Sashe 139
Asanadin Makwabtaka Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kiran sallar Asubar farko alarm ya tashe shi, duk da bai jin k'warin jikinshi amman Saboda ya saba yin raka'atanil fajr yasa ya daure ya tashi bayan ya janye Fauzy a hankali, toilet ya nufa yayo Alwala bayan ya fito ya nufi press ya canza kaya zuwa jallabiya kafin ya nufo inda zai yi sallar, bayan ya gama zaune yay yana tasbih yana yi yana kai idon shi kan Fauzy dake ta bacci cikin Duvet fuskar shi a sake kaman zai yi murmushi, yana a wurin har lokacin sallar Asuba yayi ya tashi ya kabbara don ji yay bazai iya zuwa Masallaci ba, bayan ya gama yayi Addu'oi kafin ya mik'e ya nufi gadon, bayan ya haye yana k'ok'arin janyota jikinshi ta fara motsi a hankali ta fara bud'e idanuwan ta, tana bud'e su suka shiga cikin nashi ba laifi sun d'an k'ara washewa amman duk da haka yanayin su basu dawo daidai ba sunyi kalar na mara lafiya, bin shi da kallo tayi yay mata murmushi yace ta tashi ta d'an d'aga mashi kai, tambayarta yay ya take ji yanzu da k'yar ta bud'e baki ta bashi amsa da da sauki ya kai hannu yana shafa mata kai yace zata koma normal in sha Allah ta d'aga mashi kai, shiru suka d'an yi can yace mata ko tana jin yunwa ya samo mata abunda zata ci ta d'an girgiza mashi kai alamar a'a sai kuma ta tambaye shi gari ya waye ne yace mata eh anyi sallar Asuba ita ya gama yanzu, tana jin haka ta fara k'ok'arin tashi zaune ganin haka ya kai hannu ya taimaka mata, bayan ta zauna ya tambayi salla zata yi ta d'an yi shiru sai kuma tace mashi so take ta koma d'akin da suke in taje tayi sallar a can, ce mata yay miyasa ta damu da ta koma ne nan ba d'akin mijinta bane kuma ai ba komai don ta zo don anan ma zata zauna kafin su tafi UK, yamutsa fuska tayi kaman zatai kuka tace tafi son ta koma can in suka tafi sai ta dawo nan d'in yace Ok ta fara yin sallar, shi ya taimaka mata ta mik'e da k'yar ta fara taka k'afafun tana yin tafiya a hankali yana mata sannu k'arshe ma ganin yanayin tafiyar tata sai kawai ya d'auketa ya nufi toilet da ita, bayan anyo Alwalar Hijab d'in da tazo da ita ta saka kafin ta kabbara sallar, bayan ta gama ne ya nuna mata ya za'ai ta koma can a wannan halin ko tafiya bata iya yi sosae tace mashi gara dai ta tafi in ta zauna anan kowa zai san abunda ya faru gashi ba gama hidiman bikin akai ba ko yau ma za'a yi Walima, shi kan shi bai son abun ya bud'u hakan yasa yace suje ya rakata, farko kama mata hannu yay tana tafiya a hankali ganin bata sauri yasa shi d'aukarta tana ta fad'in don Allah ya ajeta kar a gansu yace mata ba wanda zai gansu tunda Asuba ne baza'a fito yanzu ba, suna zuwa bakin kopar Falon su tace ya ajeta shi da wai har cikin Falon zai shiga da ita ta kafe sai da ya sauketa, saida ta kalle shi sannan ta juya yay tsaye yana kallon ta har ta shige, tsaye tayi a bakin k'opar shiga Bedroom d'in da suke tana zullumin shiga can wata zuciyar ta raya mata to da tayi tsaye nan in kuma wani ya fito daga wani d'akin ya ganta fa, yin wannan tunanin yasa ta kai hannu a d'arare ta tura kopar a hankali, tana sa kai cikin d'akin suka had'a ido da Fatuu dake zaune akan abun salla bata dad'e da gamawa ba, har saida gaban Fauzy ya fad'i da suka had'a ido cikin kama kai da sauri ta janye idonta ta nufi ciki, cike da k'arfin hali take tafiya a k'ok'arinta na kada a gane saidai duk yadda taso tayi tafiyar sosae abun yaci tura dole a hankali take taka k'afafun, a bakin gado ta zauna tak'i yarda ta k'ara kallon Fatuu bayan d'an wani lokaci Fatuu ta taso ta nufo gadon itama ta zauna a gefenta tana kallonta da murmushi tace mata ta dawo, kai ta d'aga mata ba tare da tace komai ba sukai shiru can Fatuu ta dafa Shoulder d'inta tace mata ya akai ne wai sai lokacin ta d'an kalleta tana k'ok'arin k'ak'alo murmushi tace mata ba komai, Aunty Mareeya ce ta fito daga cikin toilet tana yarfe ruwa ganinta saida gaban Fauzy ya fad'i sosae tayi saurin janye idonta, nufo cikin d'akin tayi tana fad'in "Zarah kin gama sallar ki ara man Hijab d'in ita waccan mai amso sak'on ta tafin man da Hijab saida dama nace...." bata k'arasa ba sakamakon ganin Fauzy da tayi a gefen Fatuu, da sauri ta nufo inda suke ta tsaya daga gaban su tana fad'in ashe ta dawo Fatuu ta d'aga mata kai, tana kallonta tace "ke malama mai amso sak'o sai muji ki shiru kika sa munata zaman jira ko kayan dad'i ne ya siyo maki ki kawo mu tattamna muma" shiru bata ce mata komai ba bata kuma kalleta ba ganin haka yasa ta