Sashe 20
Asanadin Makwabtaka Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Wuraren k'arfe d'aya suka tashi da yake ranar juma'a ne, duk suka goya jakunkunan su suka nufi hanyar fita daga class d'in, suna fitowa wayar Fatuu ta fara ringing ta kai hannu cikin aljihun rigarta ta d'aukko ta, tana dubawa taga sunan Hubby ya bayyana ta kalli Fauzy dake kallonta ta kashe mata ido tace mijinta ne ke kira Fauzyn ta d'an yi murmushi kawae, picking tay ta kara wayar a kunne a shagwabe ta kira sunan shi shima kiran sunanta yay taji yace yana a inda yake tsayawa, cikin rashin fahimta ta tambayi inda yake tsayawa a ina yace a School d'in su, waro ido tay with surprise written boldly all over her face tace "Are u serious Hubby!" tana jiyo sautin murmushin shi yace mata ai tasan bazai mata irin wannan wasan ba, cire wayar tayi cike da murna ta kalli Fauzy tace mata mijinta ya dawo gashi ma har yazo d'aukarta, itama Fauzyn tayi mamaki da sauri ta kamo hannunta tace tazo suje su gaisa sai faman washe baki take ta kasa 6oye murnar ta, sosae take sauri tana ruk'e da hannun Fauzy itama dole ta rink'a yin saurin tana fad'in kar tasa su fad'i don Allah, tana hango Motar ta saki hannun Fauzy ta nufeta da sauri sauri gudu gudu Fauzy nata dariya tana girgiza kai, k'opar gaba ta bud'e tana sa kai wani fitinannan k'amshi tare da ni'imtaccen sanyin Ac suka tarbeta, had'a ido sukai dashi yana sanye da farar shadda sumar nan tasha gyara, k'ayataccen murmushi ya sakar mata itama murmushin take mashi ta matsa kusa dashi ta kai duka hannuwanta ta tallabo fuskar shi batai wata wata ba ta had'e lips d'in su, da k'yar suka raba fuskokin nasu breathing rapidly sai murmushi suke ma juna, saida ta samu natsuwa sannan ta tuna da Fauzy da sauri ta lek'a ta hango ta daga d'an can nesa ta tsaya, da hannu tay mata alamar tazo ta nufo Motar tana d'an hararar Fatun had'i da d'an murmushi, a bakin kopar ta tsaya Fatun ta juya tace mashi ga Fauzy zasu gaisa ya jinjina kai, da hannu tay ma Fauzyn alamar tazo ta duk'o da kanta tace mashi ina wuni fuska a sake ya amsa ta sake ce mashi an dawo lafiya nan ma ya amsa, janye kan tay Fatuu na murmushi tace mata sai Monday wani kallo Fauzyn tay mata itama tana murmushin kafin tace to sai sun yi magana, tana maida kai cikin Motar zata rufe Haisam d'in ya mik'o mata kud'i yan dubu dubu sabbi dal yace ta bata, da sauri ta lek'o lokacin Fauzyn har ta tafi Fatun ta fito daga cikin Motar tare da kiran sunanta da d'an k'arfi, tsayawa tay ta juyo Fatun ta nufota, tana zuwa gabanta ta mik'a mata kud'in tace gashi inji Mijinta har saida Fauzyn ta d'an bud'e ido ganin kud'in nada d'an yawa sai kuma ta amsa tana murmushi tace "tukuicin tura sako ne aka bani kenan" gaba d'aya sukai dariya daga baya tace tay mashi godiya, har Fatun zata juya Fauzy tace mata kar dai ta manta ran Wednesday zasu fara Exams sosae Fatuu ta saki dariya kafin ta juya ta tafi, Motar ta koma ta shiga bayan ta rufe ya ja suka tafi hannun shi d'aya ruk'e da nata nan fa ta shiga zabga mashi shagwaba tana fad'in miyasa bai fad'i mata yau zai dawo ba kuma ko yau da safe ba saida sukai waya ba, yana ta murmushi idon shi akan hanya, d'an kallon ta yay yace kawae yana son bata Surprise ne, tura baki tay tace amman daya fad'i mata ai ta shirya, tambayarta yay wane irin shiri tace tayi gayu mana harda kitso da lalle har saida yay yar dariya, ganin ta d'an d'aure fuska ita ala dole fushi take yasa shi d'an matsa hannunta ta kalle shi shima kallon ta yay yace kada ta damu ko bata yi su ba a koda yaushe k'ara mashi kyau take har bata san lokacin data saki murmushi ba ta d'ago hannunshi dake ruk'e da nata tay pecking d'in shi ya d'an lumshe ido tare da furta "Day's my Baby", A wani babban Eatery ya tsaya yace mata yana zuwa ta d'aga mashi kai, tana ta kallon shi ta glass har ya shiga cikin wurin, after some minutes ya fito hannun shi ruk'e da yan manyan ledoji masu d'auke da tambarin wurin, back door ya bud'e ya saka bayan ya rufe ya koma cikin Motar yaja suka tafi. bin hanyar da suka bi tay da kallon ganin ba wadda suke bi bace, sai daga baya ta fahimci G.r.a suka nufa........
*ASM 078*
~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
........Ganin inda zasu yasa ta fara k'ok'arin raba hannun su tana fad'in bari ta kira Tk ta fad'i mashi ba sai yaje d'aukota ba ya d'aukko Mino kawae, ba tare daya saki hannun ba yace mata sun yi magana dashi tace Ok, suna isa Officer ya bud'e masu Gate ya shiga da Motar, a bakin entrance ya parker Motar Fatuu ta juya suka had'a ido a tare suka sakar ma juna murmushi har lokacin yana ruk'e da hannun nata, jingina kan shi yay da headrest idanun shi a d'an lumshe ya furta mata zaije Masallaci ya dawo ta jinjina mashi kai, cewa yay bari ya kama mata ledojin Abincin tace ya barshi zata d'auka still da murmushi akan Face d'in shi ya tambayi zata iya, yar dariya Fatun tay tace to abunda ba wani nauyi ne da su ba kuma ko suna da nauyin ai zata iya d'auka ya jinjina kai yace ya manta Babyn shi mai k'arfi ta iya bugun mutane Fatun tasa dariya, saida yay pecking hannunta sannan ya saki tace mashi sai ya dawo, bud'e Motar tayi ta fito shima fitowa yayi ya zagayo side d'in da take har ta bud'e kopar bayan ya duk'a ya fiddo mata ledojin ta amsa tana murmushi ta furta "Thanks My Hubby" jawota yay jikinshi suka kafe juna da ido suna d'an murmushi can Fatuu ta hura mashi iska a fuska ya d'an kikkafta ido tasa dariya tace yaje kar ya makara a gama sallar bai samu ba, sakin ta yay ya ce mata sai ya dawo ta d'aga mashi kai, har ya juya tace yayi masu Addu'a sosae ya d'an juyo ya jinjina mata kai kafin ya cigaba da tafiya, tsaye tay hannunta d'aya ruk'e da ledojin ta d'aga d'ayan tana mashi bye bye, bayan ya juya Motar ta kalli gate tsayawa yay ya sauke glass da hannu yay mata alamar ta shiga ciki tana murmushi ta juya tana yi tana waiwayen shi har ta shige sannan ya ja Motar,