← Book details Asanadin Makwabtaka Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 211

Sashe 29

Asanadin Makwabtaka Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Ai weekend ne irin su ake sawa yau" ya fad'a yana murmushi k'ara waro ido tay a d'an rud'e tace "amman ni ai ba yar gidan bace bak'uwa ce kawae sai in saka wannan kayan in fita ai wllh cewa ma za'ai banda kunya" yar dariya yay jin Maganan da tayi wai ita ba yar gidan bace, tambayar ta yay to miyasa ta taho da su in bazata saka ba tace "ai dama ko zan sa zan d'aura after dress ne a sama ba hakanan ba sai dai in kasa a d'aukko man after dress d'in sai in d'aura" shiru yay yana bin ta da kallo kawae har saida ta k'ara ce mashi "ka ji hubby k'asa a d'aukko man tana nan acikin kayan" sigh yay ya tambayi ba wasu ne sai wannan da sauri tace mashi akwae mana su atampa da lace duk akwae lumshe ido yay ya d'an girgiza kai yace mata ba irin su yake nufi ba irin wanda aka d'aukko mata tace eh akwae wasu, mik'ewa yay daga zaunen da yake a gefen ta ya nufi hanyar fita daga cikin d'akin ta bi shi da kallo har ya fita sannan ta maido idon ta kan kayan ta fara imagining kanta sanye da su a fili tace "tabb wayaga mara kunya", yana fita parlor yace ma Jidderh suje ta mik'e, d'akinta suka nufa bayan sun shiga daga bakin k'opa ya tsaya yace ta d'aukko mashi trolley d'in Fatuu tace to, bayan ta d'aukko mashi ya amsa yace ta jirata anan zata dawo yanzu tace to, part d'in shi ya koma tana zaune ya shigo da akwatin ya nufi inda take, a saman gadon ya d'aura shi ya bud'e da kanshi ya hau duba mata wanda zata saka dama k'ananun kayan ba su da yawa basu fi ukku ba koda aka fiddo sauran biyun suma duk saida tayi k'orafin sun kamata yace dole ta saka d'aya ciki, k'arshe wani bakin pencil skirt da bakar riga v-neck mai dogon hannu tasa sai faman yamutsa fuska take tana fad'in ita gaskiya after dress zata saka yace da yake unguwa zata je ko, shi ya taimaka mata ta gyara fuskarta da gashinta bayan sun gama yace ta saka hula su tafi lokacin breakfast yayi kar a jira su rigima ta fara mashi tana fad'in wai ya za'ai ta fita haka don Allah dama gashi tazo d'akin shi kuma duk ansan ba anan ta sauka ba, still yay yana kallonta ya goya hannuwan shi a chest, suna haka akayi knocking k'opar har saida Fatuu ta d'an tsorata, nufar k'opar yay ya bud'e ganin Mom d'in shi yasa shi sakin k'ayataccen murmushi ya ambaci sunanta tana sanye da jar polo shirt ta mata da dogon bakin skirt kanta sanye da bakar hula abun sai dai ace Tubarkallah, k'arasa fitowa yay ya rungumota jikinshi yana gaishe da ita ta amsa tana murmushi, bayan ya saketa tace "nazo tafiya da wadda kaje ka d'aukko, in kai baka jin yunwa ita ce maka akai bata ji da zaka ruk'eta ka hana tazo tayi breakfast har kiran ka akai ta landline baka d'auka ba" tana d'an hararar shi ta k'arasa Maganar yana murmushi ya bata hak'uri yace dama yanzu zasu fito tace Ok su kad'ai ake jira, har zata juya yace bari ya kirata sai su tafi tare tace Ok, juyawa yay ya koma d'akin Fatuu dake zaune a bakin gado ta d'aga ido ta kalleshi ya nufa ta, a gabanta ya tsaya yace ta tashi ga Mom nan tazo tafiya da ita yamutsa fuska ta fara yi ya d'aure mata tashi kawae sai ta fara ta6e baki bud'a ido yay alamar mamaki sai kuma yay murmushi yace bari yay ma Mom d'in magana sai ta shigo ta tafi da ita tana jin Haka ta mik'e da sauri, zuciyar tace ta bata ta d'aukko gyale tay rolling da sauri ta juya wurin kayan ta, bayan ta d'aukko ta nad'a duk da haka bai rufeta sosae ba amman dai taji gwara hakan, tare suka fito tana biye dashi Mom d'in har ta zauna akan kujera, suna had'a ido da Fatuu ta sakar mata murmushi, wurinta ta nufa a kunyace tana zuwa ta fara k'ok'arin zama a k'asa Mom d'in ta kamo hannunta ta zaunar da ita akan kujera kusa da ita, cikin jin kunya Fatuu ta gaishe da ita ta amsa mata tayi mata ta tashi lpy tace lafiya lau, mik'ewa tay ta kamo hannun Fatun tana fad'in suje tayi breakfast Habiby ya ruk'eta kuma tasan bata rasa jin yunya gaba d'aya kunya ce ta rufe Fatun, bayan sun saukko k'asan kasa d'aga ido tay ta kalli Mutanen dake a Dining area d'in wata irin kunya ta lullube ta, Haisam ne yaja seat yace ta zauna Mom ta koma gefen Senator ta zauna bayan ta zauna shima yaja kujerar gefen ta ya zauna, da k'yar ta d'ago ta gaishe da Senator idon shi akanta yana murmushi ya amsa yace "My Daughter how was ur night, hope u slept well" kai ta d'aga mashi yace haka yake so, juyawa tay ta gaishe da Hajiya itama ta amsa tana d'an murmushi, kallon Aunty tay ta gaishe da ita tana murmushi itama ta amsa tayi mata ta tashi lpy bayan ta amsa tana niyyar gaishe da Laila ta riga gaishe da ita a kunyace itama Fatun ta maida mata gaisuwar ta amsa tana mata murmushi komai nata burgeta yake bama ita kad'ai ba kusan kowa ma, dama akwae mutanen da zaka ga suna da farinjini sosae kowa son su yake sai wad'anda ba'a rasa ba tunda ance Abincin wani dama gubar wani ne amman dai Fatuu tana burge mutane sosae, sauran yaran ma duk suka gaishe da ita harda su twins Nameer k'in gaishe da ita yayi saidae ita ta gaida shi saida ya ga dama sannan ya amsa har Senator na ce mashi shi bai gaishe da ita ba tana Yayar shi kuma ta gaishe shi sai ya mula zai amsa ya kalli Dad d'in yana murmushi Hajiya tace wannan ya k'yale su kawai sun saba Senator d'in yace oh to ya gane duk akayi murmushi, Fatuu Senator yasa tayi masu Addu'a bayan ta gama suka fara cin Abincin a nutse tun Fatuu bata saki jiki ba har sai ta washe taci gaba da cin Abincin ta.

