← Book details Asanadin Makwabtaka Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 211

Sashe 4

Asanadin Makwabtaka Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bedroom ta wuce tana shiga ta nufi bakin gado ta zauna tay zuru tana cigaba da zancen zucinta, sosae Fanan take bata tausayi tasan itama ba K'aramin so take ma Ya Haisam d'in ba yanzu kuma ace ya auri wata tasan dole ta shiga matsananciyar damuwa, mamakin ta yadda akai tay saurin amincewa ba kamar data ce mata saida aka tura sak'on nan ta sani duka kuma ba'a fi kwana shidda ba, wata zuciyar ce ta raya mata wato da ya kasa fad'a mata saida asiri ya tonu ta amince shine suka taho da hakan bata faru ba tasan baida niyyar zuwa, wani abu taji mai kaman 6acin rai ta raya yanzu dai ta tabbatar ba son ta yake ba tunda saida Matar shi ta amince zai waiwaye ta dama kuma tasan Saboda Hajiya yake zaune da ita, rayawa tayi to miye amfanin zaman ta dashi wai tunda bai son ta kawai ya saketa ya huta Aunty Fanan ma ta huta da damuwa, tunanin ta nemi ya saketa ta shiga yi, wata zuciyar ta raya mata tana tunanin a yanzu zai saketa bacin yasan sirrin zuciyarta ita kanta Fanan ai don ta nuna tana son shi ya aure ta, sosae taji bata ji dad'in sak'on da ya gani ba amman duk da haka ta sama ranta zata ce ya sake ta kawai, ta d'auki lokaci a zaunen kafin ta mik'e don taje tayi wanka, bayan ta aje gyalen ta gaban mirror ta tsaya tana kallon kanta ta kai hannu tana cire yan kunnan ta fashion bayan ta cire su ta cire agogon hannunta ta d'aura su akan dressing mirror, daidai ta juyo aka turo kopar Bedroom d'in har saida gaban ta ya fad'i, shi ne ya shigo idon shi akanta yasa hannu d'aya ya tura kopar, a wurin ya tsaya suka kafe juna da ido fuskar shi a sake kaman zai yi murmushi ita kuwa yanayin tata kaman a d'aure, kauda idon ta tayi gefe zuciyarta ta raya mata tsayuwar mi take ta tafi tay wankan ta, nufar hanyar Laundry room tay idon ta a k'asa har tazo daidai inda yake a tsayen, tana niyyar wuce shi kawai taji ya kamo hannun ta na gefen da yake, yamutsa fuska tay fuskarta na kallon gefe wurin gado kirjinta ya hau bugu da sauri da sauri, wani irin haushin shi taji ya kamata wato sai yanzu da aka amince mashi ne zai yi lokacinta ta raya hakan, kaman daga sama taji ya furta "Zaraah" wani kalan murmushin takaici ta yi nan take ta fara k'ok'arin k'wace hannunta, k'ara kiran sunanta yay aikuwa a fusace ta juya idanunta har sun ciko da k'walla tace "ba suna na haka ba sunana Fatuu ka kira ni da hakan" cikin yanayin muryar kuka tayi Maganar tana rufe baki k'walla suka zubo mata sharr da sauri ta juyar da fuskar inda take kallo da, still yay yan kallonta don ya gane dalilin daya sa ta fad'i hakan, k'ok'arin matso da ita ya fara nan take ta fahimci rungume ta zaiyi aikuwa ta tirje ta fara jan hannunta sai ga abu ya zama kaman kokowa, da dai taga ta kasa kwace hannun sai ta fashe mashi da kuka ta fara fad'in ita ya sakar mata hannu, janyota yay ya had'a jikinsu ta kafe tak'i yarda ya mannata da k'irjin shi ta hau girgiza kan ta cikin k'araji take fad'in ita ya k'yaleta, sosae take kuka tana girgiza kai idonta a rufe gaba d'aya ta fara rud'a shi fuska a yamutse yake kallon tata fuskar, da k'yar ya manna ta da k'irjin nashi ya rungumeta gam sai faman kuka take, d'aura ha6ar shi yay a saman sumar ta mai santsi da tuni kallabin dake sama ya fad'i, lumshe idanunshi yay underneath his breath yake furta "am sorry for hurting u Zaraah, it was never my intention" shiru tay tana cigaba da kukan saidae sautin kukan ya d'an ragu sai sheshsheka take ga fitinannan k'amshin jikin shi duk ya cika mata hanci hakan ne yasa natsuwarta ta d'an daidaita, Moving yay da ita zuwa bakin gado ya zauna da ita ta kasance a saman cinyoyin shi har lokacin kuma yana rungume da ita gam, maida ha6ar shi yay saman kan nata breathing d'in shi na fita slowly idanun shi a d'an lumshe shi kad'ai yasan abunda yake ji a cikin ran shi ganin ta cikin halin nan, ganin kaman ta d'an natsu yasa shi janye beard d'in shi ya maida fuskar shi saitin kunnanta whispering in to her ear ya furta "I came all because of you" da sauri ta girgiza mashi kai ta d'ago idanunta sharkaf da hawaye ta juyar da fuskar ta gefe cikin fushi tace "ni ban son Auren ka sake ni!" jimm yay yana kallon ta can yay sigh calmly ya furta "Zarah kina fad'a man haka a matsayi na na mijin ki ba kyau fa" sheshshekar kukan ta ce ta k'aru, ji tay yace "Kin daina sona ne??" Kaman tana jira da sauri ta d'aga mashi kai alamar eh har saida ya d'an runtse idon shi kafin slowly ya bud'e sai kuma ya d'an cize le6en shi na k'asa, nisawa yay yace "are u serious Zarah?"da sauri ta k'ara d'aga mashi kai alamar eh wannan karon har saida yaji gaban shi ya d'an fad'i, shiru yay idon shi a kan gefen fuskar ta, mutsu mutsu ta fara yi tana son ta k'wace daga jikin shi saidae ta kasa a hasale tace ita ya k'yaleta, still shiru yay bai kuma sake tankawa ba sai dae zuciyar shi ta fara gasgata mashi abun da take fad'an, muryarta ce ta k'ara ziyartar kunnan shi tace ya saketa, sigh yay Slowly ya furta "Ok, I want you to look into my eyes and tell that u don't love me sai in maki abunda kike so in hakan zai saki farinciki" yana rufe baki ta juyo ta kalle shi cikin idon da k'arfi gaban shi ya fad'i don yana ganin fad'in zata yi, bin juna sukai da ido tana d'an huci wani irin kallo yake bin ta da shi sai motsa baki take ta kasa furta mashi Maganar gaba d'ayan su gaban su fad'uwa yake bai ta6a jin zullumin magana ba sosae irin haka, da k'yar ta fara bud'e baki tace "ba.......n......." Zuciyarta ce ta fara tariyo mata Alkhairan shi a gareta ta shiga raya mata yanzu duk son da take mashi da wahalar da tasha Saboda shi ta za6i ta rabu dashi, kawai sai gani yay ta fashe da matsanancin kuka ta fad'a mashi, wani irin lumshe ido Haisam yay sosae yaji sanyi a ran shi, Kuka take sosae ta had'e fuskar ta da k'irjin shi, daga jin yadda sautin kukan ke fita yasan ba K'aramin K'ona ranta ke mata ba zuciyar shi ce ta shiga tunano sak'on data tura mashi irin wahalar data bayyana mashi ta sha Saboda son shi, wani irin tausayin ta ne ke ratsa shi sam bai jin dad'in yadda take kukan har Fuskar shi ta nuna fararen idanuwan shi sun d'an yi ja, hannun shi d'aya ya d'ago ya d'aura a saman kan ta ya fara shafa gashin ta alamar lallashi cikin breaking voice ya fara magana "am very sorry Wife, am not happy I caused u pain, kiyi hak'uri don Allah, bansan komai ba game da haka" cigaba da shafa kan yayi a hankali sautin kukan nata ya fara raguwa, sun d'an d'auki lokaci a haka saida yaji tayi shiru sai ajiyar zuciya da take ta faman yi ya d'ago da kanta suka fara kallon juna idanunta sun yi luhu luhu sunyi ja har lokacin ajiyar zuciyar take ta saki,

