Sashe 12
Asanadin Makwabtaka Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan ta koma parlor duk ta bi ta kama kanta Hajiya tace ya tafi ta ce eh, bata dad'e da komawa ba Mino tazo jikinta sanye da Uniform d'in islamiyya taje can part d'in bata isketa ba, tana murmushi ta gaishe da Hajiya itama da fara'a ta amsa tace mata an dawo tace mata eh Fatuu ta nuna mata gefen ta alamar tazo ta zauna, bayan ta zauna Hajiya tace jiya bata zo tayin kwana ba maigida ya dawo, ita dai Minon murmushi kawae take yi cike da wasa ta sake ce mata ai da tazo ta taya ta ita duk suka d'an yi dariya, bata dad'e ba sosae ta mik'e zata tafi, bayan ta masu sallama Fatuu tace ta gaida mata da gwaggo, daga baya itama Fatun mik'ewa tay tace bari taje ta taya Aunty Saude aiki a Kitchen, Lokacin da akai Azahar sun gama komai ta wuce d'akin Aunty Sauden don tayi salla, bayan ta gama sallar ne ta fito ta nufi d'akin da Fanan take, da sallama ta tura kopar ta shiga, a saman abun salla ta hangota daga gaban gado tana jingine dashi ta juyo tana amsa mata sallamar da d'an murmushi, sosae gaban Fatuu ya fad'i da ta k'arasa wurinta taga idanunta a haka ma wai don ta samu bacci sun rage, gabanta ne ya shiga fad'uwa Fanan d'in ta nuna mata gefen gado tace ta zauna mana tayi tsaye, bayan ta zauna a sanyaye ta gaida ita ta amsa kafin tace taso taje ai can part d'in nata su gaisa bata tashi da wuri bane, cikin kama kai Fatuu ta d'an yi murmushin yak'e tace mata ai tun d'azu itama tazo ta shigo ta gaida ita ta iske tana bacci, sama sama suke d'an yin hira yawanci ma Fanan d'in ce ke kawo zance anan har take tambayar ta gwaggo tace zata shiga su gaisa in sha Allah, suna haka Haisam ya shigo duk suka yi mashi sannu da zuwa fuskar shi a sake ya amsa ya nufi mirror ya d'aukko stool ya dawo daga gefen gadon ya zauna, gaba d'aya Fatuu ta takura Saboda yawon kallon da yake mata har fakar idon Fanan tay ta d'an mashi alamar ya daina sai kawai taga yayi d'an murmushi, gaba d'aya su biyu ke yin hiran sama sama sai ta kama sannan Fatuu ta saka masu baki, daga baya Saude tazo tayi masu Maganar an shirya table bayan ta fita Fatuu ce ta fara mik'ewa dama duk a takure take cikin wasa Haisam d'in yace mata acici bazata jira su tafi tare ba sai kuma kunya ta kamata tana niyyar komawa ta zauna ya mik'e yana yar dariya Fanan ma yar dariyar tay ganin bata tashi ba yayi mata magana ta d'an yamutsa fuska tace gaba d'aya bata da appetite ne yace ta dai daure kar ta zauna da yunwa, mik'a mashi hannu tayi alamar ya taimaka mata ya kama hannun ya mik'ar da ita, bayan ta mik'e ta fara k'ok'arin cire Hijab din jikinta Haisam ya kai idon shi kan Fatuu dake kallon su suna had'a ido da sauri ta maida kan ta gefe, moving yay zuwa inda take yace su je ba tare data kalle shi ba ta wuce yana biye da ita Fanan kuma na gefen shi. Bayan sun fara cin Abincin Haisam na lura da Fanan bata wani ci kaman dai jiya can ya d'ebo ya kai spoon d'in bakinta da yake tana a gefen shi, kallon shi tay da murmushi yay mata alamun ta ci ta bud'e bakin ya bata, ci gaba yay da bata tunda Fatuu taga haka ta daina kallon su, sai gashi taci sosae, gaba d'aya Fatuu jin ta take wani iri hakan yasa taji Abincin ma ya fitar mata a rai hakanan take d'an tsakura gudun kada ta tashi ai tunanin wani abu, can bayan an k'ara lokaci ta mik'e duk suka kalleta da k'yar ta k'ak'alo murmushi tace ta k'oshi, Fanan ce tace mata amman ai kaman fa bata ci da yawa ba still da murmushin tace ai bata dad'e da yin Breakfast ba tazo ta d'aga mata kai alamar gamsuwa, idon Haisam a kanta ita dai Hajiya d'an murmushi kawae take a ranta ta raya aiki ya ga Haisam don tasan dama dole Fateema bata rasa jin wani abu a ranta a kan Abincin da yake ba Fanan d'in a baki, d'akin Saude ta wuce don acan ta aje gyalen ta, lokacin da ta shiga ba kowa a d'akin don Sauden na can baya ta nufi katifa ta Zauna tay shiru tana kallon wuri guda kaman mai tunanin wani abu, daga baya ma sai ta kwanta kawae,
Bayan su Fanan sun gama cin Abincin Parlor suka wuce Suna kallo saidae gaba d'aya hankalin Haisam na a wurin Fatuu tunani abunda take a cikin d'aki yake ta yi, ana fara kiran sallar la'asar ya mik'e yace zai je Masallaci, bayan ya fito tsayawa yay cikin harabar yana kiran Fatuu a waya saida ya kira har sau biyu amman bata yi picking ba ya juya ya nufi part d'in su a ranshi yana wani tunani, bayan ya shiga Bedroom ne yaga wayar ajiye akan bedside ashe bada ita ta tafi ba ya wuce toilet don yin Alwala, bayan fitar shi Hajiya ma ta tashi itama Fanan d'in ta mik'e suka tafi suma su yi sallar, har Hajiya zata shiga d'aki tayi tunanin Fatuu tace ma Fanan ta duba Fateema a d'akin Saude watak'il bacci take tace to, bayan ta shiga taje ta tasheta tace lokacin salla yayi Fatun tay mata godiya ta mik'e ita kuma ta juyo ta fito, d'aukar gyalenta tayi ta fito daga cikin d'akin lokacin data shigo parlon ba kowa ta nufi hanyar fita ta wuce part d'in su, tana shiga Bedroom ta cire gyalenta a gefen gado ta wuce laundry, bayan ta fito ta yo Alwala ta shimfid'a prayer mat ta kabbara salla.
