Sashe 70
Asanadin Makwabtaka Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
bayan kaman minti ashirin da tafiyar Aunty Nameer ya shigo cikin parlon Hajiya na a d'an kishingid'e da yake yaran gidan duk yini suke a School shiyasa basu cika zuwa mata hira ba Saboda gajiya kuma wani lokacin da daddare aikin Assignment suke da angama kuma aka ci Abinci da wuri suke kwanciya sai Weekend suke samun lokaci sosae har ayi abubuwan nishad'i, kujerar kusa da ita ya nufa ya zaune yana sakin faffad'an murmushi idon ta akan shi itama d'an murmushin take mashi, gaishe da ita yayi ta amsa tana gyara zamanta idonta a kan farar ledar hannun shi mai d'auke da tambari an rubuta Special soya, ce mashi tay mi ta samu ne ya d'an kalli ledar kafin ya kalleta ya girgiza ma ta kai yace ba nata bane Yayar shi ya kawo mawa taci ko Babyn su shima ya ci, ta6e baki tay tace ai kafin ai d'aran akai kwand'i dai masu Baby, yana dariya ya mik'e yace bari ya kai mata in ta ci sai ta yan mata, Fatuu na kwance tayi tsuru ta ji sallamar shi aikuwa da sauri ta d'ago suka had'a ido, cikin d'akin ya nufo ta yunk'ura ta tashi zaune, a bakin gadon ya zauna idon shi akanta yana murmushi ya gaishe da ita ta amsa itama da d'an murmushin, hannu ya kai cikin aljihun jeans d'in shi ya fiddo maganin dake cikin farar ledar magani a jiki anyi alamar guda d'aya za'a sha ya mik'a mata da sauri ta kawo hannu ta amsa tace mashi ta gode, mik'a mata ledar hannun shi yay yace gashi nan aba baby d'in su tay murmushi kawai ta amsa yay mata fatan Allah yasa tay baccin yau harda miyau tana dariya tace Amin, mik'ewa yay yayi mata saida safe ta amsa, yana fita da sauri ta kai maganin ta tura a cikin bra dinta sannan taji ta d'an samu natsuwa sai kuma ta shiga tunanin yadda zata ba Hajiya, tunanin ko taje ta d'aukko lemu a fridge ta saka mata sai ta bata tayi wata zuciyar ta raya mata ai ba lalle tasha lemu ba da daddaren nan, gaba d'aya ta rasa tunanin yadda ya kamata tayi duk fuskarta ta yamutse can furar da Dad ke kawo masu ta fad'o mata a rai tabbas a ciki yakamata ta saka mata to amman ta Yaya, zuciyarta ce ta bata ta koma parlon don yanzu Dad ya kusa zuwa in yazo sai tasan yadda zatai ta zuba mata, da sauri ta saukko daga gadon har zata tafi sai kuma tayi tunanin tayi dubarar tafiya da abunda Nameer ya kawo mata ta kai mata, d'aukar ledar tay ta nufi parlon gabanta nata fad'uwa, cikin parlon ta fito Hajiya ta d'aga ido ta kalleta ta nufe ta, daga gefenta ta zauna tana d'an murmushi ta gaishe da ita bayan ta amsa tace mata Allah yayi kenan ta fito, shiru tay bata ce komai ba sai kuma ta mik'e ta kai mata ledar tace gashi, d'an ta6e baki tay tace ta ci abunta tunda ita ya kawo mawa da yayi niyya ai da ya had'o da ita dama ba so yake taci ba don haka ta k'oshi, hak'uri Fatun ta bata tay d'an murmushi tace mata wasa take mata taci, juyowa tay taja table gaban Hajiyar bayan ta d'aura ledar ta fiddo nannadaddar foil paper d'in ciki, warwareta tayi wani uban k'amshi mai dad'i ya daki hancin su baki d'aya, wani had'addan gasashen nama ne a iya ido kawai sai ya burge mutum irin kalar suyar da aka mashi yasha su Albasa da koran tattasai harda soyayyan dankalin turawa naman dai yayi ba k'arya😋 bayan ta bud'e ta kalli Hajiya tace don Allah taci tay d'an murmushi tace ta ci ta k'oshi in ta rage sai taci, a marairaice Fatun tace a'a ita ta fara ci in ta rage sai taci, ganin in ba ci tay ba bazata k'yaleta baà kuma dai naman ya burgeta yasa tace ta zauna to sai su ci tare sosae Fatuu taji dad'in hakan ta zauna, a nutse suke ci sai faman dakon shigowar Dad take can wata zuciyar ta bata ta tambayi Hajiyar ko zata sha lemu sai taje ta d'aukko mata daga nan ta saka mata maganin, koda ta tambaye tan ce mata tay a'a bazata sha lemu ba ruwa kawai zata sha shima sai sun gama in kuma ma an kawo mata Furar ta Shikenan ita zata sha tana d'an murmushi tace to, sai Addu'ar Allah yasa akawo furar take a lokacin, cikin sa'a basu kaiga gamawa ba Dad d'in ya shigo lokacin Fatun kad'ai ke ci Hajiya ta daina ci, yana