← Book details Asanadin Makwabtaka Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 187 OF 211

Sashe 187

Asanadin Makwabtaka Part 3 Complete Hausa Novel · about 5 min read

"Naji Hajjaju, in bata son Emran ɗin shikenan amman nidai gaskiya ban goyon bayan ta auri yaron don haka ta nemi wani" fuska a yamutse tay maganar aikuwa a fusace Hajiya tace "bata neman wanin wanda take son shi zata aura matuƙar Allah ya ƙaddara hakan, ke waya hana ki auren wanda kike so, wato yanzu kin kawo ƙarfi ke ga uwa shine zaki nemi ɗaga ma mutane hankali ke wa yay maki haka, inace lokacin da kika haɗu da Mahaifinsu kina da samarin da kuke soyayya lokacin in ban mance ba yaron nan soja ɗan wurin abokin Mahaifinku gashi nan da suna.....Nasir yauwa ba wanda bai yi tunanin shi zaki aura ba daga haɗuwa da mahaifunsu duk kika ruɗe ke kinga mai jan kunne rana ɗaya kika zo mana da zancen ke shi zaki aura, a lokacin Allah ya jiƙan rai mahaifin ku shine ma yaso ya ƙi abun don shi mutum ne mai kishin ƙasar shi da al'ummarshi ni na rarrashe shi kan ya ƙyale ki har Allah yasa kukai aure, in ma kin manta ne to gashi nan na tuna maki don haka yadda ba wanda ya hana ki auren wanda kike so haka itama ba wanda zai hanata auren wanda take so" idanun Hajiya Maryam ne suka ciko da ƙwalla suka zubo mata sharr cikin 6acin rai ta shiga faɗin amman ita ko a lokacin data kawo mahaifin su ai ya gina rayuwar shi ko shikenan sai ace an taru anata auren dangin su kowa su Haisam da Nameer sun auresu ga Kakar tasu ma kan su za'a ƙare,

"Zancen gina rayuwa ko ɗazun nayi maki maganar saurin mi kike ki jira shima kiga baki san yadda Allah zai da tashi rayuwar ba sai kiga ya zamo abunda baki ta6a zato ba ai shi arzuƙi na Allah ne Maryam kema ai ba wayon ki ne ya baki ba ko, sannan Maganar anata auren su alamar suna da nagarta ne ai ko a kasuwa zaki ga ana rububin abu mai nagarta, wasu Familyn ma zaki ga basu auren bare sai yasu yasu ma don haka don anata auren su ai ba aibu bane" shiru Hajiya Maryam ɗin tayi tana goge ƙwalla,

"Ina son jan hankalin ki Maryam al'amari in dai akace na Allah ne ki daina kafiya irin haka, wannan abun daya faru yanzu tamkar ishara ne Allah ya nuna maki, nan yarinyar nan Fateema daga ta auri mijin ɗiyar ki kika ɗaga masu hankali kikai ta kumfar bakin ke ɗiyarki bazata zauna da ita matsayin kishiya ba don bata kai matsayin tayi kishi da ita ba waye waye, to yanzu ga ɗiyar ki nan ta cikin ki Allah ya ɗaura mata son Yayanta so mai tsanani itama yar jakar ubar nan harda ita aka hana Fateema zaman lafiya amma kinga soyayya ta rufe mata ido ko kunya bata ji ba tazo tace tana son Yayanta..." ta juya tana kallon Farha tare da ɗan harararta Farhar ta ɗan tura baki a hankali tace "pls Hajiya let bygones be bygones, ba kinsa mun shirya tuntuni ba",

ta6e baki Hajiya tay tace "da yake fa abunsu kike so kyace haka, shiyasa ita fitina bata da daɗi sam, yanzu da baku shirya ba kina tunani shi wanda kike son zai saurareki ne alhali kina tsangwamar yar'uwar shi, to da ya zaki da son ko sai kije ki faɗa rijiya mai kwala6e?" yar dariya Farhar tay ta sunnar da kai, maida idonta tay kan Hajiya Maryam da 6acin rai ya bayyana akan fuskarta cikin kwantar da murya tace "Wato shi Ubangiji yana yin abubuwa cikin hikima, daya halicci bayinsa sai ya kasasu wasu yayi su masu wadata wasu masu rufin asiri wasu kuma wanda basu dashi gaba ɗaya hikimar yin hakan shine don kowa ya amfana da kowa don inda yaso zai ba kowa arzuƙi amman sai bai yi hakan ba, duk wanda kika ga Allah ya ba arzuki bai bashi don ya amfana shi kaɗai ba face don ya taimaki wanda bashi dashi wanda ta silar haka zaka samu ɗunbin lada har kasamu shiga aljanna haka wanda bashi dashi in yayi haƙuri da yadda Allah yayi shi ya rungumi ƙaddarar shi bai sa6i Allah ta dalilin hakan ba shima sai kiga ya cinye jarabawar shi ta hanyar hakan har ya shiga aljanna, wasu da yawa Allah na saka arzuƙin su a hannun wasu shine zaki ga ta silar taimakon da kayi ma wani in ma aiki ka sama mashi ko kuɗi ka bashi ko auren shi kai da sauransu sai kiga hakan yayi silar arzuƙin mutumin, to dana yi nazari sai na gano kusan hakan ce Allah ya ƙaddaro tsakaninmu dasu Dije shiyasa har ya haɗamu maƙwabtaka kuma in kikai la'akari da ai basu kaɗai bane makwabtana akwae wanda muke tare tun kan suzo zaki shaida hakan, Allah yasa rabon wadatuwar su a hannun mu don haka bamu da ikon hana hakan koda kuwa ace bamu so to wllh sai rabonsu dake tattare damu ya isa gare su, don haka inason ki kwantar da hankalinki ki ɗauka mu dasu yanzu mun zama Family duk abunda ya taso tsakanin mu dasu in dai mai kyau ne to mu rungume shi hannu bibbiyu muyi fatan alkairi" shiru Hajiya Maryam tayi ta maida idonta ƙasa,

"Yanzu kin amince mata kan abunda take son?" Hajiya ta tambaya idonta akanta, ba tare data ɗago ba tace "taje Allah ya taimaka",

"Ba haka yakamata kice ba Maryam fatan alkairi zaki yi mata matsayinki na mahaifiyarta sannan ki yaƙi zuciyar ki ta rinƙa kallon abun a alkhairin" shiru tayi duk idanunsu na akanta can ta ɗago ta kalli Hajiyar tace Allah ya tabbatar da alkhairi, murmushi Hajiya tayi ta amsa da Amin Farha ta shiga yin murmushin farinciki tana washe baki tace "Thank you so much Mom, I love u" wata uwar harara ta wurga mata Hajiya tay yar dariya tace "in kina harararta fa zata ƙara 6acewa" ɗan gutsirin murmushi Hajiya Maryam ɗin tayi bata ce komai ba da sauri Farhar ta miƙe ta nufi hanyar fita daga ɗakin,
Chapter 187 · 0% Book details