Bayan sun gama Jidderh ta ja ta d'akinta Mom d'in Haisam tace mashi tana son zasu yi magana suka nufi cikin parlon , a saman doguwar kujera suka zauna suna kallon juna tace mashi dama Maganar dangin ita Daughter ne bata san ko anyi Magana ba yakamata suzo yace mata eh sunyi Magana da Dad jiya za'a tura Mota a d'aukko su tace hakan yayi amman a tura da wuri ba sai lokaci ya k'ure ba Saboda su kar6i lefen ta yace Ok, bayan sun gama Maganar sama ya haye ya koma part d'in shi, a parlor ya zauna ya fara k'ok'arin kiran Abbas, bayan yayi picking sun gaisa yayi mashi Maganar Alhaji Lawal kaman yadda sukai da Dad d'in shi Abbas d'in yace Ok zai kira shi da sun gama wayar sai aji in zai samu zuwa, Maganar dangin su Fatun ya k'ara yi mashi nan ma yace in suka gama zai kira gwaggo sai aji yadda za'ai Haisam d'in ya tambaye shi su yaushe zai taho da su yace yana tunanin ran Wednesday, hiran yadda abubuwa zasu kasance suka shiga yi kafin daga baya sukai sallama,

Suna gama wayar ya kira Alhaji Lawal d'in bayan sun gaisa a mutunce Abbas ya fara mashi bayani game da bikin, sosae ya nuna jin dad'in shi yace ai wannan ba wani abu bane, shi a wurin shi ma girmama shi akai dama kuma lokacin yana a Abujar, nan yake sanar ma Abbas d'in yana shirin tsayawa takarar d'an majalissar tarayya ne a zabe mai zuwa Abbas d'in yayi mashi fatan Alkhairi yace in sha Allahu yana nan zuwa daga baya sukai sallama, Gwaggo ya kira bayan ta d'aga sun gaisa yayi mata Maganar zuwa d'aukko yan Adamawan cike da Farinciki ta hau godiya tace zata masu Magana sai su shirya dama jiya da daddare suke Magana da Baffan Fatun kan bikin yake tambayar ta ko za'a je daga nan tace ya bari sai ta tambaya Abbas na dariya yace ma gwaggo ai ba sai an wani tambaya ba suna da hakki suje itama dariya take tace hakane wai dai kar ayi ba daidai ba, nan yake sanar mata suma ran Wednesday zasu tafi tace to Allah ya kaimu suka yi sallama.
Chapter 29 · 0% Book details