← Book details Asanadin Makwabtaka Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 211

Sashe 10

Asanadin Makwabtaka Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Jama'a ina Baiwar Allah Fanan🤔

*ASM 075*

~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

............Sosae suka sha Bacci Haisam ne ya fara tashi wurin k'arfe goma, toilet ya wuce yayo wanka, bayan ya fito ya shirya cikin k'ananun kaya wanda da gani sababbi ne sai baza k'amshi yake, bayan ya gama shiryawa ya koma bakin gadon yana kallon Fatuu dake ta shan bacci gashinta duk ya tarwatse har ya d'an rufe mata fuska, murmushi yay ya juya ya nufi k'opa ya fita,

Fanan kwance akan gado ta lullu6e da bargo tana bacci, she spent almost the whole Yesternight pacing up and down acikin d'akin, gaba d'aya zuciyarta ta hana mata zaman lafiya wani irin zafin rad'ad'i ta rink'a mata, she wept until there were no tears left, haka tay ta kai da kawowa kota kwanta tana son tayi bacci sai tay ta imaginations kan Haisam da Fatuu dole ta tashi, sosae ta jigata baiwar Allah har salla taso tayi amman ta kasa k'arshe a fili ta rink'a d'aga hannu tana rok'on Allah da ya sauk'ak'a mata abunda take ji fuskarta a yamutse, saida akai sallar Asuba bayan ta gama tayi Addu'oi sosae ta koma gado ta kwanta, ta d'an d'auki lokaci kafin cikin sa'a baccin ya d'auketa. Part d'in Hajiya ya zo lokacin da ya shigo ba kowa a parlon ya wuce hanyar corridor, Bedroom d'in Hajiyar ya nufa lokacin da ya shiga tana zaune a bakin gado tana shafa mai jikinta sanye da doguwar riga bata dad'e da fitowa daga wanka ba, bayan ta amsa mashi sallamar da yayi ya nufi inda take, a gefenta ya zauna Fuskar shi cike da annuri ga wani fitinannan k'amshi da yake saki, gaisawa sukai tayi mashi an tashi lpy ya amsa daga baya ta tambayi Fateema yace mata tana bacci, yar hira sukai sama sama kafin ya tashi yace bari ya ga Fanan tace to,

A hankali ya tura k'opar d'akin da take ya shiga, a kan gado ya hangota ta duk'unk'une a cikin bargo, saida ya k'arasa gaban gadon yaga Fuskarta a d'an bude idanunta a rufe alamar bacci take, tsaye yay yana kallonta tun daga yanayin fuskar ya fahimci she isn't alright don Fuskar ta yi wani ja, ta cikin baccin k'amshin turaren shi ya fara kai mata, motsi ta fara yi ta fara bud'e idanunta a hankali, bayan ta bud'en bin juna sukai da kallo her eyes were red and swollen yana gani ya fahimci ba K'aramin kuka ta sha ba, yunk'urawa tayi ta tashi zaune ta kasa d'auke idanunta akan shi zuciyarta sai sak'a mata abubuwa da ke k'ara mata rad'ad'i take, wasu k'walla ne masu zafi suka taho mata jin zasu zubo yasa tay saurin sauke idanunta k'asa, gefenta ya matso ya zauna ya kai hannu ya matso da kanta saman kafad'ar shi sai sheshsheka take a hankali, shiru Haisam yay ya d'an rufe ido can ya bud'e ya juya yana kallon saman kanta, gently yace mata miyasa zata sa damuwa haka a ranta sai tayi causing mata wani ciwo, da damuwa akan fuskar shi yay Maganar don ba K'aramin tausayi ta bashi ba, cikin muryar kuka tace ita kanta ba yadda bata yi ba don kar ta damu amman zuciyanta ta takura mata ko bacci bata yi ba sai da Safe nan ta d'an samu ya d'auketa, daga jin yadda take futar da Maganar zaka Fahimci she's in serious grief, shiru yay he wished he could remove all the pain from her heart, a hankali ya kwantar da gefen fuskar shi a saman kanta cikin nuna damuwa yace "Am very sorry Sweetheart am not happy I caused you so much pain" d'an girgiza mashi kai tay suka yi shiru kowa yana kallon wuri guda can yay sigh ya d'ago itama ta d'aga kai tana kallon shi, tambayar ta yay tayi breakfast ta d'an girgiza mashi kai ya furta Ok bari ya kawo mata, yana k'ok'arin tashi ta kama hannun shi a marairaice tace mashi wanka take so tayi ko zata ji dad'in jikinta, mik'a mata hannu yay ta saukko daga saman gadon suka nufi Toilet. Bayan wani lokaci suka fito yana tallafe da ita k'irjinta d'aure da towel, taimaka mata yayi ta shirya cikin doguwar riga da hula ta zauna a bakin gado yace mata yana zuwa ya juya ya nufi k'opa ta bi bayan shi da kallo Zuciyar ta na raya mata abu game da shi da Zarah, k'walla ne suka shiga gangaro mata ta d'age kai sama, yana fita cikin parlor ya had'u da Hajiya ta fito yin Breakfast yay mata Magana kan yana son breakfast zai kai ma Fanan kai kawae ta d'aga mashi ta nufi Dining ya bita, bayan Saude ta zuba mashi ya juya ya koma, Magana Hajiya tay ma Saude kan ta had'a ta kai masu nasu can part d'in su tace to, bayan ta gama Serving nata ta juya Kitchen don ta had'a masu.

