Sashe 22
Asanadin Makwabtaka Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Bayan tayo Alwala ta fito a Laundry ta tsaya tana tunanin Hijab d'in da zata yi sallar don tata tayi k'arama bazata rufe k'ugunta gaba d'aya ba gashi rigar ta kamata sosae, k'arshe dole ita ta d'aukko ta sanya sai ta d'aukko kallabin uniform d'in ta d'aura a k'ugun nata da yake babba ne ya saukko k'asa, cikin Bedroom d'in ta dawo ta d'aukko prayer mat bayan ta shimfid'a ta kabbara sallar, bayan ta gama zaune tay ta shiga tunanin wai ina ya tafi ganin har lokacin bai dawo ba kuma bata san tun lokacin da ya fita ba, mik'ewa tay ta koma laundry ta cire hijab d'in da kallabin ta aje ta dawo cikin bedroom d'in, tsaye tay gaban mirror tana kallon kanta tana sakin murmushi gaba d'aya yanzu ji take bata da wata damuwa duk wani rad'ad'i da taji a baya ta manta shi, juyowa tay zata koma wurin gado sai kuma taji tana son fita ta d'an ga gidan, nufar k'opar fita tay kanta ba kallabi sai tulin Sumarta dake fake da ribbon daga baya ta bud'e sosae, tunkan ta k'arasa fita daga cikin Corridor da zai kawo ta cikin babban parlon ta hango Haisam a d'an kishingid'e akan kujera 2 seater, da sauri ta shiga cikin parlon ta nufe shi ya juyo yana kallon ta fuskar shi a sake, tana zuwa gaban shi ta fara k'ok'arin hawa jikin shi hakan yasa shi gyara zaman shi ta haye ya tallafe ta kamar wata jaririya, a shagwabe tace "Hubby shine zaka baro ni ni kad'ai a d'aki kazo nan kai zaune kuma ko salla baka tada ni in yi ba" Fuska a yamutse take Maganar ta d'an turo baki, murmushi kawae yake mata ba tare da yace komai ba hakan yasa ta d'an Jujjuya jiki tace yayi Magana mana, hannu ya kai ya shafi gefen fuskarta slowly yace ta yi hak'uri yaso ya tada ta bayan ya dawo daga Masallaci sai kuma ya manta, d'aga mashi kai tayi ya tambayi tayi sallan yanzu tace eh, shiru yay kawai yana murmushi ta kai hannu ta fara shafa kwantaccen sajen shi can kuma ta d'an d'ago ta tura hannun ta a cikin sumar shi tana sosa mashi har saida yay yar dariya, bayan ta cire hannun kai bakinta tayi ta manna mashi kiss a saman lips d'in shi ya d'an lumshe ido, bayan ta maida kanta tana kallon shi tace mi yake a anan in kallo zaiyi ba akwae kayan kallon ba a cikin Bedroom, a hankali ya furta mata yayi bak'o ne har saida ta d'an waro ido tace "bak'o? a nan gidan?" Kai ya d'aga mata tace "ina bak'on ko har ya tafi?" shiru yay yana d'an murmushi ganin ta kafe shi da ido ya d'an girgiza mata kai alamar a'a tace "to waye bak'on kuma yana ina?" Slowly ya furta "Abbas" k'ara bud'a ido tay tace shine ya zo yana ina, d'aga ido yay ya kallo can gefen shi still da murmushi akan Face d'in shi, zaro ido Fatuu tay don ta fahimci Abbas d'in yana a cikin parlon kuma shine ya kallo, gaba d'aya mutuwar kwance tay don ta kasa yin ko kwakkwaran motsi a ranta ta raya kenan duk abun nan Ya Abbas na kallon ta, bata gama zancen zucin ba ta jiyo Muryar shi yana fad'in "Mom Zarah barka da juma'a, kwana biyu ai nace da alama dai kin mance da ni, d'azun dana zo har nake tambayar H,zakee ke yace ai kina nan kina bacci ne" runtse ido gam Fatuu tay tare da cije baki wata irin kunya ce ta lullube ta taji kamar ta nutse a k'asa Haisam sai kallon ta yake yana murmushi haka Abbas d'in ma kawai sai gani sukai ta saukko da gudu ta nufi hanyar corridor Abbas ya hau yin dariya,
