Sashe 144
Asanadin Makwabtaka Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
............Wata d'aya da rabi da zuwan Fatuu Us wata ranar Lahadi ta tashi da wani irin ciwon kai har da yar juwa take ji ranar dama Haisam a d'akinta yake su twins kuma na wurin Fanan dama haka suke yi in yana d'akin Fanan to a d'akin Fatuu zasu kwana haka in yana d'akin Fatuu to a wurin Fanan zasu kwana duk da suna da Nursery wato d'akin su wanda aka k'awata shi da abubuwan da suka danganci yara amman basu kwana a ciki, ganin yanayinta yasa yace mata su tafi Hospital amman sai tace mashi tana ganin basai sun je ba tunda ciwon ba wani tsanani yayi ba dama kuma lafiya lou ta kwanta tana ganin in tasha magani zata warke k'ilan harda gajiyar zirga zirgar da suka yi ne ya nuna gamsuwa da Maganar ta, ganin basu kaiga yin Breakfast ba yasa ta bari in taci Abinci sai tasha maganin dama suna dasu a first aid kit d'in su, Saboda yanayin da take ciki yasa bata samu zuwa Kitchen ba don had'a breakfast tare da mai aikin su wadda take baturiya, dama mafi yawancin lokutta tare suke aikin Fanan ma wani lokacin takan shiga saidai ba kowane lokaci ba Saboda aiki da take zuwa, a daddafe tayi wanka ta shirya cikin k'ananun kaya riga da skirt bayan an gama shirya masu table aka sanar dasu, gaba ɗayansu kowa yayi wanka suna sanye da k'ananun kaya lokacin da suka zauna zaman yin Breakfast d'in har su twins ma an masu gayu in ka gansu a lokacin sai kayi tunanin sunyi shekara ɗaya Koma sun fi don gaba d'aya sun yi wani irin girma sunyi 6ul6ul dasu ga bak'ar sumar su a nad'e gwanin burgewa haka idanuwansu farare tass dasu lips ɗinsu ma sun k'ara cizawa ta bangaren fata kuwa tamkar ka ta6a jini ya zubo har wani sheƙi take don mayukan fata masu tsadar gaske ake masu amfani dasu haka na gashin kan su ma, Bayan sun gaisa da juna Fanan ta kalli Little Grandpa dake hannunta da turanci tace mashi "Say Hello to Mom" kallon Fatuu yay ganin tana mashi murmushi yasa shima yay mata Fanan ta k'ara ce mashi yace mata hello ya d'aga hannu cikin Maganar shi da bata fita yace mata hello d'in itama Fatun ta d'ago mashi, kallon Abie dake hannun Haisam tayi tace mashi shima yace mata Hello ɗin yay shiru yanata kallonta ta sake maimaita mashi still baida niyyar cewa hakan yasa Fanan tace da alama shi kalar Dad d'in shi ne don tana lura bai cika yin magana ba kamar grandpa duk sukai murmushi ƙarshe saidai Haisam ya kamo hannun shi ya d'aga ma Fatun itama ta d'ago mashi sai lokacin Abie ɗin yay kaman zai yi murmushi, bayan sunyi bismilla a nutse suka fara cin Abincin baka jin komai sai k'arar cokulla Haisam na ci yana ba Abie haka Fanan ma tana ba grandpa sosae yaran suke ci, tun bayan da Fatuu ta fara ci taji kaman zuciyar ta na tashi haka dai ta daure tana cigaba, basu dad'e sosae da fara ci ba da sauri ta aje fork d'in hannunta ta dafe k'irji jin kaman amai na taho mata, Fanan ce ta fara lura ta kalleta tana tambayar ta lafiya hakan yasa Haisam kallonta shima yana niyyar yin Magana suka ga ta tashi da sauri ta nufi hanyar corridor da zai kai ta inda Bedrooms d'in su suke saidai ko kafin ta shiga corridor d'in Aman ya zubo nan ta duk'a ta shiga kwarara shi, har Kusan rigen mik'ewa ake tsakanin su suna rungume dasu twins suka nufeta, sannu gaba d'aya suka shiga yi mata Fanan ta dafata grandpa na ganin halin da Fatuu take ciki ya fashe da kuka ganin yana kuka yasa Abie shima ya saka kukan, kallon Haisam Fanan tayi da alamun damuwa akan fuskarta ta tambaye shi dama bata lafiya ne ya fad'i mata yadda sukai da ita da safen nan sam bata kawo komai a ranta ba tace mashi gaskiya yakamata su tafi Hospital a duba ta sosae da sauri yace Ok don shima halin da take cikin ya d'aga mashi hankali, saida ta gama sannan Fanan ta taimaka mata ta mik'e ta nufi hanyar Bedroom da ita don ta shirya su tafi Asibiti Haisam yabi bayan su yana ruk'e da su twins da ya rarrashesu sun daina yin kukan, ba tare da 6ata lokaci ba suka fito don tafiya Fanan tayi ma mai aikin su magana kan tazo ta gyara wurin aman kafin suka tafi, Haisam ne ke driving Fanan na front seat gefen shi tana ruƙe da su twins ita kuma Fatun an bar mata baya ita kad'ai ta zame jikinta ta kwantar da kanta, akai akai suke juyowa suna mata sannu da d'an murmushi take amsa masu tace ai taji ta samu sauk'i ma da tayi aman can tace ma Fanan ta kawo yaro d'aya ta rik'e mata harda tambayarta zata iya tace mata eh ta mik'a mata Abie, Asibitin da Fanan ke aiki suka nufa bayan sun isa ya parker Motar