A hankali Fatuu ta fara motsi kafin ta fara bud'e idanunta, hannu tasa ta janye gashin daya rufe mata fuska har saida ta d'an ji mamaki ganin ba Haisam kaman yadda suka kwanta tare, tunani tay k'ilan yana toilet tay shiru tana kallon wuri guda sai faman zabga murmushi take da gani tana cikin tsananin farinciki, can ta yunk'ura ta tashi Zaune ta jingina da Headboard, memory d'in rayuwar su ya shiga dawo mata sai faman sakin murmushi take, sosae take mamakin yadda komai ya kasance a tsakanin su, ta d'an d'auki lokaci a haka ganin shiru bai fito ba yasa ta fara tunanin ko dai bai cikin toilet d'in ne, saukkowa tayi ta nufi hanyar laundry tana gab da isa k'opar taji anyi knocking kopar Bedroom d'in, juyowa tayi ta nufi kopar ta tsaya a bakin ta, tambayar waye tayi ta jiyo Muryar Saude da sauri ta kai hannu tana tattare gashinta bayan ta d'aure ta kai hannu ta bud'e kopar, da d'an murmushi ta gaidata itama murmushin take mata ta amsa tace "Amaryar mu an tashi lpy, dama Breakfast na kawo ba kowa a parlon to da yake naga shi yalla6ai d'in a can shine nace bari in fad'i maki" still Murmushin take tace mata to kafin tayi mata godiya sukai sallama, bayan ta dawo cikin d'akin a gefen gado ta Zauna tay shiru kaman mai tunanin wani abu, ta dan d'auki lokaci can ta mik'e sukuku da ita ta nufi hanyar laundry, after some minutes ta fito jikinta sanye da bathrobe ta nufo cikin d'akin, shiryawa ta shiga yi bayan ta gama yin shafa ta nufi Wardrobe, saida ta d'an yi ruwan idon kafin ta fiddo wata doguwar rigar shadda kalar butter an yi mata red aiki, bayan ta gama shiryawa gaban mirror ta koma ta fiddo jewellery da suka hau da kayan ta saka, k'ara gyara fuskarta tayi ta goga jan jambaki ta goga maskara a gashin idonta ya k'ara mik'ewa gazar gazar kaman ta saka eyelashes, bata yi ja gira ba sai kawai ta gyara gashin don tana dashi da d'an yawa, ita kanta taga kyaun da tayi tana Fesa turare tana k'are ma kanta kallo da d'an murmushi, bayan ta gama komai komawa tay bakin gado ta zauna bata yi tunanin zuwa tayi breakfast d'in ba don ba wata yunwa take ji ba,

Bayan ya kai mata Breakfast d'in da kanshi ya shiga bata a baki sai gashi ba laifi ta d'an ci da yawa kafin ta ce mashi ta k'oshi, kokarin mik'ewa tay tace bari ta fidda kayan ya rigata tashi yace ta zauna tana murmushi ta furta mashi thanks ya d'an lumshe mata ido, har ya kusa k'opa tace don Allah ya tambayi Hajiya in akwae paracetamol ya d'aga mata kai, bai jima ba ya dawo hannun shi ruk'e da glass of water ya nufi wurinta, da kan shi ya 6allo mata Maganin ya bata ta sha bayan ya d'aura glass cup d'in akan bedside drawer da Maganin ya d'aura idon shi akan ta cikin nuna kulawa yace "Your sacrifice means the world to me, it's the most generous thing anyone has ever done for me" daka kalli idanuwan shi zaka tabbatar da abunda yake fad'i, d'an murmushi tayi ta d'aura kan ta a saman shoulder d'in shi slowly ta furta "I can do anything for you my husband" lumshe ido yay fuskar shi d'auke da Murmushi, gyara zaman shi yay ya hau gadon sosae ya kwantar da kanta a saman cinyoyin shi fuskar ta na kallon shi tana mashi murmushi ya fara d'an shafa kumatunta can yaji tace "I love u so much babe, don Allah kar canza man zan iya mutuwa wllh" idanunta raurau tayi Maganar, lumshe mata ido yay ya furta " I will never forget how much you have done for me sweetheart" lumshe ido tay still da murmushi daga yanayin fuskar ta zaka fahimci ta samu sauk'in abunda take ji a cikin zuciyar ta, cigaba da shafa fuskar tata yay can ya d'an d'age kan shi sama ya lumshe ido nan take memory d'in shi da Fatuu ya shiga dawo mashi fuskar shi d'auke da d'an murmushi yayin da Fanan ta fara yin gyangyad'i daga baya bacci ya d'auketa.
Chapter 10 · 0% Book details