← Book details Asanadin Makwabtaka Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 211

Sashe 31

Asanadin Makwabtaka Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A ranar bayan Magrib yan Adamawa suka iso, da Baffan Fatuu da Ard'o daya sha babbar riga da rawani shi ga mai Mulki yayi kaman wani d'an tsuntsu, harda Yaya da Baffan su Altine da innarsu Altinen sai d'ayar matar Ardo sai Yadikko dasu Aysha da Kamalu harda uban dawon furar su da Nono bokiti bokiti, k'auyanci kam ba sai an fad'a ba nan suka shiga zuba shi duk sun saki baki galala suna kallon Aljannar duniya in ka cire Yadikko da Baffan Fatuu ba wanda bai nuna k'auyanci ba a cikin su harda mai Mulki ya kasa sauke kan shi k'asa sai kace mai ciwon hangum, harda ce ma sauran dama yanata jin labarin cewa Abuja kaman Aljanna take shi dae babban su Fatuu murmushi kawai yake farinciki fal ran shi, su Yaya dai an kasa cewa komai sai faman jinjina kai take kaman k'adangaruwa baki a kwa6e, suma a mutunce aka tarbesu harda Hajiya ta fito suka gaisa tayi masu ya hanya sai faman kalle kalle suke su Aysha ma kaman tsoron gidan suke duk sun shishshige ma Yadikko, daga baya suma bayan akai masu jagora Mazan aka kai su d'ayan part d'in su kuma su Yadikko bangaren da su Aunty Mareeya suke, bayan sun zazzauna a cikin parlon su Feenah suka zo aka gaggaisa daga baya suka nuna masu bedrooms da zasu shiga, su dai ai sai yadda akai dasu ba baki sai idanu kawai suke wuwwurgawa, bayan sun shiga d'akin masu son shiga toilet Yadikko ce ta nunnuna masu yadda zasu amfani da komae gaba d'aya ma tsoron shi suke, Yadikko tunda tazo take ta son ganin Fatuu, kasa jurewa tayi ta fito a cikin parlor suka had'e da Saude ta nufeta tana murmushi ganin haka yasa ta tsaya, gaisawa suka k'ara yi tace mata don Allah ina zata ga Amaryar ne Saude tace basu had'u bane tace mata eh, ce mata tay ta koma d'aki bari ta dubo mata ita tayi godiya, bayan komawarsu aka kawo masu Abinci nan fa suka shiga ci hannu baka hannu kwarya a ran Yadikko ta shiga gode ma Allah daya sa su kad'ai ne, bada jimawa ba Saude ta dawo saida ta kwankwasa kopar sannan ta tura Yadikko na ganinta ta taso, ce mata tayi Fatuun bata nan wai sunje wurin amsar d'inki tace to tay mata godiya. Bayan Senator ya dawo har inda aka sauke su Ard'o yazo tare da Haisam da wasu yan uwan shi maza guda biyu da suka zo, a parlor suka zauna su Ard'on suka fito Kamalu dai Amadu yazo ya tafi dashi inda suke, ganin suna niyyar duk'awa kasa yasa yace masu don Allah kar suyi haka ga kujeru suma su zauna ai duk d'aya ake, bayan sun zauna aka shiga gaisawa suka yi masu an zo lafiya, Baffa ne ya nuna ma Ard'o Haisam yace shine mijin inna wuron ya hau jinjina kai da baban Altine yana fad'in ba shakka, godiya Senator yayi masu suka hau fad'in ba komai wllh ai sune yakamata suyi godiya nan suka hau yin godiya Ardo cikin hausar shi da bata fita sosae yace ai akwae shanu ma da suka taho dashi yana a kan hanya da daddaren nan zai iso, sai kace shi ya bada shanun ba Baffan Fatuu ba, baban Altine ne ya k'ara fad'i masu abunda yace su duka suka yi godiya suna fad'in Allah ya bar zumunci daga baya suka tafi.

