Sashe 4
Da So Kamane Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kwantar da halinki very soon zaki koma school your holiday is over mah self kinji baby ita kuwa rufaida kibar ni da ita dasauri tace wait abba ynx kasan da kace zaka kore anty rufaida oum mah fushi zatayi tace saida su tafi tare kaga lets fine another solution Abangaran malik kuwa tashi yayi da safe ya fara gudanar duk aiyukan da zama dawaniniyyar shi a gidan har gari ya karasa wayewa jama,a suka fara kai kawo domin gudanar da kasuwancin su Abby ne zaune kan clean mat din radio a gefenshi yanaji morning news su aisha da ummi na ta faman hada break fast wanka yafito dakinshi ya nufa ya kintsa kanshi yayi matukar kyau ya taje sajenshi tareda kafa hular p-cap ta zauna dass a kanshi kusa da abby ya zauna domin yana son magana dashi tare suka cigaba sauraron news din har aka kammala sannan abby yayi gyaran murya yace Malik ina son a kullum ka kasance mutun mai hakuri da juriya da jajircewa akan komai malik duniyar nan ba Komai kake nema kasamu bah kasance mai hakuri a duk idan ka samo kanka kada ka taba cutar da wani wai dan yana karkashin ka cikin gamsuwa da maganar abby malik ya ce in sha Allah abby nagode Allah yasaka da alkhairi yakara girma murmushi yayi sosai wanda sai da naga kamar shi da Alhaji habib har yaso yafi da malik Ahankali take takawa tamkar wace bata son taka tiles din dakin har ta karasa gaban bedside dinta ta dauke wayar ta yau ne karo na farko a rayuwarta da zata kira salma da kanta ba ita ta kira taba Ba tare da ita salman ce takirata bah dialing number salman tayi amma har tanuna call ended ba a dauka bah tsaki tayi tareda jefan da wayan Karo na baadadi oum tasake saukar da ajiyar zuciya tareda fesar da numfashi yanda gabanta ke buguwa har kana iya hangowa tacikin riganta Rufaidah ce tsaye akanta tana tofa mata adduo’in samun sassauci wajan mahalice mikewa tsaye Rufaidah tayi ban tagama yi wa oum dukkan azikarin datasani wanda zai sa zuciyan ta sanyi kallonta oum tayi tareda kiran sunanta nagaskiya ,Rufaidah ma kallon oum tayi tabbass tasan anzo gabar da yakamata kaddara da kuma gyaruwar alamurra su pah taka rawa a rayuwar aydah hakika anzo lokaci da rayuwar sauyi dakuma gyara ta pa wanzuwa a duniyar aydah mafita daya ce kuma hanya daya tal wanda zaya sa ququwar sauyi da tarbiyya mafi inganci su fara taka tasu rawar a fili dakuma zahiri na rayuwar aydah dukkanin hanaye biyu na oum Rufaidah ta rike cikin natsuwa soyayya irin ta yan uwan asali Rufaidah tafara wa oum magana, Uktieee anzo wajan lokacin yayi amma kafin wanzuwar komai sai kin jure sai kin daure da duk irin matakin da zamu dauka domin shine mafita ta har abada a rayuwar aseeyarh kallon Rufaidah oum keyi cikin tsantsar son jin wannan mafita wanda tasan duk dunia bayan Allah Rufaidah ce kawai zaran dazaya daure mata duk wani matsalanta idanunta dasu kayi laushi ta zubawa Rufaidah tace uktie bana shaka ko kuma fargaba akan duk abunda zaya faru indai abunda muke so zai faru indai abunda muke nema zai samu! Murmushi Rufaidah tayi tace uktieee komai zaya faru yanzu zai zamo sanadin abu guda biyu tunuwa da hakan da oum tayi yasa taji kashi tamanin na damuwanta yarage amma uktieee wani hanzari bah gudu bah abban aydah fa murmushi itama oum tayi tareda cewa wannan mai sauki ne uktieee tashi tsaye Rufaidah tayi tace yau zamu fara duk wani plan namu sosai oum takara samun kwarin gwiwa da kuma karsashin aikata duk abunda ta tsara wanda abu ne wanda zata jifi tsuntsu biyu da dutse guda Ranar baki daya wunin malik yayi a kwance sanadiyyyar alamu dayafara ji na tasuwar ciwon shi bbu sunayan Allah dari ba daya yake ta faman ambata domin bai ga ranar dawannan ciwo nashi zaizo karshe bah duk wani kokarin da abby ke son yi sam malik bai bari saboda yasan cutarwa ce dakuma cuta ga duk Wani d’a da abby ya haifa saboda a ganin malik din wani karin nauyi ne dakuma dawaniya ga abby din Allah shaidane irin wahalar da cutuwar dayake a duk sanda ciwon ya taso abby ne da ummi kawai ka kwatanta halin dayake shiga wanda bayan Allah su kawai suka san da ciwonshi sai shi da yabar wa kanshi sani bai da abokin daya zamar mashi na jiki kuma aganin shi wannan ba kamar irin normal ciwo bane daya kamata kowa yasani tunanin ne fal aranshi har bacci yayi nasarar kwashe shi .Abby ne zaune kan prayer mat sallarh nafila ya idar wanda shafa adduar shi kenan tun dazu yake lura da ummi ganin kamar akwai magana bakin kasancewar ta ba kasa fai tafiye magana ba har sai idan maganar tazama mai ma ‘ana dakuma amfanin cikin natsuwa da haiba dakuma kamala irin ta dattijan kwarai cike da so yace mata tagari uwa tagari kuma sirika tagari in Allah ya yarda tamkar mashi ya soka mata azuciya kamar wani fami yayi mata a tsohon ciwon dake ranta tamkar soso mata idan yake mata kyakya yayi har