"Forgive your Husband pls, bana jin dad'in ganin ki haka Wife, ba kamar in na tuna duk Saboda ni ne, ki manta komai ya wuce pls" yana Maganar d'umin numfashin shi na sauka akan Fuskar ta, shiru kawae tay tana kallon shi ba alamun zata tanka, fuskar shi a sake kaman zai murmushi yace mata tayi mashi magana pls sai lokacin ta d'an juyar da fuskar ta, hannu ya kai ya juyo da Fuskar ta sake kallonshi ya lumshe mata ido nan take ta gane Magana yake nufin tayi, da k'yar ta bud'e baki cikin muryar kuka da yar in ina tace "t...to ai kai baka sona ko shiyasa gara a bar Auren" d'an murmushi yayi yace mata in sun rabu to ya zatayi da son nashi,

"A...ai dama baka sani ba ko na 6oye sai in yi hak'uri kuma nasan zan daina daga baya, d...dama ai har na hak'ura za'a min Aure ko" tana Maganar ya zuba ma bakinta ido Fuskar shi kaman zai murmushi har ta gama ta d'an tura baki, murmushi yay ya d'an d'age gira yace "in kuma ni ban son rabuwa dake fa Saboda nima ina son ki" ba shiri ta waro ido bakinta ya d'an bud'e, sosae taji Al'ajabin Maganar don ta gama yanke bai sonta, hannu ya kai ya rufe mata bakinta da ta bud'e ta tura mashi bakin had'i da d'an juyar da fuskar ta, ji tayi yace bata bashi amsa ba sannan ta maido idon ta kanshi a sanyaye tace ai tasan da wasa yake tunda da yana son ta ai da ya nuna mata, murmushi yay kawae suka zuba ma juna ido Fatuu sai d'an kikkafta ido take idan tace bata jin sabon son shi na ratsa zuciyar ta to ta shirga babbar k'arya, ganin bai da niyyar cewa komai gashi ta k'osa taji da gaske yana son ta yasa ta d'an yamutsa mashi Fuska, d'age mata gira yay yace "What?" a d'an shagwabe tace he should tell her da gaske abunda ya fad'a, Sigh yay kafin a nutse ya fara Magana,
Chapter 4 · 0% Book details