Sashe 133
Asanadin Makwabtaka Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Washegari bayan sun yi lafiyayyen breakfast wurin k'arfe tara na safe aka sanar wanda za'a maida Funtua su shirya, misalin k'arfe sha d'aya na safe masu tafiyar sun gama shiryawa ciki harda su gwaggo dasu Zainab k'awayen Fauzy iya wad'anda zasu je Nasarawa mutum goma ne aka ware daga dangin Fauzyn harda Aunty Mareeya itace cikon ta goman ko k'annen su maza da mata da suka zo duk komawa za'ai dasu Fatuu dai tana cikin ayarin iyalan Senator dole taje Nasarawa, bayan anyi sallama dasu suka tafi su kuma su Aunty Mareeya suka hau shirin tafiya nasarawa, sai bayan da akayi sallar Azahar sannan aka kwashe su Amarya Fauzy ansha kwalliya tana sanye da babbar atamfa an mata half gown tasa tsadaddun takalma da jaka da kuma gyale da suka hau da kayan nata, su Aunty ma duk sun sha gayu haka ta bangaren Fatuu ma kowa dai yayi kyau. Da yake ba wani nisa ke da akwae ba tsakanin Abuja da Nasarawa basu fi awa d'aya da rabi ba suka isa garin Lafia aka nufi Government House dasu, Alhamdulillah sun isa gidan gwamnati lafiya an yi masu kyakkyawar tarba don anan suka iske su Her Excellency sun riga su isowa, komai dai na gidan mai burgewa ne a part guda aka sauke su yana da babban parlor sai kuma bedroom da zasu kai ukku ko ina an k'awata shi da lafiyayyun furniture, d'aki guda Aunty Mareeya da Fatuu da Amarya Fauzy sai Fareeda suka sauka Aunty sai washe baki take tana fad'in Allah mai iko ko yanzu ta kafa tarihi taje gidajen gwamnati har biyu na Kaduna sai kuma nan Fatuu dai sai dariya take, da yake sai da suka ci suka k'oshi a Abuja kafin su taho d'an abun sha da taunawa aka fara tarbarsu dasu daga baya duk suka kwanta suna huta gajiya, sai bayan da suka yi sallar Magrib ne aka kawo masu lafiyayyun Abinci masu saka kunnuwa su motsa harda farfesun nama da lafiyayyun gasassun kaji da abubuwan sha kai kace wata Walima zasu yi, Aunty Mareeya ce ta zuzzuba ma sauran Mutanen da suka zo tare wanda su gwaggo ne kishiyar Maman su sai Yayye da kuma k'annen mamansu da Baban su sai babbar k'awar maman tasu, bayan ta gama da kowa suma ta zuba masu duk suka zauna anan falo suna ci, suna cikin ci Hajiya Zainab tazo k'ara yi masu sannu da zuwa tana ta fara'a haka suma ta tambaye su ba wata matsala duk suka ce a'a babu komai Alhamdulillah suna godiya Allah ya k'ara d'aukaka ta amsa kafin ta kalli Fauzy data sunkuyar da kai tana murmushi tace " Daughter an sha gajiya ko?" d'an d'agowa Fauzy tayi tana murmushi ta gaishe da ita ta amsa daga baya ta tafi bayan tace ma Aunty Mareeya inda wani abu they should feel free ta kirata tayi magana, bayan tafiyarta ne suka hau yabon ta harda su Mom yadda basu d'auki duniya da zafi ba. Misalin k'arfe goma duk sunyi shirin kwanciya harma sun kwanta saidae basu yi bacci ba suna ta hira har Aunty Mareeya na tambayar Fatuu su twins tace taga tun d'azu basu wurinta tace eh suna a wurin su Aunty Laila, Aunty Mareeyar tace ba ruwan su dai basu da rigima tace mata eh gaskiya in dai suna wurin su basu wata rigima saidai ko in suna jin yunwa kuma da an basu Abinci Shikenan har kwana ma suna yi a wurin su, kallon Fauzy dake kwance jikinta sanye da kayan bacci riga da wando tayi shiru Aunty Mareeya tayi tace "Amarya ya da yin shiru ko kinata tunanin Angon naki ne" d'an murmushi tayi bata ce komai ba Fatuu ta kalleta tana murmushi Yaya Fareeda dai har tayi bacci, Aunty bata dad'e da yin Maganar ba wayar Fauzy ta fara ringing ta kai hannu ta d'aukko ta, bin screen d'in tayi da kallo ganin mai kiran Aunty Mareeya ta tambayi waye ko angon ne a hankali ta d'aga mata kai alamar eh tace to ta d'auka mana ko sai ta yanke, picking tayi ta kara a kunne a sanyaye tayi mashi sallama tana jiyo Muryar shi k'asa k'asa ya amsa suka d'an yi shiru kafin yace mata ya gajiya tayi d'an murmushi tace babu gasu nan suna hutawa yace Ok sai kuma taji yace yana son ganinta gashi nan ya turo za'ai guiding nata inda yake, shiru tayi ta kasa ce mashi komai saida yace bata ji bane sannan ta d'an had'iyi abu tace to daga haka ya katse Wayar, ganin yadda tayi tsuru bayan ta gama wayar yasa Aunty Mareeya tambayar ta ya akai ne ta d'an yi shiru tana kikkafta idanu kafin ta fad'i mata wai cewa yayi yana son ganinta zai bata sak'o, jinjina kai Aunty tayi tana murmushi tace to kuma shine tayi kwance ta tashi taje mana ta tambayi tasan inda yake ne Fauzyn na k'ok'arin tashi ta d'an girgiza mata kai alamar a'a kafin tace yace