Sashe 15
Asanadin Makwabtaka Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da yamma wurin sallar la'asar Fatuu ta fito daga wanka, bayan ta zura doguwar riga ta kabbara salla, tana gamawa ta nufi gaban dressing mirror ta fara shirin zuwa part d'in Hajiya, tun bayan daya d'aukkota daga school suna dawowa suka ci Abinci ko wanka bai bari tayi ba suka kwanta bacci, sai da aka fara kiran sallar la'asar ya farka yaje yayi wanka bayan ya fito ya shirya ne ya tasheta ya sanar da ita time d'in salla yayi, tana cikin yin shafan aka yi knocking k'opar Bedroom d'in ta juya ta nufi kopar, tana bud'ewa suka had'a ido da Fanan ta sakar mata murmushi tana sanye da fitted gown ta lace dark blue fuskarta ba wani makeup sai lip glow data shafa a baki sai kuma yanayin fuskar bata rasa shafa powder yar kad'an ta yafa mayafi mahad'in kayan a saman kafad'ar ta, murmushi itama Fatun tayi mata ta kira Sunanta kafin ta gaishe da ita, ce mata tayi ta shigo mana tace a'a bari ta jirata a parlor dama tana son zata rakata wurin gwaggo ne da sauri tace mata to, komawa ray cikin d'akin cike da zumud'i ta d'auki waya ta kira Haisam bayan yayi picking ta sanar dashi zancen fitar yace ai Fanan dama tayi mashi magana sai sun dawo sukai sallama cike da nuna k'auna, ba 6ata lokaci ta k'arasa shiryawa bata canza kaya ba sai kawae ta yafa mayafin rigar jikinta ta d'aukki wayarta ta fita.
A parlor suka zauna gwaggo nata faman sakin murmushin yak'e dama tun lokacin da suka zo tayi arba da Fanan saida gabanta ya fad'i, wani irin nauyi da kunyar Fanan d'in ne suka kamata duk ta bi ta kama kanta a haka suka gaisa tayi mata an zo lafiya da tambayar yan gidan su, lokacin Mino ta tafi islamiyya Amadu kuma yana a shago saida ma suka tsaya ya gaisa da Fanan kafin su shigo, Fatuu ce ta mik'e taje ta d'aukko mata ruwa da lemu don ta lura da yanayin gwaggon, bayan ta zuba mata cup ta mik'a mata ta fara sha, da k'yar gwaggo ta mik'e tace bari a kawo mata Abinci, da sauri Fanan d'in tace "No gwaggo ban dad'e dana ci Abinci bana jin yunwa" still murmushin yak'e gwaggo ke tayi tace "amman d'iyata Fanan ai a d'an ci na zumunci ko Yaya ne tunda yaushe rabon da acin" tana Murmushi tace mata kar ta damu ai tasha ruwa da lemu sai kuma tace "Da dai akwae dambu da na ci"
da sauri gwaggo tace "ah in shi kike so sai in yi maki yanzun nan" girgiza kai Fanan tayi tace ba sai tayi wahala ba tunda babu, da sauri gwaggon ta k'ara cewa "ai ba wani abun wahala tunda komai akwae bari kiga yanzun nan a yi" tana rufe baki ta juya ba tare data jira cewar Fanan d'in ba,
tun bayan data fara aikin girkin dambun take ta faman sambatu ita kad'ai, wani lokacin ta girgiza kai duk ta bi ta damu, Kallo suka cigaba da yi sai dai Fanan ba wani kallon take ba tafi yawan d'aga kai ta kalli sama kaman mai yin tunani sai jefi jefi take sauke idon ta kalli Tv, gaba d'aya Fatuu duk ta damu da yanayin ta don akwae alamun damuwa a tattare da ita hakan yasa bunu bunu sai ta kalleta, suna haka can ta kalli Fanan d'in suka had'a ido ta k'ak'alo d'an murmushi itama Fanan d'in fuskarta a d'an sake tace mata "Sis Zarah kinata kallo na tun d'azun da wani abu ne?" da sauri Fatuu ta girgiza mata kai ta maida idon ta k'asa , kaman daga sama taji tace "ko ina baki tausayi ne?" da sauri ta d'ago ta kalleta idon Fanan d'in akanta da alama amsa take jira da k'yar Fatuu ta d'an d'aga mata kai alamar eh kawai sai gani tay ta mata wani kallo mai kaman harara tace tunda ta k'wace mata miji ba dole taji tausayin ta ba, a rud'e Fatuu tace "a...a Aunty Fanan don Allah ki yi hak'uri.... " idanun ta har sun ciko da k'walla sai kawae gani tay Fanan d'in ta yi dariya tace tana tsokanarta ne, cigaba da kallon sukai saidae duk Fatuu jin ta take wani iri don tasan dama damuwar Fanan d'in bata wuce kan Haisam, ba'a d'au wani dogon lokaci ba gwaggo ta gama yin dambun yasha zogale da gyad'a da albasa sai uban k'amshi ke tashi, saida tazo ta tambayi Fanan d'in da k'uli take so ko yaji tana murmushi tace a kawo duka sai tasa taji wanda yafi dad'i gwaggon tace to, a d'an babban plate ta zubo mata bayan ta aje ta kalli Fatuu da d'an murmushi tace itama zata ci ne ta d'an tura baki tace eh