← Book details Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 197

Sashe 7

Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sosai duk wani kurakuran su sun gyara kuma alhamdulilah Allah yayi masu baiwar fahimta da kuma gane karatu hakan nada nasaba da tarbiyya mai kyau da kuma good background din karatu dasuka samu saida suka sake maida komai mahallinshi a gidan kafin suke shige daki su kwanta (yan uwa a kula dan adinga kauda komai kafin kwanciya bacci kama daga takalmi kwanuka dasauran su saboda mutanan boye dare shine time din hidimomin su kuma suna iya sakar ko wacce kalan cuta a jikin kayan amfanin mu)zaune suke shi da abby da ummi a dakin abby din murmushi abby yayi yace tau ka daure kaje manah tunda dai an zabe ka kamar tumun dare shima murmushi yayi kadan yace in sha Allah abby zanje ummi tace ahtau kafin kuma ka jawa kowa cikin saboda kasan halin yan kayanka Sosai sun dan bata lokaci suna fira sallama malik yayi musu yawuce daki ko daya shiga dakin sake fitowa yayi waje yayi alwalla domin yana san raya daran yana sallarh,sai wajan 2:30sannan ya kwanta Gyara daurin kallabin ta tayi tareda matse biredin dake hannunta wanda yaji kwai Sosai ga roman kai dayaji kayan kamshi a gefe sannan tayi kasa da murya kamar mai tsoron wani yaji ta tace wai yaya hof kin fahimce duk yarda na shirya filan dina koma kallonta baaba kulu tayi tace na fahimta hajajju kuma na gamsu Allah yasa komai yatafi daidai Ameen tace sai ta cigaba dacewa wai kuma yaya babu son zuciya da cuta a lamarin nan a ba wannan mutumin auran wannan yar yarinyar ina ji pah yayi talatin biyar zuwa hamsin haka baaba kulu dai tayi mata shiru saboda tasan idan ta biyeta yanzu zata cigaba da maganganu babu kai babu kugu tace ahtau ai maganar gaskia akwai bakin Mugun abu a zuciyar ku daza kuyi wannan abu nidai babu ruwana sabo hwa da Allah babu ruwana tau ni miye hadani ma da lamarin dinku bacin anyi zancan gabana kuma an nuna inda muhimmanci a lamarin da mi zai kaini shiga wannan sabon da shirka ita dai baaba tayi shiru kamar bata dakin cigaba da breakfast dinta tayi ta ba banza ajiyan hajajjun dan ma dan uwa na dan uwa bacin haka mi zai sa nazo gidan mata ta dinga dinki fusa kamar buss din cikin fim daga an bani wani gutun biredi ina ci Allah na tuba da a kano ne iyakar abunda zan ba almajirin makōta kenan still dai baaba bata kulata sai ma kwashe plates din da tagama kalaci da tayi tabarwa hajajju dakin few minutes itama ta fito dauke da kwanukan taci ta koshi sai hada zufa take tamkar babu celling fan a dakin tsabar ci ne yasata zufa ahankali tace tau kina ganin yana shigowa zaa kira ita uwar yarinyar itama ta turo ta ko kuwa ehhh haka zaayi tunda ai dole sai an hadasu waje guda sai ki tura so can gidan shi dan baban yarda kowa zai fi yarda idan aka gansu tare koh?gyada kai hajajju tayi tareda ballar goro tasaka baki tana tauna Kona 1 minute bai runtsa ba gani yake safiya takiyi yanayin da yake ji da kalaman zarah watau oum sun bada gudunmuwa Sosai wajan rikita tunanin shi yakasa fassara kalamanta da abunda yake ji a jikinshi da zuciyar shi bitar su yake daya bayan daya ganin zai rikitar kanshi da tunaninshi yasa shi shafawa kanshi lapia kiran farko na asuba har yagama shiryawa duk wani abunda zai bukata tun jiya ya shirya shi already yagama da aikin daya kawo shi kasan daman sai karashe karashe P.A dinshi yayi ma handling duk wani abunda ya rage tareda fada mashi kiran gaggawar daya samu daga gida Daga gida tsaf ya shirya kanshi cikin shadda dinkin kaftani tayi matukar karbar jikinshi yafito bafullatanin usuli cikin sassarfa yafito daga dakin babban hotel din idan driver shi ya ajiye motar ya nufa bai san dalilin dayasa yake ji wannan yanayin ba yaso yake yakira oum yagaya mata yanzu zasu taso amma yafi son kawai gaya mata gashi idan sunyi landing.Ahankali take kurbar ruwan shayin baki daya takarasa jigatuwa rufaidarh ce tsaye akanta bayan ta taimaka mata tayi wanka ta shirya ruwan tea din shine abu nafarko da aka samu zata sha tun wayewar garin kuka take mai karamin sauti domin azabar sake karuwa take tace ma auntie rufaidarh takira mata doctor ashraff tace baya nan yayi tafiya ta daure tasha magananin in sha Allah zataji sauki da sallama oum tashigo dakin tunda tashigo ta zubawa aydarh ido ko kiftawa babu rufaidarh ma dai oum take kallo tasan daurewa kawai take amma ba karamin zafi zuciyarta ke mata ba jurewa kawai take amma Allah kadai yasan halin dake ce a yanzu da fara’a suka gaisawa da rufaidarh tana tambayar ta ya mai jiki Alhamdulilah kawai rufaidarh tace taja bakinta tayi shiru babu yabo babu fallasa oum ta amsawa aydarh gaisuwan da take mata tana tambayar ya jikin nata Alhamdulilah kawai tace tacigaba da kurbar ruwan shayin kallonta oum tayi tana fesar da numfashi tareda laushe ido addua take