za'a zo a rakata inda yake ta d'aga mata kai still murmushi take yi haka ma Fatuu, wurin kayanta ta nufa don gaba d'aya akwatunan da aka kai mata sun taho dasu tana niyyar bude wani akwati Aunty tace mi zata dauka tace mata Hijab, ce mata tayi ta manta ba Hijabai a cikin kayan ne tace Oh ta manta wllh ta d'ago duk ta wani sha jinin jikinta, kallon Aunty Mareeya tayi tace don Allah ta ara mata Hijab d'in ta da taga tayi salla d'azun tana murmushi tace to in ta bata kuma da Asuba tana son yin salla fa ta yafa gyale mana da sauri Fauzyn tace ai zuwa zata yi ta dawo yanzu kawai abu zai fad'i mata Aunty tace Uhmm ta nuna mata jakar kayanta tace ta duba tana ciki, bayan ta d'aukko ta saka ta koma bakin gado ta zauna tana jiran mai zuwa ya tafi da ita Aunty tace mata to bazata shafa ko d'an turare ba ta tura mata baki kaman zata yi kuka tace itafa ta fad'i mata sak'o kawai zai bata Aunty tace eh duk da hakan ai yakamata a matsayin ta na Amarya aji tana zuba uban k'amshi tunda shima ta tabbatar sai taji yana sakin kamshi sosae a matsayin shi na ango, jimm tayi tana masu wani kallo ganin su duka suna mata murmushi ta yamutsa fuska tace wai miye suke ta mata murmushi da sauri Aunty tace to kuka take son taga sun yi kawai suna murmushin jin dad'i ne ganin Allah ya nufa ta zama matar aure gashi har mijin nata na kiranta, shiru tayi bata ce komai ba Aunty ta k'ara ce mata ta d'an shafa turaren tace ai ta fesa lokacin da ta saka kayan baccin duk da haka ta matsa mata kan ta k'ara fesawa, tana cikin fesawar suka ji an yi sallama a bakin kopar shigowa d'akin jin muryar mace ce yasa Aunty ta bada izinin a shigo, wata mata ce ta shigo da gani yare ce tana sanye da short skirt baki sai farar riga kanta ba kallabi sai hular gashi daga yanayin shigar ta zaka fahimci kamar uniform ne, wurin gadon ta nufo ta tsaya daga gaban shi tana murmushi ta gaishe dasu Aunty Mareeya da turanci duk suka amsa mata cikin girmamawa tace dama itace aka turo zata tafi da bride Aunty tace to ta nuna mata Fauzy tace mata gata nan, a sanyaye ta nufo matar tana zuwa gabanta ta d'an rankwafa ta gaishe da Fauzyn bayan ta amsa mata ta tambayi zasu iya tafiya ta d'aga mata kai Matar ta shige gaba Fauzy tabi bayan ta tana fara tafiya Aunty tace mata Allah ya basu Alkhairi ta juyo ta tura mata baki duk suka sa Dariya, yar tafiya sukai ta wata hanya suka iso wani Corridor Matar ta dakata ta juyo tana murmushi ta nuna ma Fauzy wata dakakkar k'opa dake kallon su tace mata nan ne part d'in shi ta shiga yana nan ciki ta d'aga mata kai Matar ta juya ta tafi, gabanta na d'an fad'uwa ta tura kopar bayan ta bud'e a d'arare sai kace mara gaskiya ta shiga, tsaye tayi daga bakin kopar tana k'are ma wurin kallo wanda madaidaicin Parlor ne mara hayaniya komai na cikin shi Fari ne da ratsin golden tsit kake ji sai Ac dake ta aiki gaba d'aya ta sanyaya cikinshi ga wani k'amshi mai dad'i dake had'e da sanyin, a ranta ta shiga raya to ko yana ina ganin parlon k'walam ba kowa, tana haka wayarta ta fara ringing har saida ta d'an tsorata da sauri ta d'agota ta kalli screen d'in, shine yake kiranta ta kai hannu tay picking tana karata a kunne kafin tace wani abu taji yace tsayuwar mi take har saida mamaki ya d'an kamata don ta fahimci yana ganinta cikin yar rawar murya tace ai bata gan shi ba, ce mata yay akwae k'opa by her left ta bud'e ta shigo ta amsa mashi da to, tana tunkarar kopar gabanta na faduwa bayan ta isa gabanta d'an jimm tay kamar bazata tura ba sai kuma ta tuna da yana kallonta hakan yasa ta tura bayan ta bud'e ta shiga, Ya Subhanallahi shine abunda na furta lokacin da nayi arba da Bedroom din, shima baida wata hayaniya amman fa ya tsaru kuma shima komai na cikin shi fari ne da golden da alama dai yana son irin had'in kalolin don ko a part d'in shi na gidan daya kaita can ma kayan haka kalar su take duk da ba design d'in su daya ba saidai na ko ina sun had'u, nan gadon round bed ne yana da table a gaban shi sai kuma nightstands da akai masu shape wanda ya hau da gadon daga can gefen gadon babbar press c ta glass ana hangen kayan dake ciki sai opposite da ita nan wani elegant dressing mirror ne suma labulayen cikin d'akin sun tsaru suna da kyau da kuma k'auri, a d'an gaban gadon golden brown d'in carpet ne an mashi ratsin fari kai da gani ba sai an fad'a ba dole zai yi laushi don wani irin gashi gashi ne dashi, daga d'an can gaban inda furniture d'in suke reading nook ne wato wurin karatu akwae yar madaidaiciyar