← Book details Asanadin Makwabtaka Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 211

Sashe 2

Asanadin Makwabtaka Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Yadda hakan ta faru, bayan Haisam sun gama Magana da Fanan kan zuwa Nigeria ranar talata, da yamma Hajiya Maryam ta kirata don ta ji halin da ake ciki game da tahowarta nan take sanar mata yadda sukai da Haisam kan zuwa Nigeria ta yi ma Hajiyar Magana da kanta, nan Hajiya Maryam taji dad'i sosae don tasan da wuya in Hajiyar bata bari an saki Fatun ba Saboda su duka sun nuna basu so kuma tasan yadda take ji dasu gaba d'aya, hakan ne yasa washe gari da Hajiya ta kira Hajiya Maryam game da zancen dawowar Farha da Maganar data yi mata sam bata damu ba, tun bayan da suka yanke zuwa Nigeria Haisam ya kasa samun natsuwa, damuwa tayi mashi yawa don yasan shi dae ba iya sakin Zaraah zai yi ba yadai biye mata ne don ya kwantar mata da hankali k'arshe kuma yasan indae suka zo Nigeria yak'i sakin Fatuu to abun zai k'ara kwa6ewa ne, hakan yasa ya yanke tunkararta akan hakan, Ranar Alhamis da daddare ya isketa a d'aki lokacin tana zaune akan gado tana latsa wayarta, tana ganin shi ta d'ago tana mashi dariya ya nufi bakin gadon ya zauna shima yana mata murmushi, aje wayar tayi ta matso inda yake ta kwanta a bayan shi ta yadda yay kaman ya goyata ta sak'alo hannuwanta a wuyan shi nan ta shiga fad'a mashi kalaman soyayya, sosae yaji fargabar sanar da ita abunda ya kawo shi k'arshe dai yay k'arfin hali yace mata magana yake so zasu yi, tana jin hakan ta sake shi ta dawo daga gefe tana kallon shi, d'an jimm yay ta kafe shi da ido daga baya ya fara magana gently, ce mata yay Alfarma yake son ya nema a wurinta for the first time a zaman su, jinjina mashi kai tay gaba d'aya ta maida hankalinta akan shi, ce mata yay ya zauna yayi dogon tunani gaskiya idan ya saki Zarah bai mata Adalci ba zai zama ya cuce ta ne Saboda shi ya fara saninta sannan tayi k'arama ace ta zama bazawara, wani kallo take bin shi dashi yanayin fuskar ta ya canza da alamun d'aurewar kai tace to mi yake nufi kenan, kauda idon shi yay tana ta kallon shi can ya juyo ya kalleta yace "I can't divorce her......" waro ido tay hankali tashe take kallon shi, hannu ya kai zai kama hannunta da sauri ta janye ta fara k'ok'arin nufar can d'ayan 6angaren gadon ta sauka, da sauri ya idasa hayewa saman gadon ya cafkota, rungume ta yay k'am ta fara kokowar kwacewa amman ta kasa kawae sai ta fashe da matsanancin kuka ta fara fad'in ita zai yaudara bacin sun gama Magana shine zai zo yace bazai saketa ba dama tasan yana sonta ne shiyasa ya aureta yanzu kuma daya san ita tana haihuwa shine zai ce bai iya rabuwa da ita to indai ya za6i zama da ita ita Allah bazata cigaba da zama da shi ba, sosae ta tashi hankalin ta sai k'ok'arin k'wace kanta take k'arshe kawai sai ya had'e bakunan su ya fara kissing d'inta deeply don yasan hakan zai iya calming nata, ya d'an d'auki lokaci yana mata hakan kafin ya saki bakin nata jikinta sai kerma yake tana sheshsheka, kwantar da kanshi yay saman kanta cikin sigar rarrashi ya fara magana yace mata yasan ita ba mai son kai bace tayi tunani, in ya saki Zarah zai cuceta ne yasan bazata so hakan gareta ba ko kuma sister d'inta Farha tayi aiki da Hadisin manzo SAW da yace love for ur brother what you love for urself, a yadda yasani tana son Zarah sosae