mana, tana niyyar fita Fanan tace ta bari su ci tare in basu k'oshi ba sai a k'aro masu gwaggo ta washe baki tace to, suna cikin cin Abincin Mino ta dawo daga islamiyya ta shigo tana ta fara'a ta duk'a ta gaida Fanan itama tana murmushi ta amsa mata daga baya ta gaishe da Fatuu kafin ta mik'e don taje ta cire Uniform, anan sukai sallar Magrib bayan sun gama suka fara shirin tafiya Fatuu taje ta sanar ma gwaggo zasu tafi, tana sanye da hijab da tayi salla tazo parlon lokacin Fanan na zaune a kan kujera itama ta zauna tana murmushi cike da k'arfin hali ta fara Magana "Y'ata Fanan inata so in baki hak'uri kan yadda abu ya faru tun d'azun nauyin ki yasa na kasa, nasan dole an maki ba daidai ba dole kuma hakan ya jefa ki a halin matsananciyar damuwa, don Allah kiyi hak'uri, duk ta wani bayani ba shi bane tunda mai faruwa ta faru" d'an murmushi tayi tace "No gwaggo ba komai, ni musulma ne na yarda da k'addara mai kyau da mara kyau and I hope wannan ya zama mai kyau, kawae ina son ki ma Zarah magana taci gaba da d'aukana matsayin sister nata ba kishiya ba, kuma duk abunda take so ma kanta ni ma ta so man....." Kuka ne ya taho mata da sauri tasa hannu ta rufe idanunta a rud'e gwaggo ta hau lallashinta kafin ta juya kan Fatuu ta fara mata Nasiha can ta maida Maganar da harshen fulatanci ta ce mata kar ta sake ta canza mata ta rink'a kyautata mata sosae samun abokiyar zama irinta a yanzu zai matuk'ar wahala idan ma tayi mata wani abu da bata ji dad'i ba ita ta fad'i mata zata bata shawara, haka tay mata fad'a sosae Fatun nata k'walla tana d'aga mata kai, daga baya ta had'a su gaba d'aya tayi masu Nasiha, sosae tayi ma Fanan godiya da Addu'oi tana ta amsawa a hankali, ce masu tayi bari ta zuba masu dambun su kai ma Hajiya, lokacin data zubo ta fito har sun fito tsakar gida Mino ma ta fito daga cikin d'akin Fatuu na da yanzu ita ce a ciki, har waje bakin shagon Amadu suka rako su Fatuu ta amshi kular dambun Amadu ma ya fito sukai sallama cike da nuna jin dad'i, jikin gwaggo ba K'aramin sanyi yay ba sai dai kuma yanzu hankalin ta ya fara kwanciya sosae.
Bayan sun koma gidan part d'in Hajiya suka wuce, lokacin da suka shiga ba kowa a cikin parlon dama Hajiya sai tayi sallar isha take fitowa, d'akin da Fanan d'in ta sauka suka wuce bayan Fatuu ta je Kitchen ta aje dambun, yar hira suka shiga yi suna haka aka kira sallar isha. Bayan sun gama sallar Parlor suka fito suka zauna suna yin kallo, basu dad'e da zama ba Hajiya ta fito ta nufo cikin parlon, bayan ta zauna gaba d'aya suka gaishe da ita ta amsa tace masu an dawo ya Dijen, amsa mata sukai da tana lafiya tana gaishe da ita Fanan ta sanar da ita an bada dambu ma a kawo mata tace dambu Dijen tayi kenan aikuwa zata ci don ta kwana biyu bata ci shi ba, Fanan tace ita aka mawa, jinjina kai Hajiya tayi tana murmushi tace lallai Dije na ji da ita, Fatuu ma murmushi take ta mik'e don ta d'aukko mata, A plate ta zubo mata ta sako mata spoon ta dawo cikin parlon, tana niyyar d'aurawa saman sofa table ta kinkimo mata shi Hajiyar tace mata ta barshi ta bata, tambayarta tayi lemun da zata d'aukko tace ta bata ruwa kawae, juyawa tay ta koma hanyar Dining don ta d'aukko, sosae taji dad'in dambun tana ta yabawa Fanan na yar dariya tana fad'in kodai santi take, suna haka Haisam ya shigo cikin parlon hannuwan shi ruk'e da manyan ledoji, kusan a tare Fanan da Fatuu suka mik'e suka nufe shi kowa ya amshi leda guda tare da yi mashi sannu da zuwa yana murmushi ya amsa, Hajiya na yar dariya tace sun hutar da ita ita Uwargida duk sukai yar dariya, bud'e wadda Fanan ta amsa tayi taga su ice cream ne da snacks ta hannun Fatuu kuma Fruit ne, ce ma Fatuu tay taje ta zubo a plate sai ta taho da wasu a zuba snacks d'in ta amsa da to tana niyyar juyawa suka had'a ido da Haisam ya lumshe mata idanu tay d'an murmushi kawae ta wuce, bayan ta dawo kowa aka zuba mashi su shawarma suka d'auki ice cream Hajiya tace bazata sha shi ba Fanan d'in tace mata to akwae Fura a bata tace eh, k'arshe dai basu ci Abincin dare ba don duk sun k'oshi da abubuwan daga baya wurin k'arfe goma Haisam da Fatuu sukai masu sallama Fanan harda yi masu rakiya bakin k'opa bayan sun tafi ta dawo.