ganin su yay murmushi yana sanye da farar shadda babbar riga ya k'araso cikin parlon yana fad'in shagali suke haka Hajiya na yar dariya tace Nameer ne ya kawo ma d'an su abun dad'i ita kuma ta cinye mashi duk sukai dariya, zama yay ya gaishe da ita bayan ta amsa Fatuu ma ta gaishe da shi ya amsa cike da kulawa ya tambayi ya take badai wata matsala ko tace mashi eh yace haka ake so, yunk'urawa yay ya mik'e ya nufi kan c-table ya d'aura ledojin yace to shima ga nashi a had'a aci gaba da party duk sukai dariya Hajiya tay mashi godiya da sa Albarka Fatuu ma tayi mashi godiya yay masu saida safe, wani irin bugu k'irjin Fatuu ke yi ga k'oshi ga kwanan yunwa, ga dama ta samu amman bata san taya zata zuba ba, can ta mik'e tana fad'in bari ta zubo mata a cikin cup Hajiyar ta d'aga mata kai, hannu ta kai za ta d'auki ledojin furar Hajiya tace mata ta bar su taje ta d'aukko cup d'in mana da sauri tace to, kaman ta saka ihu haka take ji ta nufi Fridge d'in, bayan ta d'aukko glass cups d'in ta dawo ta kai hannu ta fiddo robar furar tana cikin bud'ewa taji Hajiyar tace ta matsu bari ta je toilet ta dawo yadda zata sha a nutse har Fatuu bata san lokacin data washe baki ba tace to, d'aukar sandarta tay dake gefe ta nufi hanyar shiga d'akin ai tana shigewa jiki na rawa Fatuu ta kai hannu ta fiddo ledar maganin sai kerma hannun ta Keyi duk ta rud'e tana yi tana kallon kopar shigowa da kuma ta bedroom, fiddo guda d'aya tayi har zata saka zuciyarta ta raya mata ba lalle ya narke da sauri ba don furar kitif take kuma k'ilan ma guda d'aya bazai gaurayeta ba har yayi aiki, k'ara ciro d'aya tay da sauri ta maida ledar cikin bra d'in duk ta rud'e, kamo ha6ar kallabin ta tay ta saka magungunan ta rufe ta kai baki ta d'an tattauna sannan ta bud'e ta kai bakin robar furar ta zuba, sakin ha6ar tay da sauri ta rufe robar ta d'auka ta hau Jijjiga ta, maida ta tay ta aje a saman table d'in tana ta zare ido da sauri ta gyara kallabin ta sai faman zare ido take zuciyarta ta shiga raya mata ta daidaita natsuwar ta kar a gane ta, fiddo d'ayar robar furar tay ta bud'e har lokacin hannunta rawa yake ta zuba a d'ayan cup d'in bayan ta rufe robar ta d'auki cup d'in ta fara sha, gaba d'aya idanunta na akan kopar Bedroom har bata san tana kai cup d'in bakin hancinta ba sai taji take ankara, bayan wani lokaci Hajiya ta sako sandarta ganinta wani irin Fad'uwa gaban Fatuu ya hau yi, k'arasa fitowa tay ta shigo cikin parlon, bayan ta koma inda ta tashi ta zauna da sauri Fatuu ta aje cup d'in zata zuba mata tace ta barshi bari ta zuba, idanun Fatuu akan furar dake sauka cikin cup d'in tsoronta kar taga 6ar6ashin maganin, bayan ta gama zubawa ta d'auka ta kai baki duk da hakan hankalin Fatuu bai kwanta ba ta shiga tsoron kada kuma ta tauna maganin, har Hajiya ta shanye tata Fatun bata gama ba saida tayi mata magana kan tayi sauri ta gama ko taje ta watsa ruwa ta cire wannan d'amammun kayan ta kwanta tace to, bayan ta gama ta maida robobin cikin ledojin ta kwashe su ta nufi bakin k'opa inda dustbin yake ta saka, saida safe tay ma Hajiyar tace mata Allah ya tashe su lafiya, koda ta shiga toilet ba'a nutse tayi wankan ba, bata d'au lokaci ba ta gama bayan ta fito cikin sand'a taje ta lek'a cikin parlon ta hango Hajiyar zaune a inda ta barta idon ta akan Tv, jiki a mace Fatuu ta juyo ta dawo cikin d'akin ta nufi bakin gado ta zauna jikinta sanye da rigar wanka, tunanin kodai maganin bazai mata aiki ba ta shiga yi, ta dan d'auki lokaci a haka can ta mik'e sukuku da ita ta nufi wurin kayanta, doguwar rigar bacci ta fiddo bayan ta saka ta d'auki ta wankan ta nufi toilet, koda ta fito saida ta sake zuwa ta lek'a still Hajiyar na a yadda take, yanayin fuskar Fatun ne ya canza idanunta suka ciko da k'walla ta nufi gado, gajiya tay da zaman a hankali ta kwanta tay shiru k'walla suka fara gangaro mata, a hankali take kai hannu tana gogewa k'wallan, sosae ta damu da tafiyar da Haisam zai yi gashi bata san lokacin da zai dawo ba don da ta tambaye shi ce mata yake daya samu time zai zo ya ganta,