kasan ranta kafin ta tattaro duk wani kwarin gwiwa da karfin zuciyarta cikin sanyi muryar tace idan kin gama ki shirya ai kinsan idan baaba ko?dan bude ido tayi har gabanta na faduwa tace wace baabarn?harara oum ta watsa mata tace ai kinsan duk fadin Abuja baaba daya kawai ke akwai murmushi rufaidarh tayi tace aaa uktiee ki bita ahankali baby baaba kulu take nufi saukar da ajiyan zuciya aydarh tayi tace yeah I know cigaba oum tayi da magana idan kin gama in the next 10mins ki fit ozan aike ki har cup din hannunta na barazanar faduwa lokaci daya tari ya sarqe ta tace oum wannan anguwa gidan baabarh ni kuma tafada tana nuna kanta saurin girgiza kai tayi tace gaskia oum ba zanje wannan anguwan ba and I didn’t see the reason of going there tafada har cikin ranta domin ita a tunanin iyakar gaskiarta kenan sanin kan oum ne bata zuwa gidan baaba idan ma har taje tau yazama dolene oum ta tirsasa mata su tafi din kuma ko data je ma bata iya zama a gida tsaye take tsayawa har su taho idan kuma suka dawo gida ta dinga tsanar kanta kenan da kayan datayi amfani baki daya ranar duk wani kalan shower gel da turaran dake kan Mirror dinta sai ta yi amfani dasu a jikinta cikin tsawa da daga murya oum tace ASSEEYARH rike ta rufaidarh tayi tace kiyi ahankali uktiee cikin masifa oum tace tau nabaki 10mins ki shirya ki yi driving da kanki saboda ma’aikatan gidan nan baza su cigaba dayi maki bauta kina wulakantasu as if there are your slaves am I cleared saukar da kanta kasa tayi tareda gyadawa oum kai words aydarh shine abunda oum tace,yes ma juyawa oum tayi tabar dakin fadawa dakinta tayi tafashe da wani irin raunannan kuka mai taba zuciya Allah astagafirrullah Allah ka yafe man Allah kaga zuciyana yah rabbi kaga niyyana yah rabbi ka tafiyar da abunan cikin sauki ya rabbi kabani ikon cinye wannan jarabawar yah rahaman kasa kada muyi duk wannan shirin a wofi yah rabbil alameen kasa ko da ba duka burikan mu kwara biyu ba yah arrahamar rahimin ka cika mun daya kuka tacigaba dayi tamkar anyi mata mutuwa,Tau auntie mi zanyi acan din auntie kiji tausayina ki bata hakuri auntie I hate that area I can’t even imagine seeing only me a wurin nan auntie please bazanje bah rage murya rufaidarh tayi tareda jawo aydarh a jikinta cikin sigar lallashi tayi kasa da murya tace baby kiyi hakuri kinji kiyi hakuri kinga mahaifiyarki ta baki umarni kinsan halinta kuma ko ni bazan iya hanata abunda datayi niyya ba and after all aydarh ai kinga bawani zama zakiyi acan din bah hajajju fa ce tazo miki da magani tace kuma dole sai ke da kanki zakije karba saboda ka’idan maganin ko bakya son ki warke ne?ita dai aydarh bata ce komai kallon rufaidarh kawai take kamar mai son gano gaskiyan maganar tunda oum tace taje gidan baaba kulu gabanta ya cigaba da bugawa kamar ana buga mata guduma,amma auntie ba zan iya driving ba nasani aydarh daurewa zakiyi ai daga yau in sha Allah keda wannan ciwon kuma shikenan still aydarh was so confused tau miyasa sai ita zataje karban maganin tau kuma ance dokan maganin kenan can kuma ta bata fuska tareda dan tabe baki tace auntie gaskia bana son maganin while nama san traditional herbal ne girgiza kai rufaidarh tayi tasan halin aydarh zuma ce saida wuta tace mata no normal magani ne bana son sake jin komai tashi kije ganin itama auntie rufaidarh ta daure yasa aydarh tashi anhankali kamar bata son taka kasa dangeshi take domin har yanzu kafaffun ta da maranta azaban ciwo suke gaban mirror ta tsaya tana kallon kanta tasake fresh amma duk tafada closet tabude ta dauko wata mad dubai abaya magenta ta chanza inner wears magenta wani hadaddan soft lace form brassiere tasaka tareda pant da undie duk magenta din tabarakallah, fitowa tayi ta kalli rufaidarh sannan tace uhm auntie ina key din mota yake murmushi rufaidarh tayi ganin irin yanda aydarh ke ba’bata rai tace yana wajan oum bara naje nakarbo maki ki karasa shirya kiyi sauri amma kafin 10mins din yakarasa cika toh tace ta dauki lights perfume masu fitar da musulmin scent ta fesa a abayar tareda saka lipgloss kadan a kananun lips dinta sai qyali suke, fizgar mota tayi mai gadin gidan nasu naganin itace yayi saurin bude mata gate yana mai mata adduar shiriya ga yarinyar har yarinya ko alarabawa da wuya asamu mai zubin ta Allah yayi halitta a wajan nan ina ma ace Allah yay ini mai kudi da babu abunda zai hanani auran yarinya kai idan na aureta ko fita waje nagama yi habu,habu yace ni ji nake ina ma kullun zan dinga kallonta da angama man komai a rayuwa tahada komai amma saidai kash wannan halin nata na wulakanta dan adam yafi komai cim un tuwo a kwarya sule mai gadi yace hmm habu ke nan yarinyar duk abunda tayi tace tayi kuma gado girman d’a shi kanshi uban haka yake dandai ance dan gado sai yayi zarra haka suka cigaba da
Chapter 7 · 0% Book details