Tun bayan data gama tayi zaune a wurin tay shiru k'arshe ma sai ta jingina da gado ta kwantar da kanta, Fauzy ce ta fad'o mata a rai ta raya yakamata ta kira ta sanar da ita Ya Haisam ya dawo bata samu ta hau online bane shiyasa data fad'a mata tuni, tana ta zaune can taji an turo k'opar ta kai idon ta, shine ya shigo suka had'a ido bayan ya rufe kopar ya nufota ta d'ago tana kallon shi, tayi tunanin saman gadon zai zauna amman ga mamakinta sai gani tayi ya zauna k'asa a gaban ta ya d'age kafa d'aya d'ayar kuma ya mik'ar da ita tana dai ta kallon shi fuskar ta a d'an sake, kallon ta yake shima saidai yanayin kallon kaman na mai nazarinta ganin haka yasa ta sunkuyar da Fuskar ta ta koma kallon k'asa, tana haka taji Muryar shi calmly yana fad'in "I want to try my possible best to be equitable to you, but I understand it would not be as easy as I think" jin abunda yace yasa a hankali ta d'ago ta kalle shi yanayin damuwa ya bayyana akan fuskar shi, bin shi tay da ido ta fahimci dalilin da ya sa yayi Maganar k'ilan yayi tunanin ko tayi fushi ne Saboda abubuwan da suka faru tsakanin shi da Fanan d'azun, d'an murmushi yaga tayi ta kai hannu ta ta6a gefen fuskar shi da turanci itama tace mashi kar ya damu zata taimaka mashi ya cimma hakan a tsakanin su, d'age gira yay ya tambayi da gaske ta d'aga mashi kai yace kenan bata yi fushi ba, tana yar dariya ta girgiza mashi kai tace fushin mi zatayi ya d'an kashe mata ido guda ya furta kishi, sosae ya bata dariya yadda taga yayi ta fad'a jikin shi a shagwa6e tace to yau ta fara gani ya ba Aunty Fanan Abinci a baki ai tasan yana bata dama, d'age mata gira yay ya tambayi a yaushe tasan hakan tace "a can baya mana lokacin ranar nazo nan gidan har na kawo mata wainar fulawa daga baya da aka ce an shirya table ta matsa man sai munje an ci Abincin da ni, koda naje ma kasa wani ci nayi na taso na dawo parlor, dama ranar da k'yar nazo sai da gwaggo ta ce ya kamata in zo ita ta damu dani tana ta zuwa" a shagwa6e take Maganar gaba d'aya ya zuba ma bakinta ido har ta gama sannan ya k'ara d'age mata gira yace "lokacin kina ciwon so na?" wani kallo tay mashi ta d'an tura baki ya ce ta bashi amsa kawae sai tasa hijab ta rufe fuskarta tana dariya, k'ok'arin bud'e Fuskar ya fara ta bi ta k'ank'ame ta, wani abu ya fara mata yana cigaba da k'ok'arin bud'e Fuskar sai ta ji yanayin yadda take jin abunda yake matan yayi mata kaman cakulkulo ai kuwa cikin d'an k'araji ta fara fad'in "Ya Haisam!....don Allah ka bari.... Wayyo Allah zan bud'e wllh, ka bari don Allah......" ba Arzik'i ta bud'e Fuskar tana haki da dariya, shima dariyar abunda ta rink'a yi yake, ce mata yay to ta fad'i mashi still tana a jikin shi saidai ta zame ta kwanta sosae, d'aga mashi gira tay irin yadda yake mata yace ta bud'e baki a shagwa6e tace "Ehhhhh" d'an bud'a mata ido yay yace "Eh What?" tura baki tay "kai Ya Haisam ba ka gane ba" d'an girgiza mata kai yay alamar bai gane ba ta tura baki, kawai taga ya d'ago hannu aikuwa da sauri ta tare hannun tana dariya tace "Ehh lokacin ina ciwon son ka" sosae yadda tayi Maganar ya bashi dariya sukai tayi a tare saidae ita tafi shi yi,