miyasa bazata tausaya mata ba, sai huci take ta hau girgiza mashi kai tace ita dai bazata iya zama da ita matsayin kishiya ba, miyasa zai saka mata rai yayi mata alk'awarin zasu zauna su biyu, ce mata yay ya gaya mata already da aure a tsakanin su amman yanzu zai iya yi mata wani daga Zarah bazai k'ara Auren wata ba su biyu zasu zama matan shi har k'arshen rayuwar shi, shiru tay kaman mai nazarin wani abu can ta d'ago ta kalle shi idanunta sharkaf da hawaye tace "Tell me the truth, do you love Zarah?" Shiru ya d'an yi yana kallonta can ya jinjina mata kai kawai sai ta fashe da kuka ta fad'a jikin shi tana fad'in ita daman tasan son Zarah yake shiyasa tun farko ya auretan in ba haka ba miyasa bai sa Abbas ya aureta ba daga baya ya saketa sai shi daga baya kuma yazo ya kwanta da ita, tasan itace First love d'in shi dama ita ba son ta yake ba kawai tausayinta ne yasa ya aureta don haka zata bar shi sai suji dad'in zama da juna, sosae take kuka yana rungume da ita cikin kwantar da murya yace mata wayace mata bai sonta, da farko da akai mashi Maganar aurenta Saboda yasan ba soyayya suke ba shiyasa ya nuna bazai aureta ba don bai d'auka Maganar da ta yi mashi ta zai aureta ba da gaske take Saboda lokacin a wurin shi tayi k'arama da wannan Maganar, amman daga baya daya nuna ya amince Saboda yana son ta ne, kuma da bai sonta a zaman da sukai ai ya isa ta gane, tambayarta yay a zaman su tare ya ta6a cutar da ita ko hantarar ta ko dai yi mata wani abu na rashin so, d'an girgiza mashi kai tay yace to ta daina cewa haka he truly loves her kuma yana rokonta tayi mashi wannan alfarmar Saboda son da take mashi koda kuwa daga ita bazata k'ara mashi wata ba har k'arshen rayuwar su ya amince, gaba d'aya ya kashe mata jiki ganin haka yasa yaci gaba da rarrashinta, wai akace tsakanin mata da miji sai Allah d'agowa tay tace "Shikenan na Amince but don't break the promise u have made now kuma kayi man Alk'awarin zaka yi mana Adalci" sosae ta bashi tausayi don yasan Saboda son da take mashi ne yasa tayi saurin Amincewa, ce mata yay in sha Allahu zai yi masu Adalci tace ita bata yarda ba sai yayi mata Alk'awari da d'an murmushi yace to ya yi mata. Koda suna a jirgi saida ta jaddada mashi ya dai ce zaiyi Adalci a tsakanin su ko yana murmushi yace mata eh, Bayan sun iso a Bedroom d'in Hajiya suka sauka dama tun kafin su zo Haisam d'in ya fad'i mata game da amincewar da tayi itama Hajiya taji dad'i sosae, bayan sun gama gaisawa tayi masu Maganar Abinci duk suka ce mata basu jin yunwa a lokacin nan ta k'ara yi ma Fanan Nasiha sosae ta nuna mata ta d'auki abun a matsayin Alkhairi ta shiga bata misalai kan irin hakan sosae Fanan ta d'auki Nasihar Hajiyar daga baya ta tambayi Fatun Hajiya tace bata dad'e da barin Part d'in ba, ita da kanta ta tambayi Hajiya takarda ta rubuta abun ciki taba Haisam d'in tace zata mata wasa ne Hajiya na dariya tace ta dai tada mata hankali dama yar'uwarta da Mahaifiyarta sun gama nasu da alamun rashin fahimta Fanan d'in ta tambayi mi sukai mata nan Hajiya ta kwashe komai da Hajiya Maryam da Farha sukai ma Fatun, sosae ta bata tausayi har fuskarta ta bayyana, daga baya suka koma Parlor nan Hajiya ta kirata saidae ita bata san da Maganar sak'on da Fatuu ta tura ma Haisam ba saida tazo Fanan na mata Maganar ta fahimci ita ta tura mashi sak'o Fanan d'in ta gani.
Chapter 2 · 0% Book details