tana shiga cikin Bedroom ta nufi gado ta fad'a saman shi tare da kifa fuskarta a jikin katifa can ta fara d'aga hannuwa tana bugun Katifar sosae taji kunya, bayan kaman minti talatin Haisam ya shigo cikin d'akin lokacin tana kwance ringingine idonta na kallon sama ta gama borin jin kunyar, tana jin shigowar shi ta kai idon ta suka had'a ido da sauri ta juya mashi baya ya k'araso bakin gadon ya zauna yana d'an murmushi, kiran sunan ta yay tayi shiru saida ya k'ara sannan cikin tura baki ta amsa mashi, hannu ya kai ya jawota inda yake ya d'agota jikin shi ta fara yamutsa fuska tana kukan shagwaba, tambayar ta mi akai yayi tay mashi wani kallo tace ba shine ba yasan suna tare da Ya Abbas amman bai fad'i mata ba, rarrashinta ya shiga yi yace bai san taya zai fad'i mata bane ta riga ta fito shiyasa amman kar ta damu ai ba wani abu bane tunda shi mijinta ne tay shiru tana tura baki, ce mata yay tazo su gaisa zasu fita ne sai after Magrib zai dawo sai su fita da ita suci Abinci tace gidan Hajiya zasu je cin Abincin ya girgiza mata kai kafin yace zasu Eatery ne, da yar damuwa tace to ita da bata da kaya sai wannan rigar kuma ai ba yadda za'ai ta fita da ita haka, d'an jimm yay sai kuma yace Ok in ya fita yanzu zai je can gidan sai ya d'aukko mata ta d'aga mashi kai, Maganar gaisawa da Abbas ya k'ara yi mata tace ita wllh kunya take ji ya fara k'ok'arin mik'ar da ita yana fad'in ba wani abu ai, saida taje laundry ta d'aukko Hijab d'in uniform d'inta bayan ta dawo ta sa suka nufi parlon, tunda ta shigo kanta na k'asa ta kasa d'agowa ta zauna a Kujerar gefen wadda Abbas d'in yake yana dariya yace "Mom Zarah yau na zama surukin ki kenan" yamutsa fuska tay da k'yar tace mashi ina wuni ya amsa ta tambayi su Abdul da Aunty Feenah yace duk suna nan lafiya lau, da k'yar ta d'ago tace mashi sai yaushe zai kawo mata Abdul still da dariya akan fuskar shi yace tayi Yaya dashi ga baban Abdul d'in tana kulawa dashi ba shiri tasa hijab ta rufe fuskarta, tambayar ta yay ashe sun kusa fara Exams ta bud'e fuskar tace mashi eh yace to tana dai karatun ko ga Amarci kuma ta d'an juya kai ba tare data ce mashi komai ba,
"Mom Zarah nace yanzu kin gamsu Ya Haisam na son ki yana son yin rayuwar Aure da ke ko" maida kanta tay k'asa da k'yar ta d'aga mashi kai ya sake cewa "ina Maganar rabuwa da shi to ko kuwa tunda yanzu kin gane his heart belongs to not only his wife Shikenan" da sauri ta k'ara rufe fuskarta tana fad'in "Wayyo Ya Abbas don Allah ka bari" dariya sosae yake Haisam dai na zaune yana murmushi, ce mata yay ya bari sannan ta bud'e fuskar, tunano mata Maganganun da suka yi a baya kan k'addara da hak'uri ya shiga yi yace gashi nan yanzu har taci riba sai d'aga kai take daga baya ya taya ta murna yace in akwae wanda yay farinciki sosae yadda Al'amarin ya kasance bayan ita to shine k'arshe yayi masu Addu'oi sosae tana ta amsawa a hankali, bayan ya gama yace "Yanzu Mom Zarah bazamu d'aga k'afa ba dole a biya mu d'an G.r.a d'in mu gaskiya" da sauri ta tashi ta nufi hanyar Bedroom da gudu Abbas d'in nata dariya.
Bayan Magrib Haisam d'in ya dawo da K'aramin trolley d'in kayan daya d'aukko mata ta tarbeshi ta amshi kayan yace Hajiya na gaishe da ita tay murmushi kawae, saida akai sallar isha suka yi tare a cikin d'akin sannan yace ta shirya su fita, doguwar riga tasa tay rolling veil bayan ta gama suka tafi, wani babban Eatery ya kaisu suka ci Abincin bayan sun gama sun baro wurin wata plaza ya nufa lokacin da suka shiga bin wurin da kallo Fatuu tayi tana jin kaman tasan wurin bayan yayi parking a inda aka tanada yace mata yana zuwa ya bud'e Motar ya fita, daga baya ta tuna sun ta6a zuwa da shi lokacin da ya siya mata kayan gym, shagon ya shiga bada jimawa ba ya fito hannun shi ruk'e da yar babbar leda mai d'auke da tambarin wurin ya dawo, bayan ya bud'e Motar ya shiga a seat d'in baya ya aje abunda ya siyo ya ja Motar suka bar wurin, zagaya gari ya shiga yi da ita hannun su ruk'e dana juna suna ta hira irin ta masoya masu tsananin k'aunar juna saidai ita Fatun wani lokacin harda sokana sosae kuma yake jin dad'i in tana mashi sangarta, sai after 10 suka koma gida bayan ya siya mata su ice cream, a daren ranar kusan kashe juna sukai da love da alama yanzu ne suke shan Amarcin,