ga Allah wani irin abunda ya dirar mata arai wanda take kwana take tashi da dawainiyyar shi arai hawaye suka fara zarya bisa kuncin ummi wanda ba karamin dagawa abby hankali yayi bah Kallonta abby yakeyi babu kiftawa shiru yayi tamkar mai nazari kaf kalaman shi baiga idan yayi kuskuran zance ba wanda zai saka zuciya da kuma ran ummi bace ba kallo yake mata irin na mamaki da alajabi kallonta yake har sai da tagaji da kanta tayi shiru gyaran murya yayi tareda da fara magana ahankali tamkar wanda yake kan gabar ban hakuri a laifin daya aikata banyi tunani ko zaton a duk cikin kalamai na akwai wanda zai bata ranki ba ummin malik share hawayenta ummi tayi cikin karaya da tarin rauni tace abbyn malik duniya gudu take kwananki karewa suke abubuwan kullun tsayawa suke babu sauyi har sai yaushi har sai wane lokaci komai zai zamu daidai har sai wani lokaci komai zai dawo bisa mizani rayuwa tazamo manah kamar busar sarewa duk yanda iska ya kada haka sautin fitar busar zaiyi damu tunda tafara maganar yake juya kalaman nata kamar mai bita ko kuma hadda su akai, cikin karfin zuciya da tarin kwarin gwiwa yace ina ji a jikina lokaci yayi ban san ta ina ba ko ta wace hanya bah amma adduar damuke tana gab da karbo wa mu bar wa Allah komai kallonshi kawai ummi keyi bstareda ta amsa ba ko fahimtar kalaman da yake amfani dasu wajan maganar bah hankalinta sam baya tareda dashi.Tashin yayi cike da karfin hali da kuma dauriya sakamakon kira mafi daraja a duniya dayaji kaf massallanta anguwar tasu ta dauka ahankali yake tafiya har yakarasa bakin kofar dakin shi daidai ummi na fitowa daga dakin domin duba jikin nashi kasancewar tasan idan ciwon yafara lafawa bacci ke daukar mai nauyi da nisa hada ido sukayi taga lokaci guda yafada irin fadawar da ciwon ke saka shi yi cike da tausai take jera mashi kalmar sannu da adduan samun sauki kallonta yayi ya amsa mata yana nufar hanyar bayi saida yayi wanka tass sannan ya daura alwalla zuwa yanzu Alhamdulilah jikin nashi da sauki shiryawa yayi cikin cream jallabi mai matukar kyau wanda tafito da ainahin kyauwunshi na hausa fulani karfafan kirar jikin dayahade da tsawon shi wanda ke kara fito da asalin kwarjini da haibar shi takawa yake ahankali da kuma nutsuwa har ya shiga cikin massallaci ko bayan angama sallarh zaunawa yayi ya cigaba da azkar yana jiran lokacin magrib wanda tun farko dabi’ar malik din ce ahaka. Kasancewar fita suke so suyi cikin sirri hakan yasa oum da kanta driving motar hankali take juyawa fararan yatsun hannunta da suka sha ado da jan lalle dan asalin kasar sudan duk bayan seconds take sauke ajiyar zuciya duk abunda take rufaida tana kallonta wanda itama kusan hakane addua kawai takeyi Allah yasa matakin dazasu dauka ya zamu silla da kuma sanadin daidaituwar komai har suka karasa anguwar dake dauke da gidaje waenda ke nuni da tsarin anguwar ta masu karamin karfi ce sauka sukayi daidai kofar wani madaidaicin gida hankali suke takawa kowa da abunda yake rayawa a ranshi Tafiya take tamkar wace wani ke counting steps foot dinta tafiya take cikin nutsuwa aji kamala da kuma tsabar kwarewa a gayu har takai gaban wardrobes dinta wacce ke dauke da tsarin kaya tamkar ana shirin bude boutique wata grey abaya ta fiddo batada hanyani sam amma kuma tayi musulmin kyau komawa tayi bangaran underwears dinta ta fiddo wata black lace form bra tare pants dinta tsaba ta shirya kanta Yah rabbil alameen! Yah rabbil alameen!A koda yaushe tamkar ana kara fiddo da ainahin kyauwunta ne tamkar ana sake kera hallitar tane kyauwun jiki dana fuska hade fata tamkar rabawa akayi ta zaba gayun da jikin nata ya hadu dashi ke sa duk wani bawan marmarin kallonta ko da sau dayane wanda hakan ba karamin cutar da ita bane sam bata son mutane bata so hayani bata son duk wani abunda ya shafi mutane towards her Mirrow ta maida kallonta tashi tayi tareda sauke ajiyar zuciya fuskarta ta dan bata kadan tareda turo karamin bakinta hannu ta mika tareda daukar uniques perfumes dinta wanda tsabar kudi aka sa aka siya ANGHAM ALHUM,Dhahab Arabiyat sune asalin turaran da take amfani dashi wanda tun daga kan shower gel dinta face cream body cream shampoos soaps toothpaste hand cream dinta duk na company Dhahab dinne shiyasa ni’ima da asalin kamshinta wanda ya cukude da natural skin scent dinta yake bada wani ni’imtacan kamshi mai saukar da nutsuwa game da kantar da hankali tunuwa tayi batayi sallan la’asar bah dasauri tamike tana turo baki saboda tasan yanzu oum zata shigo tafara mata fada baki da sallarh da alwalla basu wuce 3mins har tayi tagama yunwa takeji hakan yasata daura bakin salkakin gashinta da scarf din abayar wasu soft flat shoes ta zira kafar ciki tafito zuwa dining area ko da tasauko babu kowa t.v ce kawai ke nata aikin sai na’urar da sanyi dake aiki hankalin sanyi wajan ya hade da