a inda aka tanada duk suka fito, basu wani tsaya Jira ba wurin ganin likita tunda dama nan ne asibitin da suke zuwa duk da Fatun wannan ne zuwanta na farko bayan tazo ƙasar, bayan Fanan tasa anyi mata duk wani abu da ake yi kafin ganin likita aka tura sunanta, tare gaba d'aya suka shiga wurin likitan wanda Bature ne yana ganin Fanan ya washe mata baki yana mata Welcome itama murmushi ta yi mashi ta amsa mashi ya maido idonshi kan Haisam suka gaisa haka Fatuu ma, mik'a ma Fanan hannu yay alamar ta bashi Adam dake hannunta ta mik'a mashi sai gashi bai mashi ƙyuya ba ya yarda dashi, nuna ma Haisam leather sofa dake gefe Yay alamar ya zauna itama Fatuu ya nuna mata ta gaban table d'in shi Fanan ma ta zauna akan wadda take facing ta Fatuu, Fanan ce tayi mashi bayanin abunda ke damun Fatun tace tana ganin ya kamata ai mata aune aune shiyasa suka zo ya furta Ok, maida kallon shi yay kan Fatuu yace mata sannu ta amsa kafin ya shiga yi mata tambayoyi, cikin tambayoyin ne ya tambayeta yaushe rabonta da period tace mashi bayan data haihu ya dawo tayi sau d'aya daga nan bai sake dawowa ba, tambayarta watannin su twins yay ta bashi amsa da shidda da rabi, bayan ya gama yi mata tambayoyin ne yace ma Fanan ya tura tests da za'a mata ta amsa da Ok tare da mik'ewa ta kai hannu ta kamo Fatuu tace suje, kallon Haisam tay tace mashi bari suje su dawo ya d'aga mata kai, ganin zasu fita yasa Adam dake kan cinyar Doctor fashewa da kuka yana Mik'o masu hannu, dakatawa sukai Fanan ta nuna mashi saitin Haisam tana fad'in "Look at Dad he's here" juyawa yay ya kalli saitin Haisam da take nuna mashi yana ta6e baki kamar zai cigaba da yin Kukan, juyawa sukai suka tafi bayan sunje lab ɗin ba 6ata lokaci aka d'ibi jinin Fatuu don yin gwaje gwajen, bayan an d'iba dawowa sukai Office ɗin likitan Fanan tace ma Fatuu ta zauna kan kujerar da Haisam yake ita kuma ta koma kan ta gaban table d'in Doctor suka shiga tattaunawa irin tasu ta likitoci, ba'a d'auki lokaci mai tsawo ba aka turo results d'in Doctor ya sanar dasu gashi an turo duk suka maida idanun su kanshi, duk awon da aka mata ya nuna lafiya lou sai guda d'aya na ciki da yake nuna akwai na tsawon sati shidda wato wata d'aya da rabi kenan tunda tazo K'asar ta same shi, tsananin mamaki ne ya bayyana akan fuskokin su ba kamar Fatuu don ita a tunaninta tunda bata period bazata samu ciki ba, da mamaki Fanan tace ma Doctor ɗin is he sure about what he said cike da tabbaci yace mata haka result d'in ya gwada tare da juyo mata da computer d'in don ta gani, bayan ta tabbatar da sakamakon d'agowa tay ta kalli Fatuu da tayi zuru tana kallon su kafin ta maida idonta kan Haisam da shima mamaki ya bayyana kan fuskar shi tace mashi yaji wai Zarah is pregnant ya jinjina mata kai, Doctor d'inne yace masu ana yin hakan su kwantar da hankalin su Haisam yay sigh kafin yace ma Doctor ɗin gaskiya yayi wuri da yawa ace tana da ciki at least jikinta na buk'atar Hutu sosae tunda bata dad'e da haihuwa ba gashi kuma twins, jinjina kai Doctor din yay yace hakane yanzu ya za'ayi shiru Haisam ya d'an yi yana kallon Floor da alama yana nazarin wani abu ne can ya d'ago ya kalli Doctor ɗin yace ya yake gani in a fitar dashi, nuna mashi yay akwae risk sosae fitar da ciki amman kaman nata da yake k'arami sosae ba'a ciki samun matsala ba Magani kawai za'a bata in akai sa'a zai fita ba tare da wata matsala ba in sun amince, jinjina kai Haisam yay kafin yace a bata maganin a tare Fatuu da Fanan suka kalle shi da sauri kowa da yanayin mamakin jin Maganar, da alamun damuwa Fatuu tace "A...amma Hubby kai da kan ka zaka ce a zubar da shi bacin kasan ba kyau hakan laifi ne" shiru Fanan tayi yanayin fuskarta ya sauya kaman zatai kuka a yadda take ji inama ace cikin a jikinta yake don sai taji bata son a zubar dashi ji take kamar ta rok'e su kada a zubar dashi amman tana gudun aga ta zaƙe, shima Haisam da alamun damuwa ya shiga kwatanta mata duka yaushe ta haihu gashi tasha wuya dole jikinta na buk'atar Hutu kafin ace ta sake wahalar wani cikin ga wahalar rainon su twins suma tunda ba yaye su tayi ba, haka ya dingi kwatanta mata matsalolin yace tunda k'arami ne kuma zata iya cutuwa haka su twins ma ba laifi bane in an cire, shiru tay tana d'an tunani ita kanta bata ji tana son cikin ba amman kuma sai taji bata goyon bayan a zubar dashi, gaba ɗaya idanunsu na akan Fatuu da tayi shiru ta kasa cewa komai ganin haka yasa Doctor ce masu ko suje gida suyi shawara in still suna son a fitar dashi