kirata "Fauziyya" shiru bata amsa ba, kallon Fatuu tay tace mata ya akai ne ta d'an rausayar da kai tace bata sani ba, tambayarta Fatun tayi yaushe ta dawo tace mata bada dad'ewa ba bayan ta gama salla itama tayi mata magana ta ganta haka, jinjina kai Aunty tay ta juya kan Fauzy ta kai hannu ta d'ago Fuskarta da d'an murmushi tace "Yar gidan Hajiya ya akai ne ko mun fara yar kunya ne" tana rufe baki Fauzyn ta fashe mata da kuka tare da kifa fuskarta a jikinta, d'an gwalo ido Aunty tay sai kuma ta fad'ad'a murmushinta ta kai hannu tana d'an bubbuga bayanta tana fad'in ya isa to miye abun kuka, jin yadda take ta kukan ne yasa ta d'ago fuskarta tana share mata hawayen tana fad'in ya isa Shikenan haka girma yake zuwa ma mutum, kukanta ne ya tashi Yaya Fareeda dake bacci da yake bata salla, tambayar Aunty tayi lafiya take kuka tana faffad'an murmushi tace mata ba komai Yaya Fareedar bata kawo komai a ranta ba don jiya tayi bacci aka tafi da Fauzyn, zama Aunty tay kusa da ita daga d'ayan 6angaren a hankali tace mata akwae abunda ke mata ciwo ne ta d'aga mata kai ta tambayi mike mata ciwon cikin muryar kuka tace duka jikinta, d'an jimm tayi tana ta kallonta can tace badai ta samu matsala ba ko tace mata likita tazo ta dubata tace wai ta rink'a zama a ruwan zafi sai magunguna da ta bata, a hankali suke Maganar amman duk su Fatuu na ji, jawota Aunty tay jikinta tana bata hak'uri tace zata daina jin ciwon bada dad'ewa ba sai faman murmushi take, tambayarta tayi yanzu ta zauna ruwan zafinne ta girgiza mata kai alamar a'a tace Ok bari tayi salla sai ta taimaka mata ta d'aga mata kai, mik'ewa tay tace ma Fatuu ta bata Hijab d'in jikinta bayan ta amsa da sauri ta nufi wurin yin sallar, bayan tafiyarta cigaba da yin sheshsheka Fauzy tay wani irin tausayinta ne ya kama Fatuu ta d'agata tana bata hak'uri tare da yi mata sannu haka ma Yaya Fareeda kai kawai take d'aga masu, bada jimawa ba Aunty ta gama sallar ta nufo su tana cire Hijab ta mik'a ma Fatuu kafin ta kalli Fauzy tace suje Toilet din, mik'ar da ita tayi har zasu tafi ta dakata tare da kai hannu tana fad'in a cire Hijab d'in ko, tana cirewa tabi kayan jikin Fauzyn da kallo kafin ta saki yar dariya tare da Fad'in "Sunan wani k'anin tsohon mu Baba Salmanu, wannan kayan fa?" tana rufe baki su Yaya Fareeda suka kwashe da dariya da sauri Fauzy ta fad'a jikinta tare da sakin wani sabon Kukan, rarrashinta ta shiga yi tana fad'in tayi hak'uri shegen bakinta ne da bai gani yayi shiru taga bada su ta tafi bane shiyasa ta tanka, da k'yar ta samu tayi shiru tayi ma su Fatuu alamar su daina yin dariyar kowa ya gumtse ta kamata har zasu tafi tace ma Fareeda ta bud'e akwatin Fauzy ta d'aukko mata towel ta kawo mata sannan suka nufi hanyar toilet tana tafiya a hankali Aunty Mareeyar tana ta mata sannu harda cewa ko ta goyata da sauri ta girgiza mata kai alamar a'a, Bayan sun je toilet d'in a cikin bathtub ta tara ruwan zafin bayan ta toshe tasa Fauzy ta cire dogon wandon baccin da yake rigar ta rufeta sosae ta kawo mata har wurin gwuiwa, itama saida ta tittirje mata wurin zauna ruwan ganin yadda take yi ne yasa Aunty ce mata wai ta tabbatar bata samu matsala ba cikin nishi tace mata eh likitar ta dubata amman tace ta samu rauni, yamutsa fuska Aunty ta shiga yi tana d'an Jujjuya kai alamar tausayi kafin tace "shi kuma surukina ya da gaggawa haka, duk da dai abun farinciki ne amman banji dad'i ba d'an jakar uba ya wahalar man dake" tana rufe baki cikin yamutsa baki Fauzy tace "Aunty ki daina zagin shi shima yace bada son ranshi hakan ya faru ba" gwalo ido Aunty tay da alamun Al'ajabi tace "iyyeee, ah lallai miji dad'i, to tuba nike your Excellency ayi hak'uri su6utar baki ce" tayi Maganar tare da d'an harararta Fauzyn ta d'an tura baki tana kikkafta idanu kaman zatai kuka, sosae ta sakata ta zauna ruwan daga baya ta baro mata toilet d'in tace tayi wanka, after some minutes ta fito d'aure da towel d'in da Aunty ta kai mata su kuma kayan baccin Sameer d'in ta ninkosu lokacin Fatuu bata a d'akin taje tay feeding su twins da yake wurin su Mom suka kwana sai Yaya Fareeda itama har ta koma bacci, taimaka mata Aunty ta shiga yi ta shirya cikin doguwar jallabiya ta d'aura kallabin Aunty tace mata tasan bata rasa jin yunwa ko ta d'aga mata kai alamar eh, shiru tayi tana d'an tunani kafin tace ina wayarta ta kira shi tace tana jin yunwa, sai lokacin ta tuna da ita taje part d'in nashi hakan na nufin ta manto ta can ta fad'i mata,