanta yakeyi ya take?tafada tana bude ido tareda turo baki dr hafsa ta kwashe da dariya, tace tofa,aydarh tabata fuska tace shine kike dariya auntie?dr hafsa tace ai ke ce da ban dariya kinsan miyasa bai daina ba?aydarh ta girgiza kai dr hafsa tace kiji yanda kike masa magana in a childish manner kinsan idan kina masa warning haka har wani dadi yakeji,Aydarh tace Wallahi ranan har abinci na hana sa sai daya bani tausayi kawai nabasa kuma shima sai dayace nabasa saboda umminsa, dr hafsa duk da bakaramin dariya abun yabata ba amma ta daure tace kai haba? Aydarh tace Wallahi,dr hafsa tace daga yau kar nasake jin kin hanasa abincin the worst part ma ki hanasa jikinki kinji Aseeya? Gabanta yawani irin fadi saboda statement din dr hafsa na karshe,batace komai ba ta sunkuyar da kanta kasa, dr hafsa tace kinga last time har sai daya kwana asibiti duk laifin da zai maki karki na hana kanki kinji Ko aydarh idan bahaka ma malikun rahama zasuyi fushi dake,and abinci ma ki dinga basa kinji babysis? Aydarh duk da Hankalin ta yatashi ta daure tace “to”dr hafsa tace promise me bazaki sake ba Aydarh da kaman zata fashe da kuka can cikin throat tace I promise “dr hafsa tayi murmushi tace yauwa yar albarka Allah yabaku zaman lafiya yakawo cutes twins masu kama da ku,aydarh dai tayi shiru tana sauraron yanda gabanta ke faduwa har sai wajan ten suka tafi time din inna tagama kwada zogalan ta sawa malik a warmer suka tafi dashi. Tace sai fa nayi contacting world health organization,malik yace tau ko na ma baki aron wayana ki kira can din yanzu? Aydarh tace you thinks am kidding you ba? Malik yace no Aydarh tace to Wallahi dana kirasu nayi karanka kayimun allura while kai ba likita ba ba nurse bas ai sun ji miyasa,malik yace kai haba hala tunda nayi miki alluran baki cigaba da tafiya ba? Aydarh tawara ido tace kusan ten days fa kenan jira nayi ayi two weeks idan naji wani abu to,malik dai kamar yayi dariya he