Fatuu na dawowa taji su yadikko sun iso tana sanye da riga da skirt na lace da gudu ta nufo bayan, tana tura kopar d'akin da suke suka had'a ido da yadikko ta nufeta tana zuwa ta fad'a mata tana dariyar farinciki sauran yan d'akin ma murmushi suke harda Yaya da alama abun yafi k'arfin ta don dole ta aje makaman yak'in nata, d'agowa tay ta juya tana gaishe da sauran sai washe baki suke suna amsawa ganin ta suke kamar Madara, zama tay a kusa da yadikko ta kama hannun Aysha tana tambayar ta ya Makaranta da d'an murmushi ta amsa mata, hira suka shiga yi gaba d'aya kowa Fatun burge shi take yadda ta koma kalar yan gayu, ganin kaman d'akin bazai ishe su ba yasa tace bari ta duba d'ayan d'akin in ba mutane sai wasu su je can, mik'ewa tay taje ta duba ta dawo tace masu ba mutane a d'akin wasu suje can suka ce to, hira suka k'ara yi da yadikko cike da Farinciki take fad'in taji mata dad'i wllh har bazata iya misalta mata ba tayi Addu'ar Allah ubangiji yasa gidan zaman ta ne na har abada ya kauda idon mak'iya, daga baya ta hau yaba irin kirkin dangin su Haisam tace samun irin su a masu kud'i yana da matuk'ar wahala, ta shiga yi masu Addu'oi Fatun na amsawa nan ta fad'i masu anyi masu anko ita nata sai zuwa gobe su Aysha kuma tace su zo suje ta d'aukko masu nasu suka mik'e cike da Farinciki suka tafi, suna fitowa cikin parlor tayi kacibus da Nameer da ya shigo, a gefen shi ta tsaya tana mashi wani kallo mai kaman harara ya sa dariya yana fad'in "kinga Yayata komai ya wuce tsakanin mu tunda naga wadda zata fanshe ki itama nazo nema don Allah ki turo man ita" cikin rashin fahimta Fatun tace wa kenan, kwatancen Mino yayi mata nan take ta gane ita ce, ta6e baki tay tace mashi to itama da sa rana akanta sai yayi hak'uri da sauri yace "No! Kar muyi haka dake pls am serious tayi man ba kamar kuma da ya kasance kuna kama tunda na rasa ki sai in maye gurbin ta dake" dariya Fatuu tay tace "wai Nameer a yaushe ka ta6a cewa kana sona ne da zakai ta man surutai haka" yar harararta yayi yace "kina nufin duk abubuwan da nike maki baki gane ba kawae fa ni don nasan ba yadda za'ai inyi aure a lokacin yasa na bari sai na gama karatu tunda kema naji likita kike son zama ashe ashe likiciyar gida ce zaki zama" dariya tay ta d'an girgiza kai tana fad'in Allah ya shirye shi, ganin zata wuce yasa da sauri yace pls ta turo mashi ita ta d'aga mashi kai, lokacin data shiga d'akin su Fauzyn suna ta faman gwada d'inkunan su da aka fara amsowa sai faman murna suke, kallon Mino tayi tace mata taje parlor ana neman ta da alamun mamaki tace ita ta d'aga mata kai, saukkowa tayi daga saman gado jikinta sanye da doguwar rigar Atamfa A-line ta yafa d'an madaidaicin gyale a saman kanta, tana shigowa cikin parlorn suka had'a ido dashi ya sakar mata k'ayataccen murmushin shi tana ganin haka ta gane shine ke nemanta kenan, nufar shi tay ta tsaya daga gaban shi tana d'an murmushi ta gaishe dashi, amsa mata yayi kafin yace in ba damuwa yana son zasu yi magana ne ta d'aga mashi kai don Nameer ba irin samarin da za'a musa mawa bane, da hannu yay mata alamun suje suka jera, suna fita ya nufi Sport field d'in gidan da ita.

A ranar saida su Fatuu suka kai tsakar dare suna hira sai daga baya ta koma d'akin Jidderh lokacin sun samu k'aruwar wata cikin yan uwan su na Daura da Suka zo k'awar Jidderh d'in ce, bayan ta shiga Jidderh d'in tace su kwanta ita bari tayi shimfid'a k'asa da sauri Fatuu tace a'a ai gadon zai ishe su. Washe gari bayan an tashi duk suka yi wanka aka fara yin Breakfast wanda lafiyayyun Abinci aka yi, daga baya kuma aka sa ma'aikatan dake hidiman Abinci suka dama furar da su Yadikko suka kawo aka rarraba ma mutane. Misalin k'arfe 12 na rana Aunty tazo d'akin Hajiya tayi ma gwaggo magana cewa za'a kawo lefen Fatuu cike da Farinciki tace to Hajiya tace mata taje ta sanar ma sauran iyayen nata tace to ta mik'e, d'akin su Yadikko taje bayan an gaggaisa ta sanar masu tace sai su fito parlor suka ce to, bayan ta fito d'akin su Aunty Mareeya taje ta sanar masu suma suka fito cikin Falon haka ma su Fauzy, bada jimawa ba aka fara shigowa da Akwatunan lefen aka shiga jera su a tsakiyar parlon har aka gama, akwati Set hud'u ne masu guda hud'u hud'u guda sha shidda kenan su kan su akwatunan abun kallo ne kala daban daban akwae set d'in bak'ak'e sai na maroon sai na brown sai kuma pink, Su Aunty ne da wasu yan uwan su Haisam d'in suka biyo kayan nan suka sa ma'aikatan da suka shigo dasu suka fara bubbud'a wa, ba abunda ka ke ji sai ma sha Allah da aketa fad'i kaya ne na gani na fad'a kusan duk ma an d'inka su harda wanda zata saka ranar Dinner, sai faman jinjina kai ake a wani d'an kit kusan duk zinarai ne a ciki harda gold su Fatuu anyi goshi hakanan ma Haisam yayi mata Akwatunan kaya inaga yanzu, bayan an gama dubawa aka hau yin godiya da Addu'oi, Fauzy ce ta koma d'akin da suka sauka da gudu da yake Fatuu na ciki ta hau bata labarin irin lefen da aka mata a rud'e sai faman zuzuta kayan take ita dai murmushi kawae take komai zuwa yake mata kaman a mafarki.
